*💘SHIN SO DAYA NE?💝*
*MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA*
*WATTPAD:HAFNANCY💞*
*IG:Hafsy___mustee*
🌠🌠
*KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE*
🌼BABI NA HUDU🌼
*Page 9-12*
Har Baba ya kare jawabinsa da nasiharsa agaremu kan zaman aure da haquri da juna,ban tsinci komai ba don gaba daya hankalina ya tafi ne ga tsananin mamakin yadda akai Engr. Mahmood ya aureni,da kuma sunan k'aryar da yayi amfani da ita wajen aurena wato *'MAHMOOD NAKOWA'*.
Taya mah xan soma tunanin xaman aure da wan saurayina? Taya kuma xan soma tunanin had'a idanuwa da Mubarak axuwan k'anin mijina?shi kuma ya dunga min kallon matar wansa?Sannan wani irin tashin hankali ne xa'ayi idan har Mubarak yasan cewar wansa ya aureni? Nasan tabbas zeyi tunanin cin amanarsa nayi bayan ko kadan bani da masaniya akan faruwar hakan.Wallahi wallahi da'ace nasan cewar Engr. ne wanda mahaifina keta burin aura min da wallahi baxan tab'a bari ayi wannan auran ba,na gwammace koma meh ze faru ya faru amma baxan taba cin amanar Mubarak ba.
Se de kuma hausawa sunce *'RASHIN SANI YAFI DARE DUHU'*.... Aikin gama ya riga da ya gama,baxan iya maida hannun agogo baya ba,amma nasan ta yadda xanyi na raba auran nan bayan na gama jin dalilinsa na aurena.........
Allah-Allah kawai nake wannan munafikin tsohon kilakin ya gama xancen soki burutsunshi sannan mu saka kafa mubar gidan don na samu na aiwatar da kudirin dake cina arai.
"Fadima tunanin meh kike?tashi ku je dare nayi Allah yayi muku albarqa.... "
Maganar Baba ne ya dawo dani daga duniyar tunanin dana Lula.Da hanxari na mik'e donna k'osa mu bar gidan.Su Mami ne suka mana rak'iya.Hafeezah ce rungumeni dani har muka isa waje inda yayi parking motarsa.
"Fadima Allah ya tsare,sae munzo ganin dakin amarya.... " Mami ce ta fadi hakan sanda na daidaita xamana ah kujerar meh xaman banza.Hakan ya bani tabbacin Lallai Zariar zamu tafi da daddaran nan.
(Ni kuwa nace sorry Fadima xakuyi 3weeks agidanki na nan Kanon dake 'court road').
Axuciyata nace"kafin kuzo ganin gida Fadima ta ware don baxan tab'a iya xaman aure da wan saurayina ba..... "
Har muka bar unguwar muka haye saman titi babu maganar data shiga tsakanina dashi.Xuciyata se tafarfasa take tare da min wani mugun zogi.
Shi kuwa Engr. Sam ya kasa sakewa da wannan shirun da Fadimar ta masa,yasan tabbas shirun nata bata banxa bace,dole akwai abinda take shiryawa aranta.Sae daya tsaya kan hanya ya siya musu gasasshiyar kaza,pizza da kuma youghourt masu sanyi na roba.
Sun kusa da 'court road' yaga shi de ya kasa haquri da wannan shirun nata,yana son ko 'yar zagi ce ta masa ko ze dan sami sassaucin abinda ke damunsa aransa.
Ahankali yace"Fadima pls speak for Allah's sake,kiyi magana don tabbas na b'ata miki,ki zageni,ki mareni idan hakan ze saka ki huce kan abinda aka miki..... Zahra'u cry out loud idan har hakan ze saka ki samu sassauci na abinda kike ji agame da cin amanar da nayi muku....... "

VOCÊ ESTÁ LENDO
SHIN SO DAYA NE? (Complete)
PoesiaIt's all about heart touching love story,betrayal & hot love💗............ Karku sake abaku labari