SOFIA
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Page_12FULANI HAƊEJIA
Fulani Haɗejia zaune gaban tsohon malamin da ya fara mata aiki shekarun baya tana kallon sa Yayi bori, ya juya, ya ɓace, ya sake dawowa asalin wajan zaman sa ya kura mata idanu yana hararar ta tsahon minti biyar yana tauna goro kafin ya tofar da gutun goron dake kunshe a bakin sa ya kalle ta ya ce,"Aikin da a kayi miki shekarun baya kamar yadda kika sani babban aiki ne kuma ya ruguje sakamakon canja malamin da kikayi yayi ta cin kuɗin ki babu aikin da yake miki, Ga shinan ina ganin komai kafin kizo nan ma kin haɗu da wani kuma ya faɗa miki gaskiyar abin da zai faru da ke nan gaba"
"To amma Boka na Haɗejia babu wani abin da za mu iya yi a halin yanzu?
"a bisa dukkan alamu yanzu dai komai kalau yake tafiya sai dai kuma taurarin Yarima suna yawo a nan garin Dutse da alama gab yake da dawowa cibiyar sa, kuma da zarar yasa kafa a garin nan to duk wani aiki da kika yi a baya zai fara rushewa, ya cigaba da cewa,"Na san an faɗa miki cewa akwai yarinyar da zata zamo shamaki da duk wani aikin da zan yi miki nan gaba wato dai kamar katanga take a rayuwar Yarima.
Fulani Haɗejia ta gyaɗa kai gumi na keto mata tana gogewa da mayafin ta tana cewa,"Na Haɗejia ka faɗa min miye abun yi yanzu?, A tsorace nake saboda ina ganin siffofin yarinyar tana razana ni a ƴan kwanakinan, Ina so kayi min babban aiki, a hana yarinyar haɗuwa da Omar, kuma a hana ta shigowa Masarautar Dutse."
"Dole sai an zubda jini da dabba mai kafa huɗu da mai kafa biyu, ga wannan idan kin koma gida kiyi wanka da shi, wannan kuma kiyi hayaki da shi, kayan da kika zo da su nan kuma ki tabbata kin kyautar kar ki kuskura ki kara sanya wannan kaya".....Ya dubi jakaciya ya cigaba da cewa,"Zaki zo nan da kwana biyu kacal domin karɓan ragowar aikin"
Ya yi ihu da babbar murya ya ce,"Sauran aiki kuma ni zan karasa""Na gode Na Haɗejia, Na gode...........Ki tafi kan ki ƙasa, ki tafi kina istigfari domin Allah ya yafe miki manya manyan zunubban da kika aikata"
Fulani Haɗejia ta runtse idanuwan ta har ta bar wajan, tana ji yana cewa,"Mata ku gadzayo ku taho wajen Boka na Haɗejia kuzo na biya muku bukatun ku, kuzo mu haɗu mu aikata zunubi......Har suka kai bakin mota bata dena jiyo muryar ba, kamar yadda ya saba kullun da wannan kiran yake kirawo mata don ma yanzu an rage zuwa, da sai a cika jejin mata suna layi tun asuban fari suke zuwa.
A ranar Fulani Haɗejia ta koma masarautar dutse kasancewar ta macce mai ɗagawa da izza ko kwana a gidan su ma bata yi tana dai zuwa gaishe da ƴan uwan nata sannan ta fita tayi damuwar da ta kawo ta garin. Tan zuwa da taimakon jakadiya aka kyautar da kayan sannan ta yi wanka da maganin, ta yi hayakin ta hankalin ta kwance. don ba zata so a sirin da ta jima da binne wa ba ya tonu...."Inaaaaaaaah" ba zan bari kowa ya gano ainahin gaskiyar da nake ɓoyewa shekara da shekaru ba domin cimma wani buri nawa.
SAGEER POV
"Yanzu don Allah yaya Sageer dole sai kayi tafiyan nan? Nadiya ta tambayi Sageer tana shirya masa kaya cikin a kwatin sa mai tsada.
Ai idan kin ga na hakura da tafiyar nan to dai ko bani da lafiya, Ke bari kiji muhimmancin tafiyar ma ko bani da lafiya sai na yi ta"
Taɓe baki tayi ta fice ta bar masa ɗakin kasancewar dawowar ta kenan daga Gidan Daddy kuma tana tsammanin ta dawo kenan sai dai kuma idan zata je ta duba lafiyar su...Yaran ma gaba ɗaya suna cen Mummy ta ce a bar mata su. ta samu Hadiza a ɗaki ta zauna suka soma hiran su na ƴan uwan taka, saboda akwai shakuwa tsakanin Nadiya da Hadiza tun zaman su a U.S.A
Sageer na gama haɗa kayan sa kala biyu ya ajiye ma Nadiya kuɗi saman gado sannan ya rufo apartment ɗin yayi tafiyar sa Tafiya ce mara tsayi domin kaduna ya nufa.
Karfe biyu na rana ya isa kofar gidan da yake tsammanin nan ne a kayi masa kwatance in da matar take, babu yanda ya iya don dole ya dakatar da ita.......Yana cikin wannan tunanin ne ya jiyo karar horn, Motar ce dai da aka faɗa masa da alama matar ce a cikin motar.
YOU ARE READING
SOFIA
Short StoryNakasar rashin ƙwarin ƙafar da Sofia za tayi tafiya ita ce KALUBALE da kuma JARABAWAR da ta shafe kowacce jarabawa zafi da ciwo.Binchiken likitoci sun gane cewa Kafafuwan Sofia tun a cikin cikin mahaifiyar ta suka samu rauni wanda hakan ya samu sil...