🌟。*。💗~ xXx
。💚。*。 。🌟
_*KURUCIYAR JIDDAH*_
.💜'*。.🌟¨¯'*❤。。🌟
*HASKE WRITERS ASSO...* 💡
_*story and written by*_
_*Asy khaleel.....✍*__Tawan kina Ina? Yau page din nakine ke kadai, ban hada ki da kowaba, Asy Tana gdy da so da kaunar da kike Nuna mata....Allah ya barmu tare *MY UMMI HAMBALI*_
3⃣1️⃣-3️⃣5️⃣
"Ni kam na gaji da zaman jiran gawon shanu! Yau komai rintsi zan tafi neman Jiddah ,bazan zauna ba yarinya ta tana chan tana fama da wahala" Goggo ke magana tana d'aure d'an k'ullin kayan ta , tana kammala wa ta kwashi slippers nata ta sa gani da yafa cinyayyen mayafin ta ta kwashi sauri kamar zata fire sama ba tare da tasan hanyar da ta nufa ba ,wani mai amalanke ne ya rage mata hanya zashi gona shi ma a bakin gonar ya sauk'e ta taci gaba da doka tafiya duk inda ta gaji ta huta se wurga idanuwa take wai tana neman jiddah baiwar Allah!.
*********************
Tuk'in keken yake ita kuwa se zuba take kamar mazari, tana Jan wata y'ar sanda a k'asa ,wani kare ta hango kwance a gefen hanya ga wasu mutane da mota me body ta sauk'e a gaban su wanda da alama sun ci kasuwa ne.Da gangan Jidda ta rafka wa Karen nan sanda ai kuwa kare yace da wa Allah ya had'a mu? Da gudu ya fafari su Jidda tun k'arfin shi Aliyu ke tuk'in keken har ya gaji ,a garin gudu ya suri wata y'ar tsohuwa d'auke da k'ullin kaya a gaban keken tana ihu k'afafu a sama Aliyu ya kasa rik'e keken kafin kace wani abu keke ta wuntsila su cikin ciyawa nan tsohuwar ta mik'e se masifa take ba tare da ta lura da wad'anda ke zube cikin ciyawar ba ta d'auki k'ullin kayan ta cigaba tana d'ingishi
Jiddah na mik'e wa ta sa dariya harda rik'e ciki ganin yadda tsohuwa ke d'ingisawa Aliyu ya biye mata shi ma har da zube wa k'asa."Wlhy kamar Goggo na har sa kayan su ma iri d'aya kuma mayafin ma haka" cikin dariya Jiddodo ta fad'a Aliyu da tuni ya mik'e yana kad'e y'ar keken shi ya ja tsuka
"Mtsew! Dallah!Goggon da kika ce da ke da ita Baku tab'a barin k'auyen ku ba ta Yaya zata zo nan?
Wani d'an Jinkiri Jidda tayi sannan ta ce "kuma fa gaskiyar ka ne ,kawai mu cigaba da tafiya"Nan suka haye keken Mutumiyar na zaune a kariya se kalle kalle take tana neman wani rigimar da zata takano"
_*ASY KHALEEL TA KOWA 👄*_
asykhaleel.Wordpress.com
ESTÁS LEYENDO
KURUCIYAR JIDDAH
Historia CortaLabarine mai cike da barkwan chi, nishad'antarwa da sanyaya rai.