💘SHIN SO DAYA NE?💝
TARE DA ALKALAMIN
📝
HAFSAT AL-MUSTAPHA_Watpadd:Hafnancy_
_please manage diz chapter wlh am busy diz days_
🌼BABI NA TALATIN🌼
Page 140-145"Agaskia 'yar Kareematu wannan Mubarak din ya kwanta min arai,na yaba da hankalinsa ba kadan ba,fatarmu dai Allah yasa yadda azahiri yake da halin kirkin nan yasa haka ma zuciyarsa mai k'yau ce...... "Cike da farin ciki nace"Amin Ummu Fadima,agaskia naji dadi sosai da kika yi na'am da Mubarak..... yanzu sauran mana Abba.... "Tace"Ga shawara idan zaki Karba.... Abbanku na dawowa ki tunkareshi da batun Mubarak din tun kafin lokaci ya k'ure miki...... "
Da sauri nace"No Umma am very scared....ban san ko taya Abba zai karbi zancen ba sabida yadda naga yake sona sosai tare da Haidar.... Ummu Fadima pls ki tayani yi masa magana yadda zai fahimta..... " girgiza kanta naga tayi tace"Not again babyna,har sai yaushe zan daina shige muku gaba ina tayaku fighting kan abubuwan daya shafi rayuwarku?har sai yaushe ne zan soma nannade hannuwa na zuba muku ido kuma na kyaleku ku kwaci 'yancin kanku? Ko baki san su kansu 'ya'ya suma suna da hakki akan iyayensu ba?" Ahankali nace"Eh! Suna dashi Umma
Ta cigaba"Good.... Toh ina son ki san cewar yadda mahaifinki keda hakki akanki haka zalika kema kina da hakki akansa.... yana daga cikin hakkin uba ya zabawa 'ya'yansa abokan rayuwa na gari,ku ya'yan zamanin nan ma ku godewa Allah yadda ake kyaleku kuke tsula tsiyarku son ranku,azamaninmu wallahi uba yake zabawa dansa ko 'yarsa abokin rayuwa don idan baki manta ba ni da mahaifinki ma auren hadi aka mana,amma azamanin nan sai kiga iyaye sun baiwa 'ya'yansu damar kawo duk wanda suke so sai ah aura musu zabinsu...... My daughter wat am trying to figure out to u is dat,karki sake kiyi wasa da wannan damar da mahaifinki ya baki na ki kawo zabinki,Mubarak kika ce kikeso kuma nima nayi na'am dashi,don haka Abbanki na dawowa ki tareshi da batunsa,ina son ki cire duk wani tsoro aranki,mahaifinki ne wanda ya tsugunna ya haifeki ba wani dodo ba,u don't hav to fear ur father at all... Ni kaina nasan yadda suka shaku da Alhaji Ahmad mahaifin Haidar,kuma nasan bazai so yaki baiwa dansa aurenki ba... Amma abinda nakeso ki gane shine,mahaifinki mai saukin kaine da kuma fahimta don haka nasan bazai miki dole ba,insha Allahu zaiyi na'am da zabinki idan har yayi bincike ya tabbatar da Lallai Mubarak nada halayen kirki.... Is dat taken 'yar Kareema?"Cike da jin wani gwarin gwiwa nace"Insha Allah Umma na fahimceki kuma zan tuntubeshi da maganar Mubarak din da zarar ya dawo.... "
"'Yata kar kiyi tunanin kamar bana son tunkarensa da maganar ne da kaina,a'ah,bana son ne yaga kamar ni nake daure muku gindin yin abubuwa,for instance,zuwanku kano kwanakin baya ai nice na shigar da maganar wajensa tare da nemar muku izini,ko alokacin ma sai da yayi dan korafi akan meyasa bana kyaleku kuna tambayar abu agunsa sai dai kuta aikoni kamar wata 'yar aiki? Toh kinga abinda ya sanya nake son ke da kanki ki tunkareshi da maganar kenan,kuma ki hanzarta kada yazo ya bullo mana ta bayan gida..... "
"Umma wai meh kike nufi ne da bayan gidan nan da kullum kike fada? "Cike da rashin fahimta nayi mata wannan tambayar.
Murmushi tayi kafin tace"Ina nufin kada ya aurar dake ga wani can wanda ba zab'inki ba.... "Da sauri na dafe kirji nace"A'zubillahi!!! Insha Allah hakan ma bazata faru ba,babu wanda zai min auran dole sai wanda nakeso ko ummata? "
"Ni wacece da zanki idan har wanda ya fini iko dake ya zartar da hukuncin hakan? "
"No Ummu Fadima kar ku min hakan don Allah" na fadi hakan ina girgiza kaina kamar wacce aka fada mata cewar ai tuni ya riga da ya zartar da hukuncin hakan.
BINABASA MO ANG
SHIN SO DAYA NE? (Complete)
PoetryIt's all about heart touching love story,betrayal & hot love💗............ Karku sake abaku labari