SOFIA
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Page_19_SHARHI_
*Barkan ku da war haka, na ce labarin Sofia chukurkuɗaɗɗiyar ƙaddara ce, Ina so na fahimtar da ku hargitsin da ke cikin labarin wanda ni ke fatan dai bai ruɗar da ku ba, zan so ku cigaba da bibiyata don ku amafana da cikakken darasin da ni Diela na ke tafe da shi, Na gode*MAITAMA DISTRICT HOSPITAL
05:00pm
Anna ce ta fito daga cikin motar ta hannun ta rike da disposable lab coat, wuyanta rataye da stethoscope sauri sauri har ta karasa cikin asibitin, ta na duba agogon hanun damam ta wanda yake daɗa tunasar da ita cewa majin yacin na tsananin bukatar ta a wannan kokacin.Ta na karasowa Nurses suka karɓi labcoat ɗin da duk wani abin da suka tabbatar ba zata bukace shi ba, sannan ta shiga ɗakin theater kafin wasu likitocin suka biyo bayan ta tare da nurses ƙwararru guda biyu....Tsahon awa ɗaya da rabi suka ɗauka cikin theater room ɗin da misalin 6:30am ta fito ta yi hanyar offishin ta bayan ta gama kimtsawa ta fito daga cikin washroom ɗin office ɗin ta samu ana knocking kofar.
"Who is at the door? Anna ta tambaya
"Dr ESHAAN Ma'am" aka bata takaitacciyar amsa."Am coming" ta faɗa tana karasawa bakin kofar ta buɗe ta ce,"Have a sit" Ya zauna ita ma ta zauna ta na cewa,"Hope babu wata matsala don ina buƙatar na huta gidan za tafi"
"No not at all take your time Doctor we are really proud of you"
"Thank you Dr.Eshaan"Anna ta faɗa tana haɗa labtop ɗin ta da wasu kayayyakin ta.
"Uhmm Doctor dama wan cen maganar da muka yi jiya wasu patient da suke son a duba lafiyar ɗan su yana fama da Hypogylcemia suna yawan zuwa asibitin nan dama Dr.Theresa ne ta ke duba su yanzu kin ga tana US, ke ne dai muke so ki duba Patient ɗin saboda yana matukar jin jiki""Yaushe ne appointment ɗin su?Anna ta tambaya.
"Ko gobe kika ce zan tura musu request ne kawai ta email kamar yadda suka ma asibitin request"
"It's okay ka tura amma ka tura musu address na hospital ɗi na, a cen za su same ni"
"Okay Ma'am thank you Ma'am" kawo na rike miki kayan Ma'am Eshaan ya faɗa yana murmushi "Sure" cewar Anna
"Dr.Anna na ce wai har yanzu ba a samu daughter ɗin ki ba? Eshaan ke tambaya."Wallahi fa ba a same ta ba, amma bamu cire rai da ita ba, In Sha Allah"
"Ohhh Allah yasa a dace""Amin ya rabbi Eshaan amma gida zaka tafi ko don naga dare ya yi"
"Eh Sai da safe" ya bata amsa, ta ce,"A gaishe da su Nana da Mimi, ya kamata su zo min weekend", " Haahhh kar ki damu Dr.Anna zan kawo su soon sai da safe"
A gajiye ta koma gida,Ta sauya kayan jikin ta ta watsa ruwa sannan ta fito ta hau kwala kira "Chioma" "Chioma"
"Yes Ma." Muryar dattijuwar mace ta amsa ta nufo sashin da gudu tana yarfe hannun ta tsugunawa ta yi tana cewa,"Sannu Madam"
"Yawwa, me kika dafa ne?
"Rice and stew Ma" Chioma ta faɗa.
Anna ba wai ta na son abincin Chioma ba ne don sabuwar ƴar aikin da ta ɗauka kenan a watan nan du du satin ta biyu ba wai ta gama karantar halayen ta ba ne duk dama tana da tabbacin tana da hankali tun daga gidan Papa aka kawo ta nan ɗin ganin ayyuka na yi ma Anna yawa Baffah yayi requesting for house help aka kawo ta ƙabila ce kwanan ta biyu Anna ta fahimci tana da tsaɓta sosai, ita tana so ne kawai Chioma ta rinka yima masu gadi da aikin cikin gida abinci, amma ban da abincin da za su ci ita da Baffah.
YOU ARE READING
SOFIA
Short StoryNakasar rashin ƙwarin ƙafar da Sofia za tayi tafiya ita ce KALUBALE da kuma JARABAWAR da ta shafe kowacce jarabawa zafi da ciwo.Binchiken likitoci sun gane cewa Kafafuwan Sofia tun a cikin cikin mahaifiyar ta suka samu rauni wanda hakan ya samu sil...