Shafi na Goma

12 2 0
                                    

SOFIA
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Shafi na Goma

*Rayuwa juyayi*

Yau kimanin watanni uku kenan da rabuwa da Anna da Baffah da kuma ƴan uwa na.
Ban taɓa tunanin zan iya sadaukar da buri na ba, ban taɓa tunanin zan iya sadaukar da mafarki na ba, ban kuma taɓa tunanin rayuwata ta kare dasu Anna ba sai da na gannin tsullugudum cikin Jahar Jigawa State zaune a kasa gefen titi, Saukar mu kenan daga mota, a wannan halin da nake ciki ma babu damar tafiya saman keken guragu, babu damar tafiya saman wheeel baro kamar kwanakin baya da ABHI yake kokarin turani da wani baro shima aro yake karɓa duk kwana ɗaya naira ɗari.

Daga wajan dana ke zaune, na hango mashina da motoci suna kai da komo a babban titin Local government, gefe ɗaya ƴan makarantar GGUSS Malam madori Government Girl Unity Secondary School, Kowacce ɗaliba tana jiran iyayen ta ko ƴan uwan ta su zo su ɗauke ta, Yayin da ɓangaren hagu kuma masu mashina ne suka jera kansu daga gefen su kuma masu saida abinci ne kama daga kan shinkafa da wake da miya, da mai da yaji, da taliyar hausa da manja da yaji sai ɗan wake da man kuli da yaji.....Maganar Abhi ita ta dawo dani daga dogon tunanin dana faɗa, "Sofia me zakici na siyo miki?

Abhi akwai ragowar kuɗi a hannun ka ne?

"Eh Akwai Dubu ɗaya ai Sofia, Jira ni naje na siyo mana" Na gyaɗa kai ina wasa da yatsun hannaye na, ina kuma lankwasa kafafuwa na da suka min tsami saboda zaman mota, duk dama ba tafiya nake yi ba, amma naji jiki saboda ban taɓa doguwar tafiya a mota haka ba.

Da kyar muka samu mafaka a ranar..A runfar mai shayi muka kwana da safe kuwa yana fitowa ya surfafa mana zagi daga ni har Abhi,"Dallah malam ka bar nan kar ka raina mana hankali, ka kara gaba nace nan ba wajan fakewa bane,"A kara gaba don Allah"

Cike da bakin cikin zagin da yamana kafin wannan maganar ta fito daga bakin shi, naji ina ma ina da kafa gau da sai na sharara masa mari amma babu damuwa, Jan hannun Abhi nayi ina cewa, "Abhi nah rabu da shi muje kawai"

Abhi ya kalli gabas, kudu da arewa, ya rasa ta ina zai samomin baro, saboda yana tsoron kada naji ciwo don idan zan daure nayi tafiya dole sai dai na ja bom bom ɗina har zuwa in da zamu, domin na masa nauyi ya ɗauke ni.

Tsugunnawa yayi yace,"SOFIA hau muje".....Kallo na bishi da shi Shin meyasa Abhi yake yimin wasu abubuwa kamar Baffa, hakika idan ina tare da Abhi wani lokacin nakan ɗauka Baffah ne saboda yanayin yadda shima yake kula dani kwatan kwacin yadda Baffah yake min.

Da kyar muka samu mafaka, wani barandar shaguna muka zauna idan suma basu kore mu ba kenan, Abhi yace min najira shi yana zuwa. Zaman da nayi har na samu Dubu ɗaya a bara, yana dawowa na mika masa ina cewa ga abin da na samu, yace" Na rike mana yana zuwa.

Ina kallon abin da yake yi, Katako ya siyo sabo dal, ya samu dutse mai kyau ya siyo kusoshi masu malfa, ya zauna ya buga min katakon harda kananan tayoyi, yana aikin yana zufa na rarrafa na isa gare shi ina goge masa zufan goshin sa da gefen ɗan kwalin da nayi lulluɓi da shi.

Da misalin karfe uku 3:00pm ya gama bugawa abin yayi kyau matuka har da dogon sanda wanda za a rinka ja ana tafiya, Ya ce,"Sofia zauna mu gani"

Ina zama kuwa Abhi ya fara jana, zir zir zir muke tafiya kaman abin wasan yara...ban san lokacin da naji hawaye daga ido ɗaya ya sauko ba tsabar jin daɗin abin da Abhi yayi na rungume sa ina ce masa "Nagode Sosai"

Ranar ma samun rumfa mu kayi muka rakuɓe, har gabanin asubahi, Abhi yana kara bani hakuri akan gobe da yardar Allah zai kama mana ɗaki amma sai yace banki ya ciro sauran kuɗin gidan sa da ya siyar.

Babu abin da yake zuwa zuciya ta sai tunanin ƴar uwa ta Hadiza da Ummu na bana iya tuna komai sai tsirarun abubuwan da ba a rasa ba....daga cikin rayuwar da muka yi da ƴar uwa ta lokacin da muke tsaka da bara, yau gashi na sake dawowa right from where i start.

SOFIA Where stories live. Discover now