CHAPTER FOURTEEN

1.9K 149 1
                                    

💘SHIN SO DAYA NE?💝

               TARE DA ALKALAMIN
                       📝
             HAFSAT AL-MUSTAPHA

_Watpadd:Hafnancy_

🌼BABI NA GOMA SHA HUDU🌼
        Page 65-70
Na dawo daga rakiyarsu Ash na tarar Suhaima da Lubna na gyara wajen da muka yi breakfast.

Ko sake kallon ita Suhaimar banyi bah,nace wa Lubna"Lubna ina Umma?"

Tace"Ta tafi bangaren Abba... "

Jin hakan ya sanya na nufi d'akina ba tare da na sake cewa komai bah.Ina shiga daki, wanka na soma yi don naji dan dad'in jikina.Doguwar riga mara nauyi na sanya sannan na dauko wayata na kunna.

Wayar tana gama booting, sai text messages suka hau shigowa kamar dama can jira suke abude wayar.

Text d'in Ash na soma budewa wanda nake tsammanin tun jiya ah Kano tayi min(idan zaku tuna sanda zata dauki Mubeen hoto tayi ignoring wasu messages.... Remembered?)

The message goes lyk dix, "Fadima idan kina yiwa Allah ki taho ki kwashe shanyar da kika yi.... Kayan sun gaji da bushewa...kina can kina soyewarki da Man d'inki ayayin da mu kuma kika barmu ana cin mutuncinmu anan.... "

Murmushin takaici nayi sanda na tuna da Mummyn Mubeen wanda itace Ash ke nufin taci mutuncinsu.Har yau mamaki nake da suka ce min matan nan tayi musu rashin mutunci akaina, sabida sam koh kusa ba tayi kama da wacce zata iya yin hakan bah.Ko da yake such is life... Diz life is full of wonders... Dan'adam tattare yake da abubuwan mamaki kala-kala.

Sauran text messages d'in kuma wanda ake aiko wa mutum ne idan kayi missing voice call.I missed about 20 voice calls daga Ummana wanda hakan na nufin tayi ta trying numbata kenan koh Allah zai bata sa'a ya shiga, she never gave up.... Uwa -Uwa kenan... Believe me if I say, No one like mother.

Sauran calls d'in dana yi missing kuma, daga Leedar ne da Ash, sai kuma Mubeen.

Mubeen kenan sai ayanzu ya fad'o min arai. Nasan yana ta trying line d'ina bai sameni bah, kuma maybe yana cikin wani hali ayanzu I guessed, idan har da gaske yana sona kenan as he said, sabida ni yanzu na daina yadda da love stories na d'a Namiji..'DR. MUBARAK' ya mugun koya min hankali.

Ji nayi kamar na kirashi, sai kuma na fasa because its not my class ni na fara nemansa,shi din mah ya kamata ya k'ira yaji ya muka kawo gida.Don haka zan k'yaleshi duk sanda yayi trying line d'in yaji ta shiga toh Alhamdulillah, amma idan bai k'ira bah toh Wallahi ni d'in mah bazan sake kiransa bah.

'ENGR. MAHMOOD' ne ya fad'o min arai.Murmushi nayi ina tuna sanyin halinsa.Namiji ne kamilalle,maganarsa ahankali cikin sanyin voice.Abinda yafi bani dariya agame dashi bai wuce yadda idan na masa tambaya.. Instead ya maido min da amsar tambayata, No sai dai shima ya jefo min tasa tambayar.

Abin dariya ya bani wanda har nake ta k'yak'yatawa, kofar d'akina naji an bude aka shigo.

It's Umma, ganinta bai hana ni daina dariyata bah,dariya fah hadda hawaye.

Ina kallon Umma wacce sai kallona take cike da sha'awa tace"Masha Allah! 'Yar Kareematu burina bai wuce na ganku cikin farin ciki bah akoda yaushe.... Na san koh baki fito fili kin fad'a bah.. tabbas daga ganin wannan hawayen murnar, its an indication dat surukin nawan ya mugun kwanta miki arai. "

SHIN SO DAYA NE? (Complete) Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz