SOFIA
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Shafi na shiddaNEW YORK CITY
NEW YORK UNIVERSITYJami'ar ƙasar New york jami'a ce wacce tayi fice lungu da sakon ƙasar amurka, kuma suke kokari wajan koya ma ɗalibai abubuwan da suka dace wato ilimi.
Makarantar tana ɗaukan ɗalibai daga kasashe daban daban, kuma tana yaye su da zaran sun gama da programme ɗinsu, kama daga kan Bsc, PHD,Doctoring degree da sauran su.
School of science ɓangaren Kimiya DEPARTMENT OF PHYSICS babu ɗaliban da department ɗin su suke ji dasu kamar B4G, *BEST FOUR GROUP* duk faɗin makarantar babu wanda bai san B4G ba kama daga kan juniors da seniors da waɗanda suka gama, da sabbin shigowa ba, Ba sa shiga harkar kowa a makarantar, ba kuma sa yadda da sabuwar abota, suna claming ilimi, kuɗi da kyau da mulki, domin kuwa ya bayyana a jikin nasu dama kayan da suke sanyawa.
NIGERIA,KADUNA, KANO ROAD
ABDULRAHIM POVFitowar sa kenan daga kwaraɓaɓɓen ɗakin da babu komai a ciki sai zallan katifa da yagulallan zanin gado wanda ya fi shekara ma bai ga ruwa ba balle omo.
Ya zagaya makewayen da ke gidan hayan wanda har da matan aure, yayin da nashi ɗakin yake lungun zaure, wanka yayi da ruwan rabin buta sannan ya fito yana fat fat fat da takalmi yayin da ya wuce wasu matan aure da suke ta kokarin girki akan murhun gawayi.
Kai tsaye ya shiga ɗakin nasa jim kaɗan ya fito sanye da farar yadi ya sha wata yagulallan babban riga tsohuwa har da hula, ya fito yana dogara sanda nan fa ɗaya aka fara gulman sa ana kuskus, yana ji Ya kundumo ashar ,"Dan durun uwar mutum ya fito fili ya yi magana mana, munafukai kawai"
Yana kai wa nan ya sa kai ya fita,lafiya kalau yake tafiya amma yana shan kwanar da ya haɗu da abokin burmin sa sai suka fara dogara sanda uwa basu iya tafiya ba....A daidai ta suka samu suka haye suna mai zantawa cikin adaidaitan.
"Baba Kamilu ya ce,"Wallahi na samu yaro a wajan baran nan fa, muna zuwa zaga ganshi"
"Kai haba Dan Allah Kamilu? Ya tambaya. "Kwarai kuwa ai baka sani ba idan da yara ne anfi samun abin bara billahillazi jiya baka ga kuɗin dana samu ba"
Ya zurfafa cikin tunani hakika ya jima yana son ɗauko ƴar sa don ta rinka taimakon sa a wannan harkar, to amma dole ya dawo yazo ya zauna yayi tunanin yadda zai ɗauko ta... yana wannan tunanin suka iso dandamalin mabaratan dake Kano road, kaduna.
Ya samu buhun dake hannun sa ya shimfiɗa cikin tsakar rana ya zauna ya kafe idanuwan sa cikin wani gilashi baki wuluk yana bara yayin da Baba Kamilu shima ya kama angle ɗin sa daban.
A ranar yana komawa bai bi takan ƴan gidan ba ya shirya kayan sa da ƴan kuɗaɗen sa da yake tarawa yayi shigar sa ta mutunci ya kama hanyar Abuja.
Yana isa da daddare ya fara binchiken halij da Anna da Baffah suke ciki, ta hanyar wani mai tattara shara a gidan ya fito da ita waje kafin motar kwale bola ta fito ta ɗauke sharan....anan ya toshe shi da dubu biyu, ya lallaɓa yaran akan yana son ya samu bayanai game danmutanen gidan a sirrince.
Ranar yini yayi a kofar gidan dake kallon gidajen Baffah, yana kallo ana ta shige da fice., har dawowan Sofia da Anna daga park ma ya gansu.
YOU ARE READING
SOFIA
Short StoryNakasar rashin ƙwarin ƙafar da Sofia za tayi tafiya ita ce KALUBALE da kuma JARABAWAR da ta shafe kowacce jarabawa zafi da ciwo.Binchiken likitoci sun gane cewa Kafafuwan Sofia tun a cikin cikin mahaifiyar ta suka samu rauni wanda hakan ya samu sil...