🌟。*。💗~ xXx
。💚。*。 。🌟
_*KURUCIYAR JIDDAH*_ .
.💜'*。.🌟¨¯'*❤。。🌟
*HASKE WRITERS ASSO...* 💡
_*story and written by*_
© _*Asy khaleel....✍*__I Dedicated This Chapter To All Fans Of *KURUCIYAR JIDDAH* Allah ya Kara so da kauna, Ina matukar jin dadin ganin comments dinku, Allah ya saka da Alkhairi...Asy Khaleel loves you so much_
1⃣1⃣-1⃣5⃣
_Tab'e baki Aliyu yayi sannan yace " wa ya fad'a miki k'arangiyar zata iya fasa taya har ta shiga tub_ ? "
_Cikin rashin fahimta Jiddah ta kama kunkumi " Toh in ba k'arangiya ba se meye zai fasa? Ai naga yana da tsini yawwa kamar bakin wannan budurwan taka wannan wanda tace min kuchaka d'in nan! Ai itama tsinin baki ne da ita! Toh me zai iya fasa tayan_?
_Tsaki Aliyu yaja " Mtsew! Ke dalla kina nan da kumatu kamar funkasau har kina zagin bakin wata! Ni kizo mu tafi! Kuma kar ki sake zagin bakin Jummai in ba haka ba nan zan barki inyi tafiya ta kura ta cinye ki ! Kinga kinyi biyu babu ke baki auri d'an sarki ba ke kuma baki koma gun goggo ba_ !"
_Ai kuwa nan Jiddah ta bud'e shafin kuka harda shure shure " Ni wallahi bazaka barni a nan ba! Kuma ai ba zagi bane tunda bance Uwaki jummai ba! Kuma ban ce Jummai jaka ce ba kawai fa cewa nayi me tsinin baki kawai ai kwatance ne yanzu kai in zan gwada ka ai cewa zanyi Aliyu me fason kafa_!"
" _Ke! Nine me fason k'afa_ !? 😳
_Lallai ma wannan yarinyar kinga hanyata kada ki kuskura ki biyo ni kinji na fad'a miki mara kunya kawai!" Haka Aliyu ya kama hanyar sa ya hana Jiddah biyo shi duk irin birgimar da take a k'asa ko a jikin sa yaja keken sa ya tafi_............
************
_Kukan ne ya isheta ga uban rana ta mik'e jiki fursu fursu tana tafe tana kuka takalmi d'aya a hannu tana me bin tayar keken Aliyu , wato hanyar da yabi da keken , sosai taci tafiya duk ta gaji don haka ta nemi gindin bishiya dan hutawa , tana zaune tana kallon wasu tsuntsaye hakan ya d'auke mata hankali se ji tayi murya daga bayan ta yace_...." _Ke ! Tashi mu tafi mara kunya kawai! " tabbas ko shakka babu tasan waye " Aliyu_!!!"
_Tsalle tayi gami da kwala ma sunan shi k'ira Aliyu!! Ashe daman ba tafiya kayi ba? Shine ka barni dan kura ta cinye ni? Me yasa ka barni? Barin sake zagin Jummai ba da gaske ni na fasa zuwa rugar Ard'o kawai ka mayar da ni gun goggo ta! Wayyo Allah Goggo ta_!!"
_Haka ta dinga ihu da shure shure da 'kyar Aliyu ya rufe mata baki " Ke! Kiyi hak'uri mana! Kuma kin fasa auren Yerima ne? Keda kullum maganar ki rugar Ard'o shine kuma saida kika iso zakice a maida ki gida_? "
_Tab'e baki tayi tace " toh kuma Ummulkhairi ma ta fad'a ai ni ba me kyau bace bare zabeni ba kawai ka mayar da ni gida! Wajen Goggo_!"
_Wani shu'umin murmushi Aliyu yayi gami da taya ta tahau keken shima ya hau suka juya akalar keken_........
_ASY KHALEEL_ 👌🏼
YOU ARE READING
KURUCIYAR JIDDAH
Short StoryLabarine mai cike da barkwan chi, nishad'antarwa da sanyaya rai.