KURUCIYAR JIDDA. Page5

2.6K 168 1
                                    

🌟。*。💗~    xXx

。💚。*。      。🌟

_*KURUCIYAR JIDDAH*_
.💜'*。.🌟¨¯'*❤。。🌟
  

      *HASKE WRITERS ASSO...* 💡

_*Story And Written by*_
  _*Asy khaleel.....✍*_

_This Page Is Dedicated To_
_*Billyosh, Miss XOXO, Ililee, Maryam Yarmama, Xahra Bukar, Shuwa, Autar Hajia, Rokkie Kaxz & Xee Yabour*_.

              5⃣

    Tun tana tafiya cikin farin ciki tana ta wasan ta a hanya har ta daina tsabar gajiya, hantsi ya dubi ludayi 😂 cikin ta se k'iran ciroma yake amma sam bata daina tafiya ba, wannan Karon takalman nata ma ta zira su cikin gyalen ta ta d'aura a kunkumi yanzu kam ko kyallin d'an Adam babu a wajen gashi gero yayi tsayi sosai tsabar ta gaji bata san lokacin da ta zube a 'kasa ba gindin wata bishiya cikin gona ta Fara sharar bacci....

        Hasken rana ne ya hasko inda take ,ta zabura ta mik'e se mutsutsuka ido take tana k'iran " goggo " shiru babu kowa a wajen se kwanon tuwo da kuma wata kodaddiyar jarkar ruwa ta faro bak'ik'irin da ita, ai kuwa nan Jiddodo ta janyo kwanon ta hau suburbud'a loma kamar an aiko ta , ta gama ta sha ruwa sanna mik'e tana goge hannu ,Juyawan da zata yi suka yi ido hud'u da wani d'an saurayi a zaton ta duka zai kai Mata amma akasin hakan se yayi murmushi yace " tuwon ya ishe ki ne? " a hankali ta girgiza kai tace " eh! Kayi hak'uri yunwa nake ji" fartanyan hannun sa ya ajiye a 'kasa ya zauna yace " Zauna ki fad'a min daga ina kike? Kuma me ya kawo ki nan?
Tabe baki Jiddah tayi tace " Ni daga k'auyen mu nake , yana Chan baya da nisa sosai na manta sunan shi ma! Amma akwai goggo ,da labaran me kayan Miya ,da baban rabe da ummulkhairi da k........" Tayi shiru dalilin dakatar da ita da saurayin yayi yace " ya isa! Kauyen ku kawai na tambaye ki shine zaki Fara kirgo min sunaye barkatai haka? Toh yanzu ba wannan ba, kizo muje gidan mu wajen Inna ta  zata kula da ke ta dinga baki abinci kinji?"

    Mik'ewa tayi tana girgiza kai " Nifa rugar Ard'o zani , babu wajen wata Inna da Zan je!" Saurayin yace " rugar Ard'o kuma? Toh ai da nisa ,me zai Hana ki huta in yaso anjima in kaiki rugar Ard'o a keke na?" Washe hak'ora tayi tace " Laaah! Daman kana da keke? Gaskiya kaji dad'i ,toh muje gidan Innar taka in yaso se ka kaini rugar Ard'o gobe" sosai yayi murmushi ya mik'e yana kwashe kayayyakin sa ya daurata kan keken suka tafi.........

_*ASY KHALEEL TA KOWA 👄*_

KURUCIYAR JIDDAHWhere stories live. Discover now