*💘SHIN SO DAYA NE?💝*
*TARE DA ALKALAMIN*
📝
*HAFSAT AL-MUSTAPHA*https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-1194933670662901/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}*
'''THE PEN OF LOVE 😘 HEART TOUCHING ❤ TEARS OF SORROWS😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINGS 💑'''
*JUST GIVE US FOLLOW.....*✔
🌸BABI NA DAYA🌸
*Page 1-5*Kwance nake saman katafaren gadona,hirar soyayya nake tare da mutumin da ban taba gani ba haka zalika shima din bai taba ganina ba, wayace kawai ta hadamu, ya fada mini cewar lambar wani abokin aikinsa ya karba gun wani, toh ayayin kwafe lambar acikin wayarsa ne yayi kuskuren rubuta wani harafi wanda asanadiyyar hakan ne Kiran ta fado layina.
Tun daga lokacin muka kulla alakar soyayya wanda dakyar ya sami ya shawo kaina kafin na yadda na karbi tayin soyayyar tasa, tun bana wani sakewa dashi har nazo na ware na soma dan sabawa dashi wanda idan har banji muryarsa arana daya ba toh kuwa ina iya kwantawa rashin lafiya,Sannu ahankali naji ya soma kwanta mini arai,Cikin kankanin lokaci naji soyayyarsa takai mini mugun cafka acikin zuciyata, gani nake ayanzu bazan iya rayuwa babu shi ba sabida yadda nake jinsa kamar wani bangare na jikina, soyayyarsa ta gama gaurayewa da dukkan jinin dake ajikina, zan iya fassara irin soyayyar da nake masa da soyayyace wacce ruwa bazai iya kashe kishinta ba, irin natural love dinnan zallah,, wayyo Allah jama'a ya zanyi da rayuwata idan har na rasashi? The worst part is that bani da tabbacin mutum nema ko kuwa aljan?DR MUBARAK MUHAMMAD MUSTAPHA kenan.
Tsawon watanni biyar kenan muna fama da abu guda ta waya wato soyayya da Kuma chatting on WhatsApp amma koda wasa bamu taba haduwa face 2 face ba,duk da cewar garurruwar da muke basu da nesa da juna,infact zan iya cewa tamkar baki da hanci muke...I am a Zaria base ayayin da shi kuma mutumin Kano ne.
Bazan iya kirga adadin magiyarsa kan mu hadu ba amma niche na hana hakan faruwa har yau,dalilina kuwa shine,ina fargabar kada yazo ya ganni yaga ban masa ba duk da cewar ni nasan I am a first class bae,ba yabon kai ba amma gaskiyar magana I know dat am perfectly okay for any type of classic man.. Na riga na daukarwa kaina alkawarin cewar koyaya Mubarak yake muddin dai shi mutum ne, toh I don't care of how he looks,ina son abina hakan, ban san wani hukunci shi zai yanke ba idan ya ganni Thats the reason why am damn scared.
Yanzun ma haka sana'ar tasa daya saba yake yi wato ina nufin magiya,"Haba my Zahra ki tausaya ki ceci rai, ki bani damar nazo naga sarauniyar data dade tana mulki acikin babban birnin zuciyar bawan Allah Mubarak, wallahi zuciyata, gangar jikina dani karan kaina muna muradin muyi tozali da kyakkyawar fuskarki yake ma'abociyar hankali da nutsuwa wacce ita kadai ta iya sarrafa daddadar soyayyarta acikin zuciyar Mubarak dinta..Please babyna is my request been granted this time around? " ya karashe maganarsa cikin wani irin salo na soyayya wacce sai da naji duk wani kuzari na jikina ya gushe sakamakon yadda zumar soyayyarsa ta narkar da duk wani gudan jini dake gudana acikin jikina.
Da kyar na iya tattaro nutsuwata, na dan saki kasaitacciyar dariyata mai birge mutane tare da twisting din muryata, nace"
Hey! Man u are making me to feel lyk am on top of the whole world... Wow haka nake da babban matsayi acikin zuciyarka da kuma rayuwarka?... Anyway thanks for dat dearest one...zancen haduwar tamu kuwa, I will still repeat myself again, kadan kara hakuri har sai zuwa lokacin da nayi ra'ayi please. "Ji nayi ya tari numfashina cikin tsawa"Fadima ya isheni hakan!! enough of all Dix bullshits and playing around wit ma senses...Am not a kid da har zaki dunga raina min wayo kina downgrading level dina sabida kinga ina yawan rokonki kan mu hadu all because am madly in love with you... Ke kuwa koda rana daya ban taba jin kinyi koda subucewar baki ba kice mu hadu ba... Zahra meyasa kika zabi da ki cigaba da azabtar dani ta hanyar haramta mini ganinki?... kai infact Fadima am doubting if u really love me as you said because your action towards me is making me to be sensing dat maybe u ar juz pretending dat you love me, whereas u don't.......Ayau dinnan nake son ki fada mini gaskiya.. Wani irin matsayi nake dashi acikin zuciyarki?... Baby pls say something you are silent.. "
YOU ARE READING
SHIN SO DAYA NE? (Complete)
PoetryIt's all about heart touching love story,betrayal & hot love💗............ Karku sake abaku labari