KURUCIYAR JIDDA.P7

2.3K 153 0
                                    

🌟。*。💗~   xXx

。💚。*。       。🌟

_*KURUCIYAR JIDDAH*_
.💜'*。.🌟¨¯'*❤。。🌟

  

    *HASKE WRITERS ASSO...*

_*Story And Written by*_
    © _*Asy khaleel.......✍*_

_Dedicated To_
   _*Jiddah Ja'o & Baby Afreen*_

              7⃣

_Ganin babu sarki se Allah yasa Goggo  ta koma gida cikin damuwa , babu abunda take yi se addua Allah ya dawo mata da Jiddah lapiya_.

   _Wani gidan k'asa suka shiga , karami ne kam amma tsab yake baka jin komai se kukan tsuntsaye dake saman bishiyar dabino dake tsakiyar gidan. Keken ya jingine jikin wani d'aki sannan ya ajiye fartanyan a gefe ya juya ya dubi Jiddah yace " Kinga nan ne gidan Inna ta , muje in kaiki wajenta ku gaisa " babu musu tabi bayan sa har cikin wani bukka dake chan gefe a cikin gidan , da alama wajen hutawan Inna ne_

    _Sallama yayi inna ta amsa cikin muryar manya sannan ya sa kai ciki itama haka tayi. Bayan sun gaisa da Inna ta dubeshi tace " Aliyu! Wannan kuma daga ina_?"

_Nan ya bata labarin had'uwar su da Jiddah . kai inna ta jinjina sannan tace " Yanzu yarinya wa yasan irin tashin hankalin da kika saka iyayen ki a ciki? Banda abunki ina ke ina rugar Ard'o keda ko sunan k'auyen ku baki kama ba_?"....... _*READ MORE*_


asykhaleel.Wordpress.com
_*ASY KHALEEL TA KOWA 👄*_

KURUCIYAR JIDDAHWhere stories live. Discover now