Sha_Huɗu 14

12 2 0
                                    

SOFIA
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Page_14

SOFIA POV
10:40am

Cikin matsakaicin gidan na mu, ɓangaren da ya kasance nan ne muke duk wasu wanke wanke kama daga kan kwanoni, tufafinmu da sauran kayan aikace aikace.

Ɗauraya nake ina matse ruwan jikin ko wani kaya ina ajiye su a gefe, Mmn Ummi tana gefen sashin nata ta kunna murhun gawayi tana sanwar miya. Yayin da Ummi ke wani ɓangare na barandar sashin nasu tana wasan ta.

"Maman Ummi taimaka a shanya min na gama matse wa"

"To gani nan, bari na karasa ɓare maggin nan"
"Toh ba damuwa" na amsa ina cigaba da matse sauran kayan.

Maman Ummi ta ce,"Sofia don Allah yau ki zo muje bikin nan jiya fa kamu kawai a kayi amma kin ga ɓarin dukiya yau da har da ke ba karamin kuɗi Abhi zai samu ba"

"Ni fa Maman Ummi bani kaunar zuwa gidajen masu kuɗi musamman inda ban sani ba.......zuwa na ko ba zuwa na zamu samu kuɗi ko ba a gidan sarakuna ba, iya wanda Al'umma suke bamu ya wadatar" na bata amsa.

"Amma ni ina so ne dai ke ma ki san ɗabi'ar jihar dutse da kuma al'adar masarautar dutse, kuma yakamata ki san yadda masarautar dutse take"

Masarauta masarauta, ni fa Maman Ummi na fara gajiya da labarin masarautar nan, har ya fita kaina"......gwara gwara ma kilisan dawakai zani taron ni da Ummi idan kin yadda ke kuma sai ki tafi gidan sarkin ki"

Na faɗa ina dariya na cigaba da cewa,"Na ji ana sanarwa a gidan radio ma ɗazu da safe da Abhi ya kunna radio sa, wai za suyi kilisan manyan dawakai daga sassa daban daban cikin jahohi uku, masu kiwon dawakai.

Maman Ummi ta gyaɗa min kai tana cewa," amma kilisan bana so saboda wani lokacin ana samun hatsari duk da ba'a fata amma kin san dole mutum ya guje ma faɗawa halaka"

"Ni kuma na fi son kilisan, you know why? Maman Ummi ta girgiza kai.
"Saboda ina son doki, musamman farin doki, kuma ranar naga wani a saman farin doki, da ina da kafa da sai dai kawai yaga na hau ko magana ba zan masa ba"

Maman Ummi ta kyalkyace da dariya, "Gaskiya kina da abin dariya, duk garin nan babu wani mai farin doki face Yarima Omar, na san shi kika gani, Ɗan sarki guda, Lallai Sofia kina so a kama ki a kulle ki cikin ɗakin duhu kenan"

Na taɓe baki na ce,"In dai saboda Farin doki ne zan yi fiye da haka ma," na faɗa ina tuna shekarun baya da muke zuwa museum da Baffah, babu kalar dokin da bana gani haka Baffah yake ɗaura ni mu hau tare, yayi ta min hoto. na share wasu zafafan hawaye gefe guda na karasa matse kaya kala ɗaya da ya rage sannan na kwashe robobin na ɗauraye wajan, Da kyar na ja katako na na koma kofar ɗakin mu ina share wasu hawaye da suka zubo min.
Ranar da na fara hawa doki.

1212 POLO AND TURF RESORT
ABUJA
FLASH BACK

Waje ne wanda aka tanadar domin kiwon dawakai da kuma koyar da yadda zaka hau doki har zuwa iyawarka.

Da ga cen ɓangaren da ake koyon hawa dawakai, tsaye nake wajan saƙagon dokin da aka kera shi da katako, Baffah ya sauke ni yana cewa,"Saura mu hau favorite ɗin ki White Horse" Nayi murmushi a tunani na abin babu tsoro ko da Baffah ya ɗaura ni sai ya koma gefen Anna yana zuba min iadanuwa na ya ga yadda zan yi.

"Baffah!! Baffah!!!!!! Ahhhhhh a zo a sauke ni, ni ka bana so, kasancewar kafafuwana basu da karfin da zan iya matse dokin kar ya yarda ni sai na rike ma dokin jelar gashin kansa, na kuma chikwikwiye shi da hannaye na sannan na kwanta a kafaɗar sa na setu da kyau....ina jin yadda Baffah da Anna suke min dariya.
Idanu wa na a rufe suke, a hankali na soma buɗe su ina kallon Anna ta na min murmushi, motsin da naji ne a baya na ya tabbatar min Baffah ya hau dokin shi ma, sai na mike na yi relax ina mai da numfashi.

SOFIA Where stories live. Discover now