💘SHIN SO DAYA NE? 💝
TARE DA ALKALAMIN
📝
HAFSAT AL-MUSTAPHA_Watpadd:Hafnancy_
🌼BABI NA BAKWAI🌼
Page 30-35Ido cikin ido muke kallon juna ayayin da kowannenmu ke raya wasu al'amura acikin zuciyarsa agame da juna.Kyawun Dr. Mubarak ya wuce yadda nake ta tsammanin gani. Namiji ne tsayayye mai cikar zati da kamala...kwarjininsa mah har wani kashe min idanuwa yake wanda hakan ya sanya nayi saurin kawar da idanuwana daga kallonsa.
Na koma kallon Jasmine wacce tana jin muryarsa ta ruga da gudunta wurinsa tana fadin"Daddy oyoyo wato dazu shine ka tafi ka banni ina ta nemanka ko? "
Lakatar karamin hancinta naga yayi yace"Am sorry babyna nayi laifi ayafewa Daddy... "
Tace"Toh Daddy na yafe maka amma wacece waccan antin mai kyau sosai...? "
Tayi masa wanna tambayar tana nuno ni da 'yar yatsarta ayayin da ni kuma na kasa kunnuwa naji ko mai zai fad'a mata.
"Kawar mominki ce... " hakan naji ya fada tare da nuna Hanan wacce naga yana gama fadin hakan ta juya tabar dakin.
Gabana sai fadiwa yake.... Daddy? Mommy? Kawar mominki?.... I juz nid answers to dix questions da zuciyata ke tambayata akai.
Kaina akasa ina tunanin abinda Mubeen ya fada, "Kawar mominki ce.... " wannan maganar shi yafi tsaya min arai.
"Bugun zuciyata sannu da zuwa..... Please Zahra juz tell me dat am not dreaming....tell me dat ganinki da nakeyi agabana yanzu its reality..." Maganarsa ce ta katse min gajeriyar tunanin da nake.
Hadiye wani katon abu kamar dutse nayi wanda naji ya tokare min mak'ogoro, nace"Mubeen u ain't dreaming.... Its ur Fadima Sa'ad sitting before u.... "
Murmushi naga yayi, sannan ya juya yana kallon Suhaima wacce sai kokarin son boye fuskarta take atsakanin cinyarta, amma kash! ta makaro don ya riga ya ganta.
Nunata yayi da 'yar yatsa yana fadin"Hey! Lil sis I caught u...wato ke mai wayau wai zaki boyemin kada na ganki koh? ... Haha ai tun awaje na gama capturing faces dinku... Gaskiya kina matukar kama da My Zahra.. "
Dago kanta tayi tana dariya, tace"Kai yaya Mubeen wallahi kayi mana wayau sosai... Wato Kai kana ta kallonmu mu bamu sani ba....don't worry ai muma zamu rama"
Yace"Yo! Bah gashi kuma din kun raman ba? Ko kuwa ba kallona dukanku kuke ba yanzu?"
"Hey! Caught one looking at me now... " Ya nuna Ash queen da yatsa wacce kallonsa take amma fuskar nan tata cike yake da alamun tambaya.
Dariya muka sanya duka sai kace wurin shakatawa muke ba gidan rasuwa ba.Anan muka kawo karshen barkwancin da wasannin, muka soma gaggaisawa tare da masa gaisuwar rashin da yayi.
Yace"Oya baby Zahra sauko kuci abinci.... Lil sis, mal. Aysha asauko pls kada abincin yayi Sanyi.. " (Dama yasan Ash queen don ina yawan bashi labarinta)
"Ni akoshe nake.... " hakan na fadi cikin wata irin cool voice wanda ni kaina ban san cewar inada ita bah.
Hararar wasa naga ya jefeni dashi, yace"Ai wallahi baki isa ba.... Baby Jasmine samo min bulala na Zane beautiful antin nan naki don naga bata son taci abincin.. "
Jasmine ce naga tana kokarin fita samo bulalar, ban san sanda nace"Jasmine dawo zanci.... " bah
Dariya akayi duka, yace"Better... "
![](https://img.wattpad.com/cover/147915298-288-k880284.jpg)
STAI LEGGENDO
SHIN SO DAYA NE? (Complete)
PoesiaIt's all about heart touching love story,betrayal & hot love💗............ Karku sake abaku labari