🌟。*。💗~ xXx
。💚。*。 。🌟
_*KURUCIYAR JIDDAH*_
.💜'*。.🌟¨¯'*❤。。🌟
*HASKE WRITERS ASSO...* 💡
_*story and written by*_
_*Asy khaleel.....✍*__Daughter! Wia r'u? Ur page x here, Wanda yasha banban dana kowa, kowacce Uwa Tana alfahari da y'ar ta, balle idan y'ar ta zamo be biyayya ga Uwarta, Ina gdy ga Allah dayasa kika zamo y'a agareni, inasanki Ina alfahari dake, Ina rokan Allah ya albarkaci rayuwarki, Allah ya tsare ya karemunke, Allah ya bani ikon aurar dake ga Wanda ze kularmin dake fiye da wanda nake maki, y'a mai San uwarta, ai dole uwar ma taso y'arta.....Allah ya barmu tare my everlasting daughter, ILYSM *ASMY B ALIYU*_
2⃣6️⃣-3️⃣0️⃣
A bakin zaure suka had'u da jiddah lokacin da ya iso gida dan chanja kaya, zaune take a k'asa dirshan tana Sosa kai tana wasan y'ar charafke. Jin mutum tsaye a kanta yasa ta d'ago idanu tana kallon shi daga sama har k'asa sannan ta cigaba da y'ar charafken ta shi kuwa kwafa yayi ya shige ciki harda banke mata k'afa.
Ai kuwa nan abun nema ya samu, wai matar falke ta haifi jaki. Jiddah iya k'arfin ta tadinga kurma ihu kamar ranta zai fita hakan yasa inna ta fito ba shiri
"Me ya same ki? Meye haka kike kurma ihu kamar aljanar da ake k'onawa"?
A hankali cikin shagwab'a ta nuna Aliyu wanda tuni ya sa sauri ya k'arisa cikin gida dan yasan Idan Inna ta fara fad'a se Allah zai CeCe shi.
Da kyar Inna ta lallashi Jiddah amma wannan karon cewa tayi sam baza ta zauna ba wajen Goggon ta kawai zata je.
Nan fa Hankalin inna ya tashi dan
ba sanin inda za'a sami Goggon tayi ba ita kuwa ta d'aga wa kowa hankali yau ko gorubar lallashin ma tak'i karb'a.....
_*ASY KHALEEL TA KOWA 👄*_
asykhaleel.Wordpress.com
YOU ARE READING
KURUCIYAR JIDDAH
Short StoryLabarine mai cike da barkwan chi, nishad'antarwa da sanyaya rai.