PART 2:CHAPTER NINE

1.8K 123 0
                                    

*💘SHIN SO DAYA NE?💝

      *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION📖✍*

       *{Onward together}*
*{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}*
'''THE PEN OF LOVE😘 HEART  TOUCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINK 💑'''
*JUST GIVE US FOLLOW.....*✔

        *MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA*

         *WATPADD:HAFNANCY💞*

          *IG:Hafsy____mustee*

                        ✨✨✨

_*wannan page din taki ce ke daya my Janaf💞,don haka kiyi yadda kike so da ita,Allah yabar qauna da zumunci*_

                          💥💥

*KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE*

         🌼BABI NA TARA🌼

*page 23-26*

    Wuraren 7:10 Fadima ta farka daga nannauyar baccinta,k'arar ruwan wankan Mahmood dake zuba ak'asa ne ya tasheta.Ahankali nake bin dakin da kallo,dakin namiji kenan babu ruwansa da tara kayan k'warmasai,komai tsaf-tsaf dashi,dakin dan gayu kenan,sae wani daddad'ar kamshin turaren daki ne ke tashiwa,gaskia Mahmood akwai tsafta da kuma son gayu.lalubo wayata nayi dake ajje gefen filon da nayi matashi dashi,niyyata na latso Suhaima don ranar da Abba ya maida min da wayata,toh ita kuma aranar ya damk'a mata sabuwar dalleliyar waya.

    Ban kai ga latso layin nata ba kawai naji Mahmood na kiciniyar bud'e kofar bathroom.Da sauri na maida wayar na ajje don bana son yaji duk wani abinda zamuyi discussing da ita.idanuwana fes akansa sanda ya fito,daga shi sae 'yar gajeriyar wando wato 'boxers',hannunsa rik'e da wani k'aramin towel yana tsane kansa dashi.Da sauri na runtse idanuwana tare da dauke kallona daga gareshi don tunda nayi wayau ni de ban tab'a ganin namiji balagi ahakan ba.

shi kuwa ya lura da yanayin data shiga,wato dai bata ji dadin ganinsa ahakan ba kenan.Murmushi ya saki tare da jefar da jikakken towel din agefe,Sannu ahankali ya taka sadaf-sadaf cikin sanda xuwa gareta ba tare da ta sani ba don har yanxu idanuwan nata arufe suke.Cak! ya dauketa kamar wata 'yar baby.

     Ni kuwa saurin bud'e idanuwa nayi jin wani bak'on al'amari ajikina wato ayau jikina yayi gogayya dana baligin namiji,don sosae ya rungumeni ak'irjinsa kamar wanda baya son ak'wace masa ni.

"Please dear nah meye haka? don Allah ni ka saukeni.... " na fadi hakan kamar xan saki kuka.

    Murmushi meh sauti naji ya sake kawai ba tare da yace min uffan ba.Be direni ako'ina ba sae acikin bath tub.

Yace"oya Maza ga ruwan wanka nan na hada miki kiyi,idan kuma so kike ni na miki toh shikenan.... "

    Zaro idanuwa waje nayi"sae kace wata 'yar baby? No ka fita pls xanyi da kaina.... "

Ahankali yace"Ai ke din babyn tawa ce.... " ya kashe min ido daya,kana ya juya ya lakuto min maclean akan brush sannan ya miko min,ya janyo min wani dan babban towel dake rataye akan kofar bathroom din tare da azawa saman wata igiya,yace"Ga towel nan idan kin gama sae ki dauro.... "

SHIN SO DAYA NE? (Complete) Where stories live. Discover now