16

3 1 0
                                    

SOFIA
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Page_16

Masarautar ya cika makil da ƴan uwa, haka zalika duk muhimman mutanen da fada ke bukata sun hallara ban da mutum ɗaya ko wane ne shi?

********
Dare ne mai ɗauke da farin wata, da kuma taurari masu sheƙi da ɗaukan hankali, yayin da ko'ina yayi tsit baka jin motsin kowa balle komai, Zaune yake daga bakin kofar ɗakinsu ya harɗe gwiwa ya sadda kanshi a kan gwiwar sa yayin da ya yi ma hannayen sa zagayen zobe da kafafuwan sa haƙiƙa yaji duniyar tayi masa ɗaurin talala, ta yi masa ɗaci bai taɓa tsammanin abu makamanci haka zai riske shi a wannan rayuwar ta shi ta yanzu ba, bai ta ɓa tsanar munanan laifukan da ya aikata ba har jarabawar rayuwa ta mai da shi haka in ba yau ba, yanzu da wani ido zai kalli ƴar sa da aka yi ma baƙin tabo, ta yaya zai goge wannan baƙin tabo mai zafi da raɗaɗi a cikin zuciyar Sofia.

"Abhi shikenan yanzu kowa zai yi ta kallo na da baƙin tabon da ya same ni? Dashashiyar muryar sofia wacce taci kuka ta soma magana daga cen kusurwan ɗakin ta duƙunƙune jikin ta.

Tamkar wanda aka daki ƙirjin sa da gungumen dutse haka Abhi ya dafe ƙirjin sa wanda yake masa suya,Jikin sa na jingine da bangon kofar ɗakin sa, babu abin da yake masa yawo a ƙwanyar sa face yadda yaje ya ɗauko ƴar sa ko tufafin kirki babu a jikin ta sai hijabi, sautin kukan ta ɗaya yana tunasar da shi da rabata da iyaye masu ƙaunar ta da tsananin kula da ita, yanzu mice ce ribar shi, na farko ya ruguje ma Sofia mafarkin goben ta, na biyu ya raba ta da jin daɗi na har abada tare da su Baffah, na uku ya kasa bata kyakkyawar rayuwa mai inganci da tsaro yanzu wa gari ya waya?

Tambayar da Sofia ta yi masa ita ta dawo da shi daga ainahin dogon tunanin da ya tsunduma a dai dai wannan lokacin wasu zafafan hawaye suka fara tseren fitowa daga ƙwarmin idanuwa sa, lokaci ɗaya ya miƙe ya hau zuba kaya cikin karamar jakkar su.

"Abhi ina zamu kuma?

"Sofia na zan mai da ke wajan su baffah ne, ban cancanci zama uba mai baki kariya ba ƴa ta"

Da mamaki Sofia ke kallon Abhi, wajan su Baffah shin murna za tayi koko baƙin cikin abin da zata je musu da shi? wani ɓangare na zuciyar ta kuma ta tausaya ma Abhi duba da yanda yake ƙokarin zama mutum na gari a dalilin ta a kusa da shi, ba ya da kowa a yanzu idan ta tafi wa zai rinka kula musu da mahaifin su?

"Abhi ah ah"ba zan koma ba", Babu in da zanje na bar ka kai kaɗai"

Tausayin Sofia ya kama Abhi ya rungume ƴar ta sa, yana cewa faɗa min Sofia ina kike so na kai ki , na miki alkawarin zan yi iyakar bakin ƙoƙari na na samo kuɗin da zan kula da ke" Na miki alkawarin ba zan sake fita dake bara ba"

Na share ma Abhi hawayen dake fuskar sa, na murmusa, sannan na ce,"Abhi ni fa musulmace kuma na yadda da ƙaddara mai kyau da mara kyau", Cikin zuciya ta na ce Meya sa har yanzu ƙwanya ta ta kasa mantar da ni fuskar Yarima Omar gangar jiki na yana bani tamkar na taɓa ganin sa a wasu wurare da ban. a fili kuma na ce,"Ba dan Allah ya kawo shi da gaggawa ba da watakil yanzu ana ta kuka ana jiran gari ya waye a kai ni makwanci na"

"Shi ɗin tamkar adali ne a cikin rayuwar ki, duk mutumin da zai maka kwatan kwacin wannan taimakon na ceton rai to tabbas yakamata shi ma ka saka mi shi da alkhairi wata rana"

"A ina zan gan shi domin na gode masa? Babu ɗan sarkin garin nan ne Abhi kuma ma ɗazu naga yadda ran wani mutum ya ɓaci ko shi ne mahaifin sa domin kamannin su tamkar an tsaga kara" Sofia ta tambaya

"Bana tantama amma kin san ni ba sanin mutanen fadan nan na yi ba, ka wai dai ina ganin mutanen mu dake ciki suna aiki a matsayin haɗimai su kawai muka sani"

Na gyaɗa kai a hankali na ja jiki na karasa ƙasan kullin kaya na ɗauko abaya ta tana nan sabuwa dal don bana saka ta, na laluba cikin aljihun na ɗauko telescopes ina shafawa a hankali ina tuna shekarun da suka shuɗe, yaron da na sani lokacin muna kanana kamannin su ya ɓaci nesa ba kusa ba da Yarima Omar, shin ko dai shi bai gane ni ba kamar yadda ni nake ƙoƙarin gano shi. wata zuciyar ta bani amsa, Iska na wahalar da mai kayan kara kenan.

SOFIA Where stories live. Discover now