PART 2:CHAPTER TWO

1.6K 141 2
                                    

*💘SHIN SO DAYA NE? 💝*
  
*MALLAKAR:HAFSAT AL-MUSTAPHA*

       *WATPADD:HAFNANCY💞*

   *KASHI NA BIYU:RIKICIN KARSHE*

          🌼BABI NA BIYU🌼

     *💧💧💧KAI  AMARE💧💧💧*
          💧💧                               💧💧
              💧                                     💧

    *page 3-6*

       Har muka isa kanon ban mah san mun iso ba sabida tun shigata motar,cigaba nayi da sana'ar kukana,Ash kuwa sae aikin rarrashina take don ni da ita kawai muke xaune agidan baya,ita kuwa Zuwairah gidan gaba ta xauna wacce jefi-jefi suke d'an taba hira da meh tuki wanda na lura kamar yana cikin abokan ango.Shi din mah yayi rarrashin duniyar nan amma naki nayi shiru,can yace arabu dani kila so nake shi angon nawa yazo ya rarrashi abarsa da kansa,abin ya baiwa su Ash dariya,ni kuwa haushi maganar tasa taban kamar na tashi na kifa masa lafiyayyun mari.

   Mubarak ne ya fad'o min arai,yanzu shikenan mun rabu kenan? Yanzu baza'a taba k'irana da matar mubeen ba kamar yadda nake ta burin hakan sae matar Mahmood Nakowa?abin mamaki mah wai dangin mijin nawa ah kanon suke,kada watarana fa mu had'e dashi.... Wani b'angaren xuciyata kuma yace"xancen banza keda mah ah Zaria zaki zauna? Sannan meye naki na wani damuwa akan mutumin da baya qaunarki,mutumin da kuma sam be damu da rayuwarki ba?

      "Toh! amaryar Nakowa mun iso,sae ki had'iye kukan naki ya isa hakanan kinga gidan surukai xamu shiga kada suga kina koke-koke su aza ko surukar tasu ba jaruma bace...... "

Ash ce ta katse min gajeriyar tunanina alokacin data bud'e min kofa da k'yau wai na fito,sae asannan na ankara da cewar har mun iso ban sani ba.

    Sannu ahankali na sako kafafuwana waje tare da dire su akasa,wani daddad'ar ni'imtaccen iskar yammacin nan ne ya soma min barka da xuwa.fitowar tawa tayi daidai da wayar da wannan meh tukin keyi wanda ayanzu nasan sunansa don naji Zuwairah ta ambaci sunan wai *'KHALEED'*.

     Cewa yayi"Kai dan iskan ango kana ina? gashi fah mun iso amma anki bamu amaryar..... "

Saurarawa naji yayi,can yace"Na taba maka irin wannan wasar ne? Ka yadda dani anki bamu ita wai sae kaje da kanka.... "

Ya sake saurarawa,can ya d'an d'ara yace"Kai wasa nake maka mallam karka min hauka,ga amaryarka nan mun kawo maka ita,tasha kuka kuma har yanxu tana kan yi ne sae kazo ka lallashi abarka........ "

    "Ayyyirihiiiiiiii,lale marhaba da zuwan amarya.... " rangad'e rangad'en gudar dangin mijina ne ya hana min jin k'arshen maganar Khaleed da mijina.Ni kuwa jin sun nufoni ya saka na k'ara jan mayafina gaba don kada suga fuskata.

        Wata 'yar matashiyar budurwace naga ta rungumeni tana fadin"Oyoyo!amaryarmu sannu da xuwa...... "

Mama Jamila ce ta rad'a min magana akunne,cewa tayi"Ki shiga da kafar damarki tare da bismillah,haka kuma xakiyi idan aka maidaki can gidanki.... "

    Daga mata kai nayi alamar naji jawabin nata,daga haka naji wasu mata su wurin uku suma sun rungumeni kamar zasu kada ni akasa suna min sannu da xuwa har muka shige gidan.

Wani daki aka saukemu aciki wanda muka ji wani daddad'ar kamshin turaren wuta ya mana maraba da xuwa,gaskia ba laifi suma kanawa akwai son kamshi.Maganar gaskia ba k'aramin karramamu akai ba,nima sae naji na d'an saki jikina amma har xuwa wannan lokacin ban yaye mayafin kaina ba,ina nan lullub'e aciki kamar wata munafuka,lokaci xuwa lokaci nake dago kai na d'an saci kallon mutane.

    Cikin k'ank'anin lokaci muka ga an cika mana gaba da kayan ciye-ciye da shaye-shaye.Mama Sadiya ne suka dan taba amma babu yadda basuyi dani ba amma naki ci.Ce musu nayi ak'oshe nake.Ak'arshe dai ruwa kawai na d'an sha.

SHIN SO DAYA NE? (Complete) Where stories live. Discover now