Shafi na Bakwai

7 1 0
                                    

SOFIA
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Shafi na Bakwai

Sun fita waje don duba ainahin hanyar da suka bi alokacin jirgin ma yana kokarin tashi, don an jira su basu karaso ba, Already Baffah har ya bada cigiya da sanarwa ƴar sa ta ɓace.

Sai dai sun yi rashin sa'a domin kuwa tuni sun jima da barin airport ɗin,

ABDULRAHIM POV
9:00am

Karfe 9:00am tara daidai motar su tana kan titin Nnamdi azikwe way suka paarker don su huta saboda irin wutar da suka ba ma motar duk gudun kar a kama su.

Daga wajan ya sallami matar data taimake sa sannan ya ɗauki Sofia ya tari mai napep suka wuce Kano road kai tsaye.

Ko sallama bai yi ba ya shiga da Sofia yayin da kallo ya koma kan sa, amma babu wanda ya isa yace uffan yana shiga ya kwantar da ita saman katipha sannan ya fita waje ya zauna saman kujerar dake gefen ɗakin yana zaman kashe wando duk kallon matan yake yana murza gashin bakin sa, yayin da ya ga mazan sun fara dawowa kawo cefane yayi gyaran murya yace,"Duk wanda ya san cewa bai biya kuɗin hayar gida na ba, to ya gaggauta tashi domin kuwa gida yanzu ba nawa bane eheee duk masu yimin rashin mutunci to yau zan rama, saboda kunga ina kyale ku kuna sheke ayar ku......Yana kaiwa nan yaji kamar motsin Sofia daga cikin ɗakin.

12:30pm

"Anna" Anna"
"Anna kai na ciwo" "Anna"

Shine abin da nake maimatawa idanuwana a rufe saboda nauyi da suka min kai na ma yayi nauyi, buɗe labulan da akayi hasken rana ya haska min fuska take yanke na buɗe kuma runtse idon a hankali na rufe da hannun na tashi zaune ina sake kallon ɗakin da ma mutumin da ban isa na gane ko shi waye bane.

Ihu na tsala yayi saurin rufe min baki da hannu yana cewa ,"Sofia am"

"Sofia na"
"Ni ɗin mahaifin kine na asali, baki sanni ba ko" Baffah da Anna basu san faɗa miki ne saboda kar ki dena son su"

"Na ture sa da karfin da Allah ya bani,
Tuna yadda akayi aka ɗauko ni lokacin dana shiga ɓan ɗaki, wata mata na gani tana uzurin ta, na nemi taimako akan ta taimaka min zanyi fitsari, ta taimake ni amma daga karshe ta shaka min wani abu daga nan kuma ban sake sanin in da kai na yake ba sai yanzu" Na share wani hawayen da suka zubo min na ɗaga idanuwa na na kalle shi" Na ce ,"Anna ta faɗa min komai, Aunty Hadiza da bani labarin komai, Duk irin tsanar da kayi mana a baya bai ishe ka ba, shine ka sake rabani da farin cikin rayuwata"

"Me kake nema ne a duniyar nan ABHI"

"Ya juyo da rinannun idanuwan sa gare ta jin sunan Abhi data ambata, ya ce,"Duk dacewa na muzguna wa rayuwar ku Sofia and yet ina da muhimmancin da zaki sake kallo na ki kira ni da wannan sunan???

"Ka zalunce mu ka zalunci Ummu yau ina Ummu, yau ina Laila matar daka fifita da mu, yau ina Ƴaƴan daka fi so kayi rayuwa da su, Sageer yana cikin daular Anna da Baffah, Nainah Tana Germany yayin da sauran suna karkashin kulawar Anna da Baffah wanda suke gaban Sageer da Nadiya ƴar Alhaji Lawal", Na sha majinar hanci na, na cigaba da cewa a tunanin ka Baffah da Anna mugunta suke maka......Kai kayi kutso cikin rayuwar su, kuma Allah ya gama sanya ma rayuwar su albarka tun da ya haɗa mu da su kuma suka rike mu da zuciya ɗaya, sun fi min komai a duniyar nan, amma ako da yaushe ina maka kallon Mahaifi na, Mahaifin da........"

"Ya isa haka nan Sofia, Idan kowa ya guje ni don Allah ke ma karki guje ni, Dake da Hadiza kece wacce a ko da yaushe nake mafarki dake, walau Allah zai gafartamin idan na kyautata miki, duk da na sani yanzu Hadiza da wuce wajan bata bukata ta, amma ke fa har yanzu kina cikin kuruciyar da zan kula dake kamar yadda kowani mahaifi yake kula da ƴaƴan sa"

Hawayen bakin cikin da suke zuba daga kwarmin idanuwa na sune suka canja launi zuwa Hawayen farinciki saboda komin lalacewar Uba akwai jini mai tafiya kaman teku wanda ya ke kunshe da soyayyar uba da ƴaƴan sa a yau duk wani laifin da Abhi yayi mana a baya wannan kalmar kaɗai d akuma hawayen da suke sauka daga idanuwan sa su suka shagalar dani suka jefa ni cikin kogin da ban isa na ce zan rayu ko ba zan rayu ba.

SOFIA Where stories live. Discover now