KURUCIYAR JIDDA. P9

2.2K 147 0
                                    

🌟。*。💗~     xXx

。💚。*           。🌟

_*KURUCIYAR JIDDAH*_

.💜'*。.🌟¨¯'*❤。。🌟
  

     *HASKE WRITERS ASSO...* 💡

_*story and written by*_
    © _*Asy khaleel....✍*_

_This Page Is Dedicated To_
    _*NUCEEY LUV, Alhdlh Ina matukar murna da godia gun Allah daya baki ikon kammala Exams dinki lfy Allah yasa muga gud result,Amin*_

               9⃣

     _Tafiya suke se wak'ar ta take yi ko kallon inda yake bata yi ba tana ta kalle kalle chan ta hango mai rake_


  _Laah wlhy rake ne, kai nawa gab'a d'aya?" Me rake ya ce " naira biyar ne_


    _Da gudu ta kama rigar Aliyu tace " Rake zan sha" babu musu ya siya mata tana tafe tana sha duk ruwan raken yana zuba a jikin ta har suka k'arasa rafi_


_A hanyar su ta dawowa tace " Yaushe zaka kaini rugar Ard'o? Ina de ina da kyau ko? " bata k'arasa tambayoyin ta ba wata budurwa ta shigo gaban su tasha kwalliyar y'an kauye da jambaki da kwalli duk ta b'ata fuska se washe cinyayyun hak'ora take_


" _Ali ya kake , jiya baka je dandali ba me yasa_?"



_Shima Aliyu ya washe hak'ora ya ajiye tulun a k'asa yace " Aah ah ! Jummai Jummai!! Yau kece haka_ ?


_Jiya na gaji ne daga gona shiyasa ban zo ba" washe hak'ora ta sake yi tana wani rufe fuska tace " Kai Aliyu kai kam akwai iya aiki! Nasan ka da himma_!

_Wannan kuchakar kuma ina ka samo ta_??"



  _Jummai ta fad'a tana nuna Jiddah wanda yanzu kam hannun ta a kunkumi yake tana murguda baki kafin tace_ 😏


" _kai kai kai! Dan kiji ni ba kuchaka bace kuma wlhy se na fad'awa Inna_!"

_Ta juya zata tafi Aliyu ya d'aura hannu a ka yace Jummala kije zamu had'u a dandali_ ,

_ke Jidda ki tsaya mana haba Hauwa kulun majada!!" Ya d'au tulun yabi bayan ta da sauri sukabar Jummai se huci take_ ........... _*READ MORE*_



asykhaleel.Wordpress.com
_*ASY KHALEEL TA KOWA 👄*_

KURUCIYAR JIDDAHWhere stories live. Discover now