💘SHIN SO DAYA NE?💝
TARE DA ALKALAMIN
📝
HAFSAT AL-MUSTAPHA_Watpadd:Hafnancy_
🌼BABI NA GOMA SHA TARA🌼
Page 90-95Yammaci ne mai tattare da ni'imomin ubangiji.Sararin samaniya ya mugun hade rai alamun dai kiris ya rage ruwa ya sakko.Ga wani daddadar Iska dake tashi ahankali Wanda na tabbatar awannan lokacin, zuciyoyin al'umma na cike da nishad'i sabida dadin iskar.Adaidai wannan lokacin ina kwance saman gadona,operating my system, ban wani dade da dawowa daga makaranta bah.
Gani nayi iskar da ake ta soma yin karfi da yawa,hakan ya sanyani mikewa naje na kulle windows din d'akin.
Rigar sanyi na dauko na sanya donni akwai ni da saurin Kama sanyi. Gama sanya rigar keda wuya,naji an doko sallama cikin d'akin. Suhaima ce,ina gama amsa mata sallamarta, na haye gado tare da maida hankali kan abinda nake. Don tun randa taci mutuncin Leedar agabana, ban sake bata fuska bah.
Zama tayi akan gadon,duk na lura jikinta asanyaye yake.
"Yaya Fadima barka da warhaka... " hakan naji ta fad'a cikin sanyin murya.
"Yauwa barkanki.... " Na bata amsa atakaice.
"Lovely sisturh am very sorry for my rude actions the other day.... Please kindly find a place in ur beautiful heart to forgive ur lil sis...... " Ta fadi hakan almost in tears.
"Never mind my dear... Haka rayuwar take, no one is beyond mistakes....Suhaima na tambayeki mana? "
Da sauri tace"Ina jinki sis... "
"So nake ki fad'a min tsakaninki da mahaliccinki.... Shin akwai wani abu ne daya dad'e yana damunki azuciya? Koh kuma wani ya taba miki laifi ne da har yau kika kasa yafe masa?.... Ki fad'a min gaskiya kinga baki da 'yar'uwa mai Sonki kamar ni.... " Nayi mata wannan tambayar tare da tsareta da idanuwa.
Lol! Kar kuso kuga yadda yanayin Suhaima ya koma,remember yadda yanayin Wanda yake shirin k'arya yake komawa right? Toh hakan yanayinta ta rikid'e ya koma.
"Seriously sis babu abinda ke damuna wallahi..... Buh why diz questions? Koh kinji wani abin ne? " Yanayinta mah ya nuna she's so confused.
"No, juz feel lyk asking u such questions... Toh naji.... Yaushe zaku soma exams? "
"Ran Monday insha Allah... " acewarta
Nace "Good, Allah ya bada sa'a.... Would u be free on Friday? Jibi kenan?.... "
"Yea... Throughout ina gida... "
"Alright ki shirya..... ranar zamu je ABU tare,want u to study the environment kafin ki samu admission anan.... "
Cike da murna tace"wow sis thank you so much wallahi kamar kin san ina masifar son naje naga environment d'in ABU kafin na sami admission.... amma hope ke da kanki zaki sanarwa su Umma...?"
"Wannan bah matsalarki bace... I will take care of dat as usual... tashi ki tafi please kada ki cikani da surutu, kinga am doing something very important here kar kisa nayi mistake... "
At once ta mike ta fice daga d'akin ba tare da ta min wata gardama bah.Tunanin Mubeen d'ina ne ya fad'o min arai.Agaskiya ni kaina nasan nayi matuk'ar missing d'insa wanda atake anan naji zuciyata na son taji daga gareshi if he is really okay at all.
Samun kaina nayi da daukar wayata,nayi dialing lambarsa,ai kuwa nayi sa'a call d'in ta shiga har ta soma bada wannan boring tune d'in nan wato 'bum-bum'
KAMU SEDANG MEMBACA
SHIN SO DAYA NE? (Complete)
PuisiIt's all about heart touching love story,betrayal & hot love💗............ Karku sake abaku labari