🌟。*。💗~ xXx
。💚。*。 。🌟
🌟 _*KURUCIYAR JIDDAH*_
.💜'*。.🌟¨¯'*❤。。🌟
*HASKE WRITERS ASSO...* 💡
_*story and written by*_
_*Asy khaleel.....✍*__This Page Is Dedicated to_
_*Billybadaru, Seemaluv & UmmieJaafar Allah yakara so Btw Us*_3⃣
Tsuka goggo ta Saki tace " ni matsa min a jiki kuma ki fito da mangoron nan ki taho mu maida shi tun kafin baban ki ya dawo ! Yarinya se ci babu abunda kika sani kina biyewa su Dije gwara su iyayen su sun dafa 'kasa kefa? Idan kika takalo rigima babu mai tsaya miki ni da kika raina wa wayon ma na daina biye miki tunda abun naki haka ne?
Saboda Allah ki rasa wanda zaki tsokano mana se baban Rabiu mai tumbi? Wannan idan yazo daga ni har ke zai zaune mu wlhy "
" toh goggo kiyi shiru mana! Se magana kike yi bayan ga baban ma ya dawo ni ki kyale ni kawai in ci tuwo na don gobe zamu je rugar Ard'o Surajo "Goggo bata san lokacin da ta Saki salati ba , ke y'ar nan me kuma zaku yi a Chan? Oh ni Hamsatu naga ta kaina ! Yanzu me zai kai ku har rugar Ard'o ????" Jiddah ta bushe da dariya taci gaba da cin tuwon ta ko kallon inda goggo take bata yi ba hasalima tana gamawa ta shiga bayi business💩.............
Asubar fari Jiddah ta fito daga d'aki ta d'ebo ruwa a buta harda neman kujera wai alwala zatai kawai ta wanke fuska ta kurkure baki ta wanke hannu da k'afa ,inda tayi nan ta shimfid'e tabarmar tayi ta dungurawa , sannan ta yi sand'a zuwa d'akin goggo ta bud'e gwangwaro ta ciro wata atamfa matso kusa 😅 duk wannan gwaggo bata sani ba se minshari take ja har Jiddah ta gama kwalliyar ta bakin nan yasha ja ga uban bak'in kwalli ta d'iga ta ciro takalman ta shoke ta yi damara da gyalen ta sannan ta nufi hanyar k'ofa " Goggo in kinga dama kiyi awa hud'u kina bacci nidai yanzu rugar Ard'o zamu tafi " tana kai wannan ta fice tana tsalle tana wak'ar ta ta kullum...
Firgigit goggo ta mik'e tana salati " ke Jiddah! Jiddah!! Oh ni Hamsatu naga ta kaina yaya Zan yi da wannan yarinyar ? Yanzu fisabilillahi se ki Kama hanya har rugar Ard'o ? Wacce uwar zakiyi a Chan ? Ai zama bai Kama ni ba......... _*READ MORE*_
_*ASY KHALEEL TA KOWA👄*_
YOU ARE READING
KURUCIYAR JIDDAH
Short StoryLabarine mai cike da barkwan chi, nishad'antarwa da sanyaya rai.