🌟。*。💗~ xXx
。💚。*。 。🌟
_*KURUCIYAR JIDDAH*_.
.💜'*。.🌟¨¯'*❤。。🌟
*HASKE WRITERS ASSO...* 💡
_*Story And Written By*_
© _*Asy khaleel....✍*_
_Dedicated To_
_*Jiddah Ja'o & Baby Afreen*_
1⃣0⃣
_Yau sati biyu kenan amma sam babu labarin Jiddah don goggo ta ga babu sarki se Allah , ta had'a kayan ta kaf ta d'au hanya zuwa rugar Ard'o ko Allah zai had'a ta da y'ar jikallen ta_ ......
" _Yaya Aliyu dan Allah ka shirya mana da sauri ,nifa wannan akwalar keken naka dashi da babu duk d'aya ne don tafiyar mu a k'afa ma zai fishi sauri_!
" _inna de tana daga gefe tana jin dramar tasu yayinda Aliyu ke galla mata harara yace " tunda haka ne se ke kitafi a k'afan ni ina bisa keken nawa_ " .............
_Wani dattijon unguwa ne ya dakatar da Goggo " haba Hamsatu! Yanzu idan kin fita ina zaki fara nemo ta? Nasan yaro irin Jiddah akwai shiga rai amma kuma addua zamu yi Allah ya bayyanar da ita in ba haka ba ke yanzu ena zaki fara nemanta ? Yarinyar da an duba duk fad'in Jakusko bata nan shine zaki kwashi hanya wai nemanta? Ai kawai rok'on Allah zamu shiga yi har Allah ya bayyana mana ita_"
" _Ayya de baba sabo? In ban je ba wa zai je min? Y'ar marainiyar Allah ,daman gata nan ba wani kwari gareta ba salam salam take kamar hawainiya , babu wuya in abu ya sameta ta shiga halin k'ak'a nikayi nikam bazan iya zama ba_
." _Da kyar baba dattijo ya shawo kan gwaggo suka koma gida duk tabi ta rikice_.....
***************
_Kai nifa na gaji da zama a kan wannan akwalar keken naka , meyasa bazaka tsaya mu huta ba? Da yanzu a k'afa ne da mun kai rugar Ard'o!" Cewar Jiddah dake faman gwaguyar goruba gami da kankance idanuwa saboda yadda fuskar ta ke fuskantar hantsi_.
" _Ke ki sauk'a mana ! Se ki taho da 'kafar taki! A haka nake son keke na don haka ni a kai zan tafi in kinga na sauk'a toh Paci nayi_!"
" _Me kuma paci_??"
_Ta tambaya tana k'ok'arin sauk'a daga keken_
_Yana nufin iskar tayan ya sace ya koma sakwa-sakwa shikenan se yak'i tafiya_."
_Dariyar mugunta ta tsaya yi yayinda Aliyu ya zuba mata ido har tana fad'uwa " lallai taya zata yi paci_!!"
_Cikin rashin fahimta Aliyu yace " Kamar yaya_?"
_A'a cewa nayi in baka kula da karangiya ba tayar zata yi paci_!" ................
*************************
_*Hmm Jiddodo tana shagalinta Ku biyo Asy danjin me Jiddah take shirin shiryawa*_
asykhaleel.Wordpress.com
_*ASY KHALEEL TA KOWA 👄*_
YOU ARE READING
KURUCIYAR JIDDAH
Short StoryLabarine mai cike da barkwan chi, nishad'antarwa da sanyaya rai.
