5&6

241 17 1
                                    

.https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK

AHALINA

    (Siblings of different Father's)

(Book two in Aure uku series)

            By

   CHUCHUJAY ✍🏽

Gamasu san a tallata masu hajarsu cikin farashi Mai rahusa 09058191213 .

EPISODE 5⃣➡6⃣

    A hankali Nameer yake tuki a yayin da motar ta ɗauki shiru cos tabbas idan yayi magana shi kansa yasan bazai iya mayar da ita bakinsa ba duba da yarda zuciyar sa ke tafarfasa ,

Murmushi Anisa dake gefen sa tayi tace"Baby tunda muka taho bakin ka shiru kaƙi magana amma wani abu da baka sani ba shine ,ni a kowanne yanayi naganka burgeni yake ,shafa kan jaririn hannunta tayi tace "bashi da suna fa har yanzu cos dama uba ke bawa yaran sa suna 'dan haka wannan lokacin ma akan yarona hakan ne zai faru ,ka bashi suna and trust me DNA test ɗin Chan da zai fito 99% positive ne ,ni banga menene amfanin wahalar da kai ba. "

    Wani irin wawan burki yayi Ya Kalleta cikin fushi mai mutuƙar yawa yace "fita a motar nan ,"

Kallan sa take tana wannan murmushin wanda yake ji kamar ya yagesa a fuskarta ,hannunta ta kai ta ɗora a nasa tace "Nameer Stop trying ,mene amfanin ƙokarin da kasan babu wani outcome Mai kyau da zai fito a cikinsa?"

Kazo mu rufawa juna asiri muyi Aure mu bawa yaranmu rayuwa Mai kyau da inganci,babu wanda Ya gani babu wanda yaji please,

    Hannunta da ta saka Akan nasa Ya yakice da ƙarfin gaske kana yace "ke duk wani guntun haukaki fa inaji dashi,kila ma yafi na kanki ,sannan nasan duk hanyar da zanbi naci maki mutunci wallahi fiye da yarda baki zato 'dan haka kafun na wulakantaki ki fitar mun a mota tunda bata ubaki bace."

Ƙaramun murmushi tayi Mai ci masa rai kana tace "Cool down Man,"Bude murfin motar tayi ta fita tana Mai faɗin ,mu haɗu a gida uban ƴaƴana,

Wani irin figar motar yayi wanda Ya sakata saurin ja da baya tana Mai darawa tana juya wayarta da tayi recording abunda ya faɗa yanzu nayi mata rashin mutunci kana ta danna numbern uwar ɗakinta,

Kira ɗaya ta ɗauka ,murmushi tayi kamar tana kallanta kafun tace "uwar ɗakina ina fatan kin gama da Asibiti?"

Licking lebenta na ƙasa tayi tace "Allah yabarmu tare ,sannan a yanzu maganar da nake maki na samu wata hujja da babu yarda iyayen Nameer zasuyi dole su yarda,

Lokacine da yakamata ace sun girbi abunda suka shuka musamman Imam paki da matarsa Umaimah Bulama,ina jin suna jin labarin kiyayya da fansa amma bana taba tunanin sun tab'a ganin irin tawa ƙiyayyar da fansar dake dumama acikin zuciyata da b'argona wadda nake ji kamar na soke dukkanin acting ɗin da nake na kashesu a zuwa ɗaya,kin san nayi training wajen yin kisa ko wacce irice ballantana kuma akai ga maƙirici,

Dariya tayi kana ta kashe wayan tana Mai faɗin"Wallahi da ni yarinya ce Mai hali na gari,amma dukkan wannan halayyar ta gari ta ƙare ne a lokacin da na rasa mahaifiyata kuma kash sai Ya zamana kafun ta tafi ta sanar min da waɗanda sukayi silar mutuwarta,dukkan godiya ta tafi gareta da ta barni da ƙyautar fansa da ƙiyayya,wadda na rantse da Ubangijin da na yarda dashi bazan tab'a gushewa ba sai na ƙarar da zuri'ar Paki da duk abunda suka mallaka. "

    Da haka ta nufi gidan 'dan shirya saban tuggunta.

******************************************** 

  Bayan Rabuwar Nadiya da Evan ta daɗe tana saka da warwara a cikin zuciyarta kafun ta nufi gida kai tsaye dan ko office bata san zuwa,

Abu guda ɗaya ya tsaya mata a zuciya wanda shine yarda Evan yasan Abubawa da dama akanta ciki kuwa har da inda take zama,

AHALINA(book 2 in Aure uku series)✔Where stories live. Discover now