💘SHIN SO DAYA NE?💝
TARE DA ALKALAMIN
📝
HAFSAT AL-MUSTAPHA
_Watpadd:Hafnancy_🌼BABI NA GOMA🌼
Page 45-50
Kallon juna muke cike da shauk'in so da kauna, ayayin da kowannenmu da abinda yake ji azuciyarsa agame da d'an'uwansa.Adaidai lokacin kuma ruwan da ake ta tsulawa ya d'auke wanda bazan iya fadin awanni nawa aka dauka ana yinsa bah, buh all wat I know is dat nasan dai mun dad'e Zaune acikin wannan 'joint' din.Samin kaina nayi da katse mana wannan sweet moment d'in ta hanyar fadin"Mubeen pls tashi mu tafi ruwan ya tsaya because I don't see the reason why I will keep wasting my time here bayan nasan cewar bah aurena zaka yi bah..... " Na fadi hakan in a romantic voice d'ina.
Da sauri ya tari numfashina"Says who?.... wallahi Zahra u ar the woman of my dreams...wlhy da'ace ni dake mun soma soyayya kafin Mummy ta kawo shawarar hadani da Hanan toh wallahi da ke kadai kawai zan aura.... Amma Allah shi kadai yasan daidai daya sanya hakan ta faru...dama can an riga da an rubuta cewar Hanan must be my first wife kafin ke becuz Zahra aurenki nake so nayi, sai dai idan kece kika gujeni... Amma fah ki sani cewar muddin kika gujenin, toh tabbas rayuwata tazo karshe..... "
Girgiza kai na soma yi ayayin da hawaye ke gangarowa saman cheeks d'ina, nace"No Mubeen dina pls don't say dat.....Ka tuna Hanan da Jasmine bah zasu so su rasaka bah, kuma kai mah bah zaka so ka gansu acikin kuncin rayuwa ba..... Haka zalika nima bazan so na rasaka ba.... Buh the fact is dat bazan iya aurenka bah Mubarak..... "
Cike da tashin hankali yace"Fadima idan har baki aureni bah wallahi toh duk wani masoyi na zai iya rasani...... " Ya fadi hakan cikin rawar murya, alokaci daya kuma naga yakai hannu ya dau wayarsa dake saman table din dake gabanmu.
Dialing wata number naga yayi tare da kange wayar akunnensa, alokaci daya kuma naji ya sanya wayar aloudspeaker ah sa'ilin da numbar wanda ya kira ya soma ringing alamar yayi nasarar samin wanda zai kira d'in.
"Hello hubbina" hakan naji an fada ah sa'ilin da wanda aka kira yayi picking wanda jin muryar da kuma sunan da aka ambato agareshi ya sanya nasan HANAN ce ya kira.
"Naam Hanan.... ga antynki nan tace wai ita bah zata aureni bah sabida ina dake....... "
Da sauri na fisge Wayar na kange akunne, cike da tsiwa na soma magana"Sannu munafaka, duk naji irin taku kalar basajar da kuka shirya akaina....lemme even ask you.... Ke wacce irin macece da har take goyan mah mijinta baya daya k'aunaci wata bayan ita har take burin ita wannan din ta zamo kishiyarta?.... Are u sure u are alright kuwa becuz ni dai banga macen da zata taya mijinta irin wannan aika aikar da yayi bah wanda akarshe ke din zai cuta sabida idan ya aureni ba lalle ne ya kwatanta adalci atsakaninmu bah sabida yadda yake nuna miki tun yanzu ya fi sona akanki... Yanzu so nake ki auna maganganuna ah mizanin hankali ki fada min ya kike ganin labarin zai sauya bayan ya aureni...?
Cikin shesshek'ar kuka tace"Anty nasan bayan ya aureki zan zama abar tausayi sabida yadda zai dunga fifita sonki afilli akan nawa... Nasan zan shiga cikin wani mayuwacin hali fiye da wanda nake ciki ayanzu amma farin cikin mijina ya fiye min komai....banyi tsammanin zaki yi blaming d'ina bah don na baiwa mijina goyon bayan ya auro wata bayan ni.....Ni dai don Allah ki auri mijina don dake yake kwana azuciya kuma dake yake tashi da.... Mijina yana masifar sonki.... Mubarak d'ina is dieing for u, so pls Sister Zahra ki rayu da Abu Jasmine dina idan har kina kaunar ki cigaba da ganin farin cikinmu........"
Yanke call d'in nayi tare da rushewa da kuka, kukan da zan iya cewa na tausayinta ne don ni dai ban taba ganin mace mai son mijinta irin Hanan bah. Yes I can call dix a true love, because true love shine kaso abinda duk partner dinka keso,Ka bashi duk wani farin cikin da kake ganin he deserved,koda kuwa ka kasance kai kana cutuwa ayayin faranta masan..... Dats true love kamar yadda Hanan kewa Mubarak wanda bana jin ni zan iya yin abinda ita tayi.tabdi!! Na ijje kishinmu na mata ah ina?
![](https://img.wattpad.com/cover/147915298-288-k880284.jpg)
YOU ARE READING
SHIN SO DAYA NE? (Complete)
PoetryIt's all about heart touching love story,betrayal & hot love💗............ Karku sake abaku labari