Sha_Ɗaya 11

12 2 0
                                    

SOFIA
NOBLE WRITERS ASSOCIATION

Page_11

SOFIA POV

"WAHEEDI"
Ita ce kalmar da na fi amanna da ita a rayuwata ta yanzu, bana shakkan fita bara bana kuma shakkan haɗuwa da koma waye, Yayin da kallo ɗaya za kayi min ka tabbatar da rama tsagawaran talauci da sanadin yawo a rana ya haifar da duhu da ramar da nayi.

Chukurkuɗaɗɗen mayafin dake saman kai na wanda na ɓoye ainahin surar gashin dake kai na, yayin da na zuba ma wani ɓangare idanu ina kallon motocin dake kai komo a ko wani sa'i guda tare da mutanen da suke kai komo a gefen hanya yayin da baki na baya gajiya da faɗin Waheedi.

Na Sunkuyar da kai na kawai naga an  sako min naira ɗari biyu sabuwa dal, ɗago kai na yayi daidai da rashin samun wanda ya bani wannan barar, tunani na da kwakwalwata ta shiga rubibin tuna wanda ya sanyo min kuɗin nan, gabas da yamma, kudu da arewa sune abin da idanuwa na suke kallo amma sama da ƙasa babu kowa a wajan sai ni kaɗai, Abhi na cen gefe shi da abokanan sa mabarata nayi mamakin yadda ya san mutane da dama duk da cewa yau kimanin watan mu uku da baro kaduna, ya isa ya san mutane kasancewar dama tun da muka zo garin bai zauna ba koda yaushe fita yake yi.

Kuɗin da aka sanyo min na ɗauka da bisimillah a baki na na ajiye ma wata tsohuwa mabaraciya iri na amma bata gani, na ce "Baaba ga bara an bamu na ɗau nawa na baki naki"

"Abb  to to to madallah godiya nake ƴan nan kina da amana, Allah ya shi albarka ko"

"Ameen ya Allah" na amsa ina mai ɗauko alkur'ani na yayin da na soma karantan suratul yasin ban ajiye ba sai da na kai karshen ayah hankali kwance na rufe na fara waigawa ina yafito Abhi da hannu don an fara kiraye kirayen sallar azahar.

FULANI HAƊEJIA

Bukkazu yayi wani kara yana ja da baya lokaci guda ya girgiza yana muzurai yadda kasan ana kona sa, kwaryar dake gaban sa wanda ya nuna masa hoton SOFIA tana karatun alkur'ani, ya sake toshe kunnuwan sa, bai gama tsorata ba sai da yaga ɗari biyun da ya ba ma ɗan aika an dawo masa dashi, tuni ɗari biyun ya kama da wuta ya kone shi kaɗan sa kurmus.

Bukkazu ya ce,"Na gargaɗe ku kada ku shiga gonar wannan yarinyar domin kuwa tana da haɗari, ban san ko ita wacece ba amma jininta mai karfi ne, tana da tsarin da ban san daga ina ta same shi ba, aradu ba zan iya ba.

"To ka karasa mana sharuɗɗan mana Bukkazu" Fulani Haɗejia ta faɗa tana kara gyara zama duk da cewa suma sun tsure da yanayin da Bukkazu ya shiga.
Bukkazu ya kalle su da jajayen idanuwan sa, ya ga alama duk azabar da yake amsa daga wajan yarinyar nan, su ɗin basa jin komai, ya ce,"Sharuɗɗan karshe kenan, ku fita daga gonar yarinyar nan domin bazaku iya ja da ita ba na gaya muku"

Lokaci guda Bukkazu ya toshe kunnuwan sa yayin da sautin karatun alkur'anin yake masa amsakuwwa cikin kunnuwan sa,Ya ce,"Idan kunne yaji to gangar jiki ya tsira" Yana gama faɗin haka ya ɓace daga ɗakin babu shi babu alamar sa dashi da tarkacen sa.

Fulani Haɗejia kuma ganin abubuwa ra'anin ainun ya saukar mata da zazzaɓi, Jakadiyyah kuma ita ke jinya...Ranar dai babu zuwa turaka, yini tayi tana ɗura ma Bukkazu ashar ya firgita su.

Washegari ta tashi garau, ta shirya tsab cikin shigar ta ta matan sarki, ranar sai Haɗejia, tare da Jakadiya suka tafi, da tunani canza wani malamin don Bukazzu kam ba ba lallai ya dawo ba.

Minti arba'in motocin Mai martaba suka bazu saman titin gidan sarautan jihar dutse yayin da motar Fulani Haɗejia na baya ana tuka ta ita da Jakadiyyar ta....a daidai lokacin da motocin suke tafiya a hankali suna dosan bakin gate daidai nan ta buga uban tsoki tana cewa,"Kiga Almajirai da mabarata ba hali Sarki yazo fita sai sun taru suna maula da alama akwai mai sanar da su cewa Sarki zai fita" ta dafe goshin ta tana tuna jiya da Mai martaba yake sanar da ita zasu yi tafiya zuwa Kano, ya ce mata ta shirya tun da zata je Haɗejia sai su fita tare motoci biyu su raka ta.

SOFIA Where stories live. Discover now