57&58

270 11 0
                                    

AHALINA

(Siblings of different fathers)

Book two 'in Aure uku series.

EPISODE 5⃣7⃣◼5⃣8⃣

   Tun da Nadiya tayi sallar asuba bata koma ba,zumuɗinta kawai taji kiran mom ɗin Ahmed wanda har baƙwai na safiya bata kirata ba wanda tana da yaƙinin cewa 'ya tashi koda kuwa sau ɗaya ne,ganin shirun da kuma fargaba yana neman karta 'ya sakata tashi ta shirya wuraren takwas na safe ta nufi asibitin ita Kaɗai cos ta riga da tasa Haleems da Naomi booking ɗin jirgi su fara gaba domin ita kam a yanzu bata ga ta tafiya ba sai taga ƙwal uwar daka domin kuwa ko me za'ayi sai tagan shi,

Kai tsaye ɗakin da aka kwantar dashi ta nufa kamar wata munafuka tana Addu'ar Allah yasa babu kowa a ciki,kwance ta tarar dashi a kan cikinsa idanunsa a lumshe,tunanin yana baccine ya sakata takawa a hankali ta zauna kan kujerar dake facing ɗinsa,idanunsa dake lumshee ta zuba ma ido kana ta sauke idanun tana mai faɗin"Alhamdulillah ko yanzu Dad yazo ya koreni ai ƙwalliya ta biya kudin sabuli tunda har na samu na saka ka a idanuna,"

A hankali ta kamo hannusa tana mai kallan bandage ɗin dake bayan sa,lokaci guda idanunta suka ciko da ƙwalla,cikin karyayyiyar murya tace"Why?"Mene ya saka ka zabi daka ji ma kanka ciwo akan ni naji,wanene ya faɗa maka idan kai kana kwance a maimakona zanji daɗi ,i Just hope nice abun nan ya sama ba kai ba saboda baka chanchanci haka ba ko kusa ko misali.

    Goge hawayen dake faman mata reto a kumatu tayi tace"ka warke da wuri cos dolene zanyi scolding ɗinka na ƙarba mun stab da kayi bada izinina ba"

Batayi Aune ba sai ji tayi ya shafa hannunta da ta riƙe nasa dashi yace"Why don't you scold me Now My love".

Kallan idanunsa tayi da sauri ,har a lokacin a kulle suke,dukan wasa ta kaimasa tana mai faɗin"so idanunka biyu you silly lover"

Ɗan sautin ƙara yasa wanda ya ruɗata nan take ta duka tana mai faɗin im sorry,

Dariya yasa sosai har Adam Apples ɗinsa 'na motsawa gwanin shawa'a,hannunsa ya miƙa mata yace"help me up,"Babu musu ta taimaka masa ya zauna tana mai kaffa kaffa da ciwansa gudun kar ya fama.

Hannunsa ya ɗora kan gefen gadon yayi mata alama da tazo ta zauna,

Zama ɗin tayi tana mai goge guntuwar kwallar dake gefen idanunta ,alama yayi kamar zai kama hannunta sai kuma ya fasa,kular da tayi da gesture ɗinsa ne ya sakata murmusawa tana mai kama hannunsa tace "ka riga ka taba and 'na tababata a yanzu baka da lafiyan bad thoughts,yar karamar dariya yayi kana yace "Ina mutuwar sanki Nadiya,A yarda nake jinki a zuciya zan iya karba miki stabs ko mai adadin yawansu ,zan iya mutuwa domin ki sannan da ace za'a dawo mun da rayuwata a sake maimaitawa zan sake mutuwa a dominki,'na sani im a public figure wanda nake da mad crushes waɗanda nasan they will kill for me musamman ma a yanzu da mutane da dama ke ganin kin jani astray saboda 'na zabi addinin musulunci ,amma mene ?

Abun da nake san ki sani wanda shine ,"zan kula dake a ko wanne hali,zan baki tsaro a duk inda kike muddin Babu tsaro a wannan gurin,zan soki da dukkan rayuwata ,a wannan abun daya faru na sake samun gamsuwa da kaina 'na cewa tabbas ina buƙatar ki kusa dani,Ina san ki zamo mallakina matata,zan baki duk wani kulawa da ya kamata ace Namiji ya bawa matarsa ,sannan na gama yanke shawarar binki ƙasarki inda nasan nan hankaliki zaifi kwanciya,idan kuma ba Nigeria ba ki zabi ko wacce ƙasa kike so zan biki mu gina rayuwa mai tsafta a tare domin duk inda kike nan ne ƙasata"

    Saurin goge hawayenta tayi kana tace"shi yasa ai ka ƙwana biyu baka kirani ba,"

Murmshi yayi mai kyau yace "aiki yasa ban kiraki ba shima kuma Babu yarda zanyi ne ,Ina samun lokaci kuma da sauri na bibiyi schedule ɗinki na dawo Ghana gareki na ƙarba miki rauni ya sarauniyata"

AHALINA(book 2 in Aure uku series)✔Where stories live. Discover now