💘SHIN SO DAYA NE?💝
TARE DA ALKALAMIN
📝
HAFSAT AL-MUSTAPHA_Watpadd:Hafnancy_
🌼BABI NA TALATIN DA UKU🌼
Page 152-157
Cikin Ikon Allah kuwa,washegari Mubeen ya tashi garas dashi,sosae yake jin qarfin jikinsa,sae de d'an ciwon kai daya sauran masa.Koda ya tashi,farkon abinda ya soma fad'o masa arai bayan yayi sallar Asubahi shine,kiran Zahransa,idan har kuma be sameta ba,toh ze latso Mahmood yaji yadda ta k'aya musu tsakaninsa da Fadimar idan har yama je gidansu din kenan kamar yadda ya alqawaranta masa.
Wani tunani ne ya fado masa arai na kila zega missed calls daga Zahransa ko kuma Mahmood,don ze iya cewa adaren jiya besan inda yake ba sabida zafin ciwo balle yaji k'arar wayarsa da ze nuna cewar k'iransa ake.Da sauri ya lalubo wayar,abin mamaki se kuma yaga wayar akashe bayan kuma ya tabbatar akwai chargy sosae aciki,hasalima full bar yake da.Atake anan yasan kawai wannan aikin Hanan ce.Kallonsa yakai gareta,baccinta take hankali kwance,tunda ta iddar da sallar subhi wani nannauyar bacci ya kwasheta sabida ta kwana tana ibada,tana meh rokarwa mijin nata a safe trip to India,shi kuwa mutumin naku bashi da masaniyar tashiwar daren nata.
Dan siririn tsaki ya saki hadi da dan murmusawa,tabbas yasan dalilinta na kashe wayar,tayi hakan ne don ya samu some rest,kada mutane su takurashi da kiraye-kiraye.
Ahankali ya furta"Hauwa'u Jiddanah kenan,ina mugun qaunarki fiye da yadda kike qaunata..... "
ita kuwa kamar taji abinda ya fada,don cikin baccinta ta mirgino zuwa gareshi tare da shigewa jikinsa tana meh kankamesa.Murmushi yayi abinsa tare da dada kankameta shima,kana,ya maida hankalinsa ga wayarsa tare da kunnata.Tana gama booting babu wani b'ata lokaci ya latso layin Fadimar. As usual 'Switched off' akace masa.Ji yayi kamar ya kurma uban ihu sabida yadda yake jin zuciyarsa na tafarfasa kamar d'anyar ganda.
'He really nid to speak to his Zahra,Infact!! he really nid to see her one on one before he go.' abinda ya aiyana aransa kenan.
Yaso latso Mahmood amma se kuma yaga rashin dacewar hakan,Maybe yana sharar baccinsa ahalin yanzu kuma baze so atakurashi ba.Haka ya haqura tare da tausasa zuciyarsa data haqura har gari ya dan kara wayewa sannan ya kira dan'uwan nasa.
Be yadda ko kadan bacci ya sake d'aukarsa ba,don so yake shidda ta buga sannan ya tashi ya shirya Jasmin don zuwa makaranta,sam baya son Hanan ta motsa da nufin tashiwa ta shirya Jasmin din da kanta,so yake kawai ya ganta kwance tana hutawa,don hakan ba k'aramin dadi yake masa ba ya ganta kwance bata aikin komai musamman yanzu da take dauke da babynsa kuma yake bata wahala.Jasmin da tunda ta dawo daga hutun weekend ta tarar da Goggo Ladidi,se ta kauracewa iyayenta,ta koma ga goggon,ta zama 'Jasmin din goggo',dalili kuwa shine Goggo Ladidi akwai shegen surutu,sae ya zamana tana biyewa Jasmin din suyi tayi,Jasmin din kuwa abin nema ya samu,ta samu yar'uwarta meh surutu shine ta mak'ale mata,don bacci mah tare suke yinsa ah masaukin da aka sauke Goggo,haka mah abinci tare suke ci,infact hatta wanka mah wani sa'in Jasmin nokewa take ta hana kowa yi mata wai sae de Goggon ce zata mata.
Hayaniyarsu ce ya jiyo ah kicin wanda hakan ya bashi tabbacin lallai sun tashi kenan,watakil Goggon kiciniyar dafa mata abinda zata kai makaranta take kamar yadda tayi jiya.Ahankali ya zare jikinsa daga na Hanan,cikin sanda ya fice daga dakin gudun kada ya tasheta.
Yana dab da karaso kicin din yaji Jasmin na yiwa Goggo surutunta,cewa take"Goggo kin san Daddyna ze tafi India yau ko? "
Goggo tace"Eh! na sani 'yar lelena... "
Ta cigaba"Yace idan ya tashi dawowa ze taho min da actorn nan meh suburbuda 'Ram charam.... "
Dariya sosae Goggo ta shiga k'yak'yatawa,Jasmin akwai ta da ban dariya.
YOU ARE READING
SHIN SO DAYA NE? (Complete)
PoetryIt's all about heart touching love story,betrayal & hot love💗............ Karku sake abaku labari