KURUCIYAR JIDDAH. Page 4

2.7K 178 0
                                        

🌟。*。💗~   xXx

。💚。*。      。🌟

_*KURUCIYAR JIDDAH*_
.💜'*。.🌟¨¯'*❤。。🌟
  

        *HASKE WRITERS ASSO...* 💡

_*story and written by*_
     _*Asy khaleel......✍*_

   _This Page Is Dedicated to_
      _*My Members- Asykhaleel Novels World , Dandalin Asykhaleel N Majalisar Asykhaleel Allah ya barmu tare*_

               4⃣

    Sosai take gudu kamar zata tashi sama ,  takalman ma ta cire su tana k'ira " kai me amalanke! Tsaya ka rage mana hanya " tun Ummulkhairi tana da k'arfin gudun har ta gaji ta zube a k'asa itama hakan tayi se maida numfashi take tace " Toh se mu tafi a k'afan mu kawai kuma wlhy duk inda naga lado mai amalanke sai na nuna mishi nima nice " tana magana tana tafa hannu Ana fari da idanuwa .  dijen baba tace " nidai tsoro nake ji dun baba in yasan na fito ranshi seya b'aci"

    Jiddah da ummulkhairi suka had'a baki wajen cewa " Dallah matsoraciya! In baza Kije ba tou ki koma nidai se na tafi rugar Ard'o ance d'an sarki zai zab'i budurwa kuma ni zai zab'a don haka  baran koma ba se har ya zaben!"

   Zaro ido Dije tayi tace " LA. LA LA! Wlh babu ruwana baba zai doke ni ni kunga tafiya ta ,  toh me ma d'an sarki zai yi dake ? Kin manta su Altine ? Duk daga rugar Ard'o suke ma fiki kyau wlhy gara kuzo mu tafi kawai dandali mu wuni a Chan !!

   Da baya baya ummulkhairi ke komawa tana fad'in " nima gaskiya baran je ba , ke dai kizo mu koma kinga can hayin gada wad'annan y'an iskan suke zama kuma ma nikam Inna ta aikeni shagon baba Dreba sai de ki tafi ke kad'ai"
Tsuka Jiddah ta ja " Mtsew! Toh se me?  Kuje ku d'in ni gaskiya barin koma ba ,kuma duk abunda na samo kar kusa rai , kuma se d'an sarki ya ce yana sona, zaku gani a doki Zan dawo  insha Allahu !!" Ummulkhairi ta mak'e kafad'a tace " oho kuma sai na fad'awa goggon ki!" Jiddah tayi fari da ido tace " in kin fasa !!" Nan sukayi hannun riga Jiddah ta tafi tana y'ar wakarta suma su Dije suka koma gida................ _*READ MORE*_

_*ASY KHALEEL TA KOWA👄*_

KURUCIYAR JIDDAHTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang