💘SHIN SO DAYA NE?💝
TARE DA ALKALAMIN
📝
HAFSAT AL-MUSTAPHANa sad'aukar da wannan page d'in ga shahararriyar marubuciyarmu 'Khadeejerh Abdullahi Dukamaje' AKA DeejahAbdul...I wish u a very happy married life!!
🌼BABI NA ASHIRIN DA BIYAR🌼
Page 120-125
Leedar na shiga part d'insa wanka ya soma yi don ya d'an ji dad'in jikinsa,sannan ya sanya k'iran Reedah,bugu d'aya,biyu ta d'aga tare da marairaice murya tamk'ar zata saki kuka.Ashagwab'ance tace"Haba big brother d'ina ina ka shige ne tun safe ina ta nemanka...yafi sau goma ina zuwa part d'inka don dubawa koh ka dawo.... "
"Toh noise maker kada acikani da surutu mana.... Yanzun nan na dawo daga school,auta am so much hungry,yi maza ki kawo min kome kuka girka please.... And extend my greetings to sweet mother,kice mata idan na huta zan shigo mu gaisa... "
Yana gama fad'in hakan ya yanke call d'in tare da cillar da wayar saman cushion yana mai dad'a gyara kwanciyarsa kan wani kujerar da yake kwance akai.
'Sweet mother' kamar yadda suke k'iran mahaifiyarsu,itace hakimce saman kujera tana tsefewa Reedah kai.Sun gama tsifar kenan Leedar ya k'irata.Tana gama wayar,Sweet mother tace"Son ya dawo ne? "
Da sauri tace"Yes sweet mother wai dawowarsa kenan... Kuma yace yunwa yakeji sosai wai nayi sauri na kawo masa abinci.... " Ta fad'i hakan ah sa'ilin da take kokarin mik'ewa.
Maida ita kan kujerar da take zaune Sweet mother tayi,tace"Toh ai k'ya bari na tufke miki sumar kafin kije amsa k'iran sarki.... "
Dariya abin ya baiwa Reedah don most of the times sunan da Sweet mother ke k'iran Leedar da ita kenan.Cewa take ya iya mulki kamar wani sarki.
Tace"Mother hurry up kin san sweet brother baya cika son ata keeping nasa waiting...."
Ganin uwar nata na slow wajen tufke mata gashin ya sanya tayi dabara ta k'waci kanta tare da k'arasa tufkewar da kanta.Kitchen ta nufa don d'aukar abincin sweet brother d'in nata ta kai masa.
Sweet mother dariya ta saki na ganin abinda 'yar autar tata tayi,tace"'yar banza ai gobe mah rana ce k'ya kuma kawo min wannan tsamin kan naki kice na tsefe miki ita.... Yanga nima zan miki... "
Dariya kawai Reedah ke tayi don tana jiyo duk Maganganun mahaifiyar tata daga kitchen,don awata k'aramar falo suka zauna.Azuciyar Sweet mother kuwa farin ciki ne fal acikinta ganin yadda 'ya'yan nata ke tsananin k'aunar junansu,addu'arta akullum itace, Allah ya k'ara musu d'ankon k'aunar junansu tare da haskaka rayuwarsu.
'French rice' shine Reedah ta kai masa wanda ita da kanta ta girka ta ijje masa,sanin da tayi cewar yayan nata na masifar k'aunarsa.Sallama take ta k'wadawa amma babu amsa,har ta iso dab dashi bai sani ba sabida duniyar tunanin daya lula ciki.
Ijje kular abincin tayi saman wani centre table sannan ta matsa kusa dashi tare da d'an tabosa.Afirgice ya d'ago kai ya kalleta.Sauke ajiyar zuciya yayi ganin itace ba aljaninsu ba kamar yadda yayi tunani afarko.
Ahankali yace"oh! Last born u really scared me wallahi.... "
Da mamaki tace"Wai sweet bro meke damunka ne da har ya sanya kayi nisa cikin tunani? Hammana please wat's wrong?..... Fine,nasan bazai wuce akan Suhaima ba,brother kawai ka fita aharkarta tunda taki ta baka chance kayi mata proving cewar zargin da take maka is not true.... Brother I think kawai juz turn the game u are playing with her sis to become the real one,ma'ana kawai kayi proposing mah Fadima................ "
KAMU SEDANG MEMBACA
SHIN SO DAYA NE? (Complete)
PuisiIt's all about heart touching love story,betrayal & hot love💗............ Karku sake abaku labari