KURUCIYAR JIDDA.P2

4.1K 236 1
                                        

🌟。*。💗~   xXx

。💚。*。       。🌟

🌟。_*KURUCIYAR JIDDAH*_
.💜'*。.🌟¨¯'*❤。。🌟
  

     *HASKE WRITERS ASSO...* 💡

_*Story and written by*_
     _*Asy khaleel...✍🏻*_

_This page is Dedicated to_
  _*Miemiebee👄 & Queen Salmat 4d lurv*_ .

              2⃣

     Tafe take tana tsalle hijabin ya karkace wuyan yayi gefe hancin nan a bushe ,se waka take yi
        "  Ahayye wata tafi wata ! A gashi nafi goggo👯!
       👯 A kyau nafi goggo
      🎧🎧🎧🎧🎧🎧🎧🎧 ( Jiddodo ta maida goggo marainiyar wayonta 😅)

     Duk inda ta wuce sai sun yi dariya domin da ihu take wak'ar  ko a kwalar ta se tsallen ta take yi har ta kai wajen Malam labaran ta mik'a mishi kud'in tana Sosa 'keya tace " wai ka bani Hmmm me ma?" Malam labaran yace " Ashsha!! Kedai ban san ranar da za'a aiko ki ki yishi daidai ba, yanzu ki koma wajen goggo ki tambaya me za'a baki?

   Murguda baki tayi tace " Na tuna fa  kub'ewa da kabewa zaka bani" Jin haka labaran ya fahimta don yasan Aiken goggo baya wuce yakuwa don haka ya saka mata yakuwa da kabewa ya mik'a Mata , ta amsa tana dariya sannan ta cigaba da wak'ar ta...........

       Maimakon ta wuce gida se ta chanja hanya saida tayi nisa ta tsaya ta Kama kunkumi tace " yanzu ina ma Zan Fara zuwa? Yau akwai shan mangoro a lambu tunda goggo tace " in naga dama in tafi wasa na har dare yayi " 😅😅😅 CHAI NAWAWOO FOR YOU JIDDAH JA'O!!).

       A hanya ta iske k'awayen ta UMMULKHAIRI da DIJEN BABA se fama suke da rake dukan su takalman su d'aure a kunkumi da dankwalin su , da gudu ta k'arasa wajen su tana washe hak'ora ta ce " tsammin rake " ta langabar da kai kamar zata yi kuka ,ummulkhairi ta had'e fuska tace " ba wani tsammiki da zamuyi gaskiya bazai yiwu ba! Jiya da kika sai agwaluma ko kallon inda muke bakiyi ba 😏"

     Wani shu'umin murmushi Jiddah tayi ta juya kai tana dariyar mugunta ,da sauri Suka miko Mata raken alamar suna tsoron ta ,saida ta kusan shanye duk sannan ta mik'a musu kotar rake ta sakala hannun ta a kafad'ar su ta shiga tsakiya tace " kuzo muje lambun  baban Rabe mu tsinko mangwaro kuma wlhy duk yarinyar da ta sa aka Kama mu Sena babballa Mata kafafu , ba musu suka ce " eh wlhy muje , nan suka Kama hanya suna bin ta yayinda ta rik'e ledar yakuwa da kabewan tana shilla shi sama...............

        Shiru shiru bata dawo ba har bakin magariba ,goggo duk ta damu gaba d'aya ,har ta yi sanwa ruwa ya tafasa ya k'one har ta gaji ta kad'a kuka , ganin bata da niyyar dawowa yasa goggo ta zari hijabin ta tabi bayan Jiddah

    A zaure suka ci Karo da ita d'auke da ledar babu ko hijabi don kuwa ta dauro mangwaro cikin hijabin har yafi k'arfin ta , duk kuma ba wasu nunannu ba , suna had'a ido ta sa dariya tace

  " Ungo yakuwar ki! Nikam wlhy nauyi matsa min in wuce , wannan mangoron idan na saka su waje mai zafi zasu nuna , dan ma nasha guda biyar a hanya " tana magana tana Kutsawa cikin gidan ta bar goggo tsaye baki a sake , bata ce Kala ba ta d'auki ledar ta yi cikin gida ta zauna ta zubawa Jiddah ido tana kallon yanda take faman d'iban tuwon laushi daga kwarya ,ta koma kan tukunyan Miya duk rabin kifin ciki ta kwashe tazo gefen goggo ta zauna ta Fara daka loma 😂

      " Yanzu Jiddah wannan wacce irin rayuwa ce? Karfina yana k'arewa ke kuma kamar dad'a shashanci kike yi kina susucewa , fisabilillahi se yanzu bayan magariba zaki kawo min abunda Zan yi Miya? "

   Had'e rai Jiddodo tayi tace "Goggo wlhy babu kyau ! Ke da kanki kika ce in je in naga dama se dare ma in dawo "
Goggo bata san  Lokacin da ta Fara doka salati tana tafa hannaye ba " Jiddah ina ga kekam ciwon zuciya ce zata kasheni tun lokaci ne bai yi ba "
     Jin haka Jiddah ta ture kwanon tuwon ta kurma ihu tana tsalle , Wayyo goggo kar ki mutu , ki Bari lokacin naki yayi barin sake ba wlhy , kawai ma abunda ya saka muka dad'e tsinkar mangwaro muka je kuma se Ummulkhairi ta fallasa mu wawiya ita wai tsoron kadangare take yi , baban rabe ya fito da k'aton tumbin shi yana masifa shine muka gudo kuma fa ya gane ni !
    Kawai Kedai goggo ki shirya don gobe se ya had'u da ke nidai kar ki mutu don idan yazo ke zai fara nema................ _*READ MORE*_



_*ASY KHALEEL TA KOWA 👄*_

KURUCIYAR JIDDAHStories to obsess over. Discover now