PART 2:CHAPTER ONE

1.6K 130 9
                                    

  💘SHIN SO DAYA NE?💝

*MALLAKAR:HAFSAT AL-MUSTAPHA*
           
          *WATPADD:HAFNANCY*

*Gaisuwar ban girma gareku my wadpaddians & Hafnan's novella group,thanks for showing me true love,I also love you all so very much... 💗💗💗💕*

       
*KASHI NA BIYU:RIKICIN KARSHE*

         🌼BABI NA DAYA🌼
  
    Page 1-3

Ban kai ga isa kofar fita ba,sae kawai naji kaina ya harba,atake naji kamar ana buga min ganga akan,dakatawa nayi tare da rik'e kan da hannaye bibbiyu.

     "Muido lafiyarki kuwa? " haka naji Anty Hajaar ta fada.Ni kuwa ko tankata banyi ba sabida wani irin jiri da naji yana nemar kwasheni ya kifar akasa.

Gani nayi tsayuwar na nemar gagarata don haka sena koma da baya na zauna da k'arfi agefen gado.

    "Amaryar Nakowa lafiya kike kuwa?" Hakan naji k'awayena sun fad'a tare da tasowa suka zagayeni,wasu ta saman gado ayayin da wasu kuma ke tsaye agabana suna meh jiran nayi musu bayanin abinda ke damuna.

    Ash ce ta shigo dakin tana fadin"Oya Fateenah,'yan mata duk ku taso aje ayi ho....... "

Ganin da tayi an zagayeni,sae sannu ake min ya saka ta cillar da mayafinta tare da rugowa da gudu,ture wasu friends dinmu tayi wanda hakan ya bata damar samun kusanci dani.

   "Fateenah wats wrong? Lafiya naga kin dafe kai da hannuwa bibbiyu?"

Ash kuwa tsoro ne ya cika xuciyarta fal. Azuciyarta tace"Oh! Yah Allah kar dai ace Fadima ta samu labarin wanda aka daura mata aure dashi shiyasa ta shiga cikin wannan halin?"

    Ita Ash tana waje sanda su angwaye suka shigo,sae taci karo da Mahmood wanda kuma aka nuna mata cewar ai shine angon Fadimar.Atake anan taji cikinta ya duri ruwa,ji tayi tana matuqar buqatar toilet awannan lokacin don yadda taji kamar tana shirin sakin gudawa ajikinta.Ai kuwa da azama tayi toilet din.

Koda ta fito,sake komawa tayi,alokacin suka ci k'aro da Suhaima wacce itama kiranta akai da ta fito suyi hotuna da angwaye,itama tana ganinsa wai amatsayin angon yar'uwartata,murza idanuwanta tayi da kyau don ta kara tabbatarwa da lallai ko shi dinne.

     Ai kuwa shi dinne dai ba wai kamanni ba,da azama ta koma ciki don labartawa yayartata shine suka ci karo da Ash din.

Ash tace"Ke kuwa kanwa meya faru ne naga kina rafka wannan uban saurin har bakya kallon gabanki kike tafiya?"

    Arud'e tace"Hmmm! Anty Ash kin san wa kuwa nagani amatsayin angon Yaya Fadima? Wallahi wannan wan saurayinta Mubarak dinnan na Kano ne.... Kin tunashi ai? Wannan Engr.Mahmood ne yake da suna ko....?"

Ash tace"Wallahi nima na ganshi,ganinsa ya saka nayi toilet don wata gudawa naji ta taho min alokaci guda don fargaba..... "

    "Amma taya hakan ta faru? Dama yana sonta ne? Kuma taya akai har ya samu ya shawo kan mahaifiyarsa ya aureta bayan tun ganin farko da tayi mana bata qaunarmu musamman ita yaya Fadimar?mafi daurewar kan wannan al'amari ina shi Mubarak din yake ne da duk hakan ta faru??"

Suhaima ce take fadin wannna maganar ahankali cike da kuma tashin hankali.Ita kuwa Ash cewa tayi"Wannan tambayoyin duk abakin shi uban gayyar zamu samu amsoshinmu..... Kuma.... "

   "Wae Suhaima kuskus din meh kukeyi ne tsaye anan baza kizo ayi hotunar ba kun shanye mutane can tsaye arana suna jira? "

Anty Hajaar ce ta katse musu hirarsu alokacin da take kokarin xuwa ta kira Fadimar itama ta fito ayi da ita.

SHIN SO DAYA NE? (Complete) Where stories live. Discover now