15

41 2 0
                                    

SOFIA
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Page_15

HATCH FOREST PARK,
United Kingdom
12:20am

Tsakiyar kurmi ko in ce dajin da babu komai a cikin sa sai tarun bishiyoyin da suka gaji da tsayi suka haura saman gajimare, tsananin bakin duhun da ya mamaye kurmin ya isa ya tabbatar maka da gabatowar dare mai cike da firgici da razani.

Karo na ba adadi take jiyo muryar ƴar uwar tata, tana ihu tana kiran sunan ta, amma ta gaza gane ainahin sashen da zata samu ƴar uwar tata, "Aunty Hadiza ki zo ki taimake ni, Aunty Hadiza ina tsananin cikin damuwa, Aunty hadiza ina bukatar taimakon ki"

"Wayyyyooo Allah Aunty Hadiza zasu kashe ni......sai kuma muryar ta fashe da kuka mai tsuma zuciya da tsananin tausayi, Wanda ya kara jefa Hadiza cikin matsanancin damuwa ta dafe kan ta da hannayen ta ihun na shiga kunnuwanta tana cewa,"SOFIA ina kike, Sofia na kasa ganin ki, Kanwata Sofia gani nan zuwa zan tamaka miki, ki kwantar da hankalin ki babu abin da za su iya miki da yardar Allah"
1...2....3........
Buɗe idanuwanta tayi ta tsinci kanta kwance cikin ɗakin ta saman gadon ta, Idanuwanta na kallon saman ceiling da sauri ta mike zaune tana mai da numfashi ta fahimci mafarki take yi gaba ɗaya duk ta haɗa zufa, a hankali ta duba agogon dake gefen bedside ta gadon karfe 07:10am Share wasu zufan dake saman goshinta tayi tana cewa yau time ya wuce haka ga su Asad zasu makaranta, ya akayi ma baccin safen yayi nauyi ne haka, fuskar ta kawai ta wanke a babban washroom fankacece Sa'annan ta sauka ƙasa, A hankali take jiyo muryoyin su cike da raha da farin ciki.

Asad ne yake kiran sunan Daddy! Daddy!!! Me, Daddy me opppss Daddy i don't want this, i simply want milk chocolate you know it's my favourite hannn"

Asad ɗan shekara goma sha ya faɗa yana ta tsalle yana kokarin kar ɓan chocolate a hannun Ahmad, yayin da Minal ke ta musu video tana dariya daga karshe wayoo tayi ta zagaya ta karɓe ledan milk chocolate ɗin tana cewa,"Yeeeeeehhhh i got it" ta gudu bayan ta ajiye camera ɗin ta hau saman matakalar bene tana cewa,"It's Mummy"

Rungumar da aka yi ma Hadiza ne ta dawo da ita daga firgicin mafarkin da yake ta mata yawo a kwanyarta, ta na sauka daga saman matakalar benen ta janyo Minal tana cewa," Chocolate is not good for your health Minal"......Ta karɓi Chocolate ɗin tana cigaba da cewa,"Good morning Yaya Ahmad"

"Morning my wife" ya faɗa da murmushi a fuskar sa, "How was your night? Ya tambaya.

Maimakon ta amsa shi sai ta kai duban ta saman mini stool ɗin dake wajan, yawan kitkat chocolate, da Milky Candy, Milk chocolate ne a saman wajan da alama yau sun ɗaga masa hankali kenan. Ta karasa wajan tana cewa,"Har kun shirya ne Asad, babu wanda zai ɗauki chocolate, duk sai kun dawo daga school" ta faɗa tana kwashe sauran dake saman table ɗin tana kallon Ahmad ta ce,"Aikin ka ne ai na sani, kai ne kake basu chocolate Yaya Ahmad, Ka shirya musu Lunch box ne?

"Tun yaushe kuma, ai mun ga kina ta bacci yau dukan mu mu kayi aikin breakfast da launch" Cewar Ahmad yana zagayo wa ta bayan ta yana rungume ta ya manna mata peg sannnan ya kwace chocolate ɗin yana cewa,"Guys i got the chocolates let get out of here" duk suka bi bayan sa suna gudu suka fice daga falon, Hadiza ta girgiza kai tana cewa,"Uhmmm Bye" ba zan iya da dramar ku ba Yaya Ahmad" Hadiza ta faɗa tana kwashe kayan da suka zubar a falon tana gyarawa, ta shiga kitchen nan taga yadda su kayi kacha kacha da kitchen, cake an yanka an bar rabi, chocolate jar ɗinnan sun ci bread da shi, anyi soye soye chips, fried egg, cake sandwich da sauran su, haka ta gyara a hankali tana nazarin mafarkin da tayi, bayan ta gama duk wani aikace aikacen ta tayi wanka ta shirya sannan ta janyo laptop ɗin ta kunna ta kirawo Anna video call.

"Good afternoon Anna"
"Afternoon Hadiza ya kids" Anna ta amsa tana sake tamabayar ya yara, sai dai kallon Hadiza take kamar me neman wani abu a fuskar, da sauri ta ce,"Kina cikin damuwa, na ga alama kwance a fuskar ki, Me ke faruwa?

SOFIA Where stories live. Discover now