SOFIA
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Page_20ANNA SPECIALIST HOSPITAL
8:00am
Fulani Mami ce ke ta safa da marwa ta gama waya da ƙanwar mahaifiyar ta wacce ta ke Maitama district ta shai da mata idan sun gama da asibitin za su karaso ta gidan.Bayan ta gama ne ta hau kiran wayar Mai martaba tana tsaye a corridor kofar ward ɗin da Omar yake ta na neman network so ta ke ta yi waya da Mai martaba ta sanar da shi cewa jikin Yarima da sauki. Daga cen nesa da in da take kasancewar safiya ce sai take jiyo muryoyin wasu Nurses mata biyu da kuma wasu mutane.
"Nurse Grace ga ƴan uwan masu gawan nan da Dr. Anna ta ce a fito da ita"
"Okay su biyo mu muje ɗakin ajiye gawa"
Fulani Mami ta jiyo Nurses suna maganar ta ɗan wai ga don ganin mutanen da suka yi rashi wani dattijon mutum ne da ƴar sa matashiya sai matar sa dattijuwa, ta kauda kai tana niyan juyawa ne idanuwan ta suka hango mata wani mutum ta cikin glass mirrow ward ɗin dake kallon na su, tamkar Abbhin Sofia kwance saman gado an sanya mishi oxygen ga na'ura na ta aikin ta numfashin sa na tafiya da sauri sauri, alamar ba a hayyacin sa yake ba ya gama tabbata, sai dai abin ya ɗaure mata kai ta yaya Abhi har ya taho nan Abuja kuma yaushe a kai addmitting ɗin sa, wata zuciyar ta ce baki da amsar waɗannan tambayoyin ki bari zuwa anjima kila zai farfaɗo ai sai ki dawo, haka nan ta koma ɗakin da ɗan ta yake.
MALE WARD VIP2
Kwance ya ke yana danna wayar sa, chatting yake da Andrew da Leo dai dai lokacin da Mami ta shigo jikin ta a sanyaye ta zauna saman kujera tana cewa,"Ka tashi daga baccin Yarima?"Eh Mami, Mami ni fa na ji sauki sosai tun shekaran jiya kuke bani candy amma sam ciwon bai sake ni ba sai yanzu da likitan nan ta bani magani, farat ɗaya na warke gani cikin koshin lafiya"
Mami ta yi murmushi ta ce,"Babu damuwa nima dai ina jiran likitan ne na ji ance bata jin daɗi amma anjima zata iya zuwa, so i don't know maybe zamu kara ko da kwana ɗaya ne zuwa gobe sai mu koma"
"Allah ya kai mu, amma Mami ina so idan mun koma, zan tafi na fara processing dream ɗina as you know buri na na zama Astronaut yana nan daram"
"Ya ya za kaji da ƴar mutane Omar?
"Ai ba zan wulakanta ta ba kamar yadda na ɗau alkawari, amma na sha faɗa miki da akwai wacce nake tsananin so cikin garin abuja idan na same ta zan aure ta In Sha Allahu"
"Hmm Allah ya tabbatar mana da alkhairi,amma kana da tabbacin ita ma bata yi aure ba"
"Mamiiiii" ya faɗa yana jan sunan ya ce,"Mami zan jaraba duba ta kafin mu koma, mu bari sai jibi kinji Mami""Allah ya kai mu" har ta yi shiru sai kuma maganar Abhi ta faɗo mata arai, tana wannan tunanin lambar wayar Mai martaba ta shiga, bugu ɗaya biyu ya ɗauka yana sallama cike da ɗokin kewar su ya ce,"Fatan kun isa lafiya?
"Lafiya lau yallaɓai Abban Omar, ai tun da muka iso network ya ɗauke cak"
"Madallah, don nima nayi ta gwada layikan ku har da na Omar ban samu ba jiya amma yau kam ban gwada ba"
"Sai yanzu muka samu network"Cewar Yarima Omar yana daɗa matsowa don jin abin da Abba zai ce.
"Ma Sha Allahu, Omar waraka ta samu to to to Alhamdulillah" Duk suka amsa da amin sannan suka yi hira kaɗan daga bisani Mami ta ce,"Ni kam Mai martaba nace, kun dubo Abhi kuwa mahafin sofia?
"Eh mun duba shi amma an samu akasi domin kuwa ya riva da ya tafi Abuja shi ma" Mai martaba ta bata amsa ta na daɗa gyaɗa kai sannan suka yi sallama ta kashe wayar gaba ɗaya hankalin ta ya soma ta shi da lamarin "babu makawa Mahaifin Sofia na gani" babu zato babu tsammani maganar ta dira cikin kunnuwan Yarima Omar ya ce,"Kin ga Mahaifin Sofia, wacce na ke nema fa itama sunan ta Sofia amma ita tana da iyaye kuma a lokacin fa Mami har da ke muka ganta amma na san ba zaki tuna fuskar ta ba, Maman ta likita ce sunan ya ɗan shi ge min amma a asibitin Maitama muka haɗu"
YOU ARE READING
SOFIA
Short StoryNakasar rashin ƙwarin ƙafar da Sofia za tayi tafiya ita ce KALUBALE da kuma JARABAWAR da ta shafe kowacce jarabawa zafi da ciwo.Binchiken likitoci sun gane cewa Kafafuwan Sofia tun a cikin cikin mahaifiyar ta suka samu rauni wanda hakan ya samu sil...