🌟。*。💗~ xXx
。💚。*。 。🌟
_*KURUCIYAR JIDDAH*_
.💜'*。.🌟¨¯'*❤。。🌟
*HASKE WRITERS ASSO...* 💡
_*story and written by*_
_*Asy khaleel.....✍*_
_Idan kina nesa, ki matso kusa ki karba rabonki, page din nakine kawar arziki, ngd da so da kauna....Allah ya barmu tare *BASMAH ER LELE*.
3⃣6️⃣-4️⃣0️⃣
"Banda fitsara irin ta yaran zamani haka kawai da girma na zasu sank'ame ni bisa keke sannan su rantab'a da k'asa kamar bredi bugun k'ato? Ji yadda suka ji min rauni shed'anu y'ay'an kawai! Duk laifin Kuluwa ne yarinya kamar shed'anu sun mata fitsari a kunne?"
Goggo ce ke tafiya tana banbami zani na Jan k'asa tana zare idanuwa"
Su kuwa tafiya suka sha inda suka iso k'arshen hanyar wanda ta rabu kashi biyu,Aliyun yace su bi dama Jiddah tace hagu zasu bi Cewar ta tasan hanyar daga nan ,haka ta dinga ihu har seda ya bi ra'ayin ta suka bi hanyar dake hagu.
Tafiya suke har ya gaji ya sauk'a daga keken se faman ja yake ita kuwa tak'i sauk'a haka yake Jan keken da ita ga gajiya ga nauyi ga bala'in Jiddodo wai keken nashi akwala ce bata sauri.
Wuni suka kwashe a hanya Jiddah har da gyangyad'i wai bacci take ji se goshin magariba suka iso wani k'auye
Aliyu ya washe hak'ora tunanin shi sun iso k'auyen su Jidda yayinda ita kuwa mik'e wa tayi tana banbami.
"Kai ka daina wani washe hak'ora ni nan ba k'auyen mu bane kawai baka san hanya ba ka kawo ni wani k'auye k......."
Dakata wa tayi dalilin hango Altine y'ar Fulani ,tabbas bata manta fuskar ta ba dan yawancin ranakun kasuwa tana kai nono garin su Jiddodo aikuwa ta falfala a guje ta nufi inda ta hango Altine
"Jiddah! Jidda! Ki tsaya ni mana! Ina kuma zaki?" Aliyu ya tambaya yayinda ya haye keken shi yana bin bayan ta
"Toh ka taho mana! Se wani kwala min k'ira kake ai nasan wancan Altine sunan ta , zata nuna mana hanyar gidan mu" Cewar Jidda ba tare da ta nuna gajiya ba take gudun......
_*ASY KHALEEL TA KOWA 👄*_
asykhaleel.Wordpress.com
YOU ARE READING
KURUCIYAR JIDDAH
Short StoryLabarine mai cike da barkwan chi, nishad'antarwa da sanyaya rai.
