SOFIA
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Shafi na TaraNEW YORK CITY
NEW YORK UNIVERSITYKwance yake saman lallausan gadon sa mai shimfiɗe da zanin gado white and duvet milky color da wasu lostsatsun pilluluka sama da huɗu irin gadon nan da baza ka so ka tashi daga bacci ba. Bedside ɗin dake gefen gadon mai ɗauke da lamp masu kawo wuta dark blue, milky and white color kasancewar ɗakin yayi duhu duhun asubahi wutan sai ya bada kala gwanin birgewa. Wayar sa kirar Samsung ya tashe shi daga nannauyen baccin da ya keyi wanda tuni ya fara motsi kai kace babu mutum cikin wannan lallausan gadon.
A hankali cike da natsuwa ya sanya hannu ɗaya ya ɗauko wayar yana buɗe sexy eyes ɗin sa wanda suka koma launin ja alamar yayi bacci sosai.
*Mai martaba *
Shi ne sunan da aka rubuta kan fankacecen screen ɗin wayar wanda ya sanya ya ɗauka yana kara wayar a kunnen sa tare da sake kwantar da kansa saman pillow ɗin yana mai da numfashi silently.
"Assalamu alaikum Yarima"
"Amin wa'alaikumus salam" Barka da dare Mai martaba" Ya faɗa ba tare da ya duba agogon ɗakin nasa ba saboda ya san agogon Nigeria yanzu dare ne."Lafiya lau Yarima muna nan Fulani ta ɗaga man hankali sai na kirawo ka da layin da muke kiran ka"
"Uhmmm Hmmmm" kawai ya iya furta wa yana daɗa saurarar Mai martaba, a hankali ya ce,"Mami i missed you, nayi kewar abincin ki da komai ma"
"Nima nayi kewar ka Yarima na, kana linke kayanka da kyau kuwa?, Kana tsaftace ɗakin ka dai ko Yarima?, Kana karatu da kyau?
Tambayoyin da take jero masa su suka sanya shi ya kara wastsakewa daga baccin da ya keyi, Ji yayi ta sake wata tambayar "Yarima fatan kana ibadan ka da kyau, baka barin sallah ta wuce ka?
Wannan tambayar ta sanya shi duba agogon bangon ɗakin nasa wanda yake nuni da karfe shidda da rabi 6:30am ya shafa sumar kanshi yana tuna ko sallar asubahi bai samu damar yi ba, ya kai duban sa saman tebur ɗin karatun sa wanda cike yake da tarkacen littafai, Ya tuna karatun da yayi jiya wan da dalilin haka bai kwanta da wuri ba gashi ya makara sallah.
Cikin sakan uku yana wannan tunanin Mami ta sake cewa,"Yarima ko dai soyayyah ka fara ne? Na ji kayi shiru ne.
Sai a sannan yayi murmushi wanda ya kara fito da ainahin gashin gemun sa da sajen dake kwance lublub a fuskar sa sa'annan ya ce,"Mami ina Othman ne baya kewa tane?
"Ga Othman nan sai bajakolin sa yake saboda yaga baka gida"
"Hahhhhh ki ce masa yayi iya yin sa zuwa wata shekara dai na kammala degree ɗina na farko zan ɗaura da karatun mafarki na kafin na dawo In Sha Allah, sai mu hau sararin samaniya da shi"
Mai martaba na jin su yayi dariya ya cigaba da abin da yake yi, yayin da Mami ta cigaba da magana da ɗan nata. "Ya kamata dai ka dawo Yarima saboda kowa yana son ganin ka, Kaji Yaro na"
"Maaamiiiiii" Yarima ya faɗa da sigar shagwaɓa, ya cigaba da cewa,"Zan dawo Mami ko dan na ganki hankali na nima ya kwanta"
"Ohhhhh baza ka dawo saboda ni ba kenan? Mai martaba ya faɗa yana mai kara kunne a wayar shima.
"Abba na, na kai nah, ni na isa taka warka lafiya Mai martaba sarki Abban Yarima Omar da Othman, Mijin Fulani Mami da Fulani......." Sai kuma yayi shiru wanda ban san dalilin shirun nasa ba.
Sukayi dariya daga bisani suka shiga hirar rayuwar ɗan nasu, ganin Fulani Hadejia ta shigo sai suka kashe wayar suna mai kewar ɗan nasu.
Tashi yayi bayan yayi wanka yayi sallah, ya shirya cikin native ya fito tsab da shi shigan hausawa yau yayi, yana tsaye bakin ɗakin nasa ya hango Rajvir yana nufo in da yake, jiran sa yayi suka karasa a hanya suka haɗu da Leo da Andrew sannan suka haɗa kai suka shiga aji
YOU ARE READING
SOFIA
Short StoryNakasar rashin ƙwarin ƙafar da Sofia za tayi tafiya ita ce KALUBALE da kuma JARABAWAR da ta shafe kowacce jarabawa zafi da ciwo.Binchiken likitoci sun gane cewa Kafafuwan Sofia tun a cikin cikin mahaifiyar ta suka samu rauni wanda hakan ya samu sil...