🌟。*。💗~ xXx
。💚。*。 。🌟
🌟 _*KURUCIYAR JIDDAH*_
.💜'*。.🌟¨¯'*❤。。🌟
*HASKE WRITERS ASSO...* 💡
_*Story And Written By*_
_*Asy khaleel......✍*__Dedicated To_
_*Jiddah Ja'o*_1⃣6⃣-2⃣0⃣
_Hadari ne ya hado kamar ba gobe bak'ik'irin Aliyu se faman sauri yake da keken nasa domin su samu gurin fakewa " Yaya Aliyu muyi sauri mana! Wannan ruwan dukan mu zai yi fa! Ni bana son ruwa_ !"
_Tsaki Aliyu yayi yace " Ke dallah bakya ganin k'ok'arin da nake yi ne ko ni ce miki nayi so nake ruwan ya doke ni_?
" _shiru tayi a take ta zama abun tausayi ko me dalili oho_?
_Haka suka dinga lulawa cikin daji amma kafin su samu mafaka ruwa ya sauk'o da k'arfin gaske , jagab yayi musu kamar kaji 🐓 suka fake gindin wata bishiya har ruwa ya d'auke , babu abunda Jidda take banda rawar d'ari , saida ruwa ya tsaya chak Aliyu ya mik'e_
" _Tashi mu tafi ke ruwan ya tsaya!" Cewar Aliyu yana k'ok'arin matse yar tsumman rigar sa , jin tayi shiru ya sake maimaita abunda ya fad'a " Baki jini bane wai? Ki tashi ruwan ya d'auke mu k'arasa gida Inna zata baki wasu kaya ko sanyi ya kama ki! " shiru dai bata motsa ba dan haka ya Tunkude kanta daga kifawan da tayi kan gwiwar ta aikuwa ta zube a k'asa kamar matacciya_ 😳
_Jiki na rawa cikin firgici Aliyu ya d'aga ta " Innalillahi! Jiddodo! Jiidda! " kan kafad'a ya ajiye ta gami da jan keken da hannu d'aya a haka har ya isa k'auyen su_......_Abokin shi Labaran ne ya hango shi , cikin sauri ya nufo inda suke ya taimaka masa da keken yayi cikin gida da ita , inna na ganin su ta baza tabarma fuskar ta d'auke da alamar tambaya , saida ya nutsu tukunna ya labarta mata komai a nan inna ta fahimci sanyi ne ke damun Jiddah kuma lallai wajen danshi ba mazaunin ta bane balle kuma har ruwa ya daketa nan Inna ta had'a y'an magungunan gargajiya ta jik'a aka bawa Jiddah kwanan ta uku sannan ta murmure_.........
*************
_Tun da abun nan ya faru Jiddah ta zama y'ar gatan yaya Aliyu , a tak'aice duk abunda yasan zai cutar da ita baya bari, duk shirmen ta biye mata yake yi , kuma duk inda tayo tsokana se ya shige mata ! Aliyu ya kasance kyakkyawan saurayi matashi duk cikin k'auyen Gololo , y'an matan nan kowa Aliyu musamman Jummai wanda babu abunda bazata iya a kanshi ba amma Bangaren Aliyu kuwa Yarinya ce y'ar shekaru sha d'aya a ranshi Jiddah ta Aliyu! Kamar yanda yake mata kirari duk da tarin wautar ta shi baya gani_....
_A yanzu rayuwa ta koma sabuwa gareta , ta fara mance gidansu kullum de zancen ta goggo amma ba wai don tana marmarin komawa ba. Chan k'auyen su kuwa, Su baban Rabe mai lambu sun samu sakat domin ko ba komai an daina tsinkar masa mangwaro_ 😂😂😂😂😂
_*To Jama'a KO kuma ince Readers*_
Yanzu de wasan tsakanin mutum uku ne JUMMAI ! ALIYU GA KUMA JIDDODO IKON ALLAH! 😂😂
Ku biyo Asy Khaleel danjin me xe wakana acikin dan takaitacchan labarin nan© _*ASYKHALEEL TA KOWA*_ 👌🏼
asykhaleel.Wordpress.com
DU LIEST GERADE
KURUCIYAR JIDDAH
KurzgeschichtenLabarine mai cike da barkwan chi, nishad'antarwa da sanyaya rai.