💘SHIN SO DAYA NE?💝
TARE DA ALKALAMIN
📝
HAFSAT AL-MUSTAPHA_Watpadd:Hafnancy_
🌼BABI NA TALATIN DA HUDU🌼
Page 157-159
*RAYUWAR MUBARAK AKASAR INDIA*
Rayuwar Mubeen akasar India rayuwace yake yinsa adaddafe sabida har Xuwa wannan lokacin be samu ganawa da Fadimarsa ba kamar yadda yayan nasa yayi assuring dinsa cewar washegarin tafiyarsa zata mallaki wayar da take ta jira.Toh kuwa tun awashegarin ranar yake ta gwada layinta don shi ya kamata ya kira because ita bata da lambarsa ta nan,se de idan ba Mahmood ne ze tura mata ba,kuma koda ya turan mah ai bazata juri kiran layin k'asar waje ba sabida it will caused alot of charges,gwanda shi ya kira ze fi sauki.
Zuwa yanzu ya riga ya gama yardarwa kansa cewar raina masa hankali Mahmood yake,kwata-kwata beje gidansu Fadimar ba.Har yanzu de maganar daya ce da yake gaya masa.
"Wayar har yanzu be shiga hannunta ba,ita kuma taki kowani waya wai se wannan din..... "
Sam wannan maganar ba abinda hankali ze dauka bane,taya za'ai yace masa taki kowani waya se wannan? Ita ko kadan bata tausayin halin da shi ze iya shiga ne idan beji daga gareta ba?
Idan yayi wannan tunane-tunanen se yayi ta ganin kamar raina masa hankali Mahmood din yake masa.Jiya mah bata dadi suka rabu dashi ba awaya.
Ce masa yayi"Anya Yaya Mahmood kaje gidansu Fadimar nan kuwa? Kodai k'aryace kake min don kawai hankalina ya kwanta.?..... "
Azuciye yace masa"Yanzu Mubarak don rashin kunya ni kake nemar karyatawa? Ba damuwa gobe mah ai ranace.
Mubeen be sake cewa komai ba ya yanke call din.Abokan aikinsa Dr.James da Dr.Vera idan suka gansa cikin damuwa tsiya suke masa don aganinsu kewar matarsa Hanan ce ke damunsa,basu san cewar damuwar ta antyn Hanan dince bane (lol).
****
*KAWO GAISUWA**BAYAN SATI BIYU*
*SATURDAY,4:00PM*
Misalin qarfe hudu ta yammacin ranar asabar aka kawo gaisuwar Fadima Sa'ad Mainasara da kuma 'yar'uwarta Suhaima Sa'ad Mainasara.Ah bangaren Haidar,Kanin mahaifinsa Mal.Bala,abokin Babansa Alh Nafiu,se kuma wan mahaifinsa Alh.Tanimu suka zo.Bangaren Mahmood kamar yadda akace shine wanda ze auri Fadimar,Alh.Mu'azzam wanda kanin mahaifinsa ne,yazo da tasa tawagar mutane har biyar,shine cikon na shida.
Bangaren masu k'arbar gaisuwar kuwa,bayan mahaifinsu Fadima Justice Sa'ad,akwai kannensa biyu da kuma wansa wadanda suka taso tun daga Adamawa don k'arbar gaisuwar 'ya'yan nasu.Daya daga cikin kannen nasa,wan Haj.Kareema ne (idan zaku tuna nace muku auren dangi sukai,so duk dangin Justice Sa'ad na Haj.Kareema ne itama).Hahaha! hatta Kanwarta Anty Hajaar seda ta biyosu.
An karrama bakin sosae,girki kala-kala akai masu kai kace koh ranar bikin ne.Suka nemi auren Fadima da Suhaima wa 'ya'yayen nasu,kuma an basu,aka yanke masu sadaki dubu hamsin-hamsin don nemar albarkar aure.Sukace sam 'yan matan sunfi k'arfin dubu hamsin awajensu.Da k'yar Su Abba suka yadda suka k'arbi dubu dari-dari,don ada mah waliyyin Fadima yayi niyyar bada dubu dari biyu ne kamar yadda saurayin nata yace abayar.Amma Abba yaki yace adai kawo dubu darin.Aka tsaida lokacin biki nan da wata daya cur! babu ragi haka kuma babu kari kamar yadda Abba ya fada tun farko.Toh! Jama'a sae muce Allah ya kaimu lokaci musha bikin Fadima da Suhaima.
![](https://img.wattpad.com/cover/147915298-288-k880284.jpg)
YOU ARE READING
SHIN SO DAYA NE? (Complete)
PoetryIt's all about heart touching love story,betrayal & hot love💗............ Karku sake abaku labari