💘SHIN SO DAYA NE?💝
TARE DA ALKALAMIN
📝
HAFSAT AL-MUSTAPHA_Watpadd:Hafnancy_
🌼BABI NA GOMA SHA BIYU🌼
Page 55-60
BANGAREN LEEDAR
Leedar ne zaune saman sallaya ya idar da sallar asubahi. Ya hau rera karatun Qur'ani cikin zazzak'ar muryarsa mai dadin sauraro. Bashi ya dakata daga karatun bah har sai daya ga gari ya soma haske sannan ya ijje Qur'anin yaje ya kwanta.So yake ya koma bacci amman baccin yaki zuwa. Idan ya rufe idanuwansa yayi kamar zaiyi baccin sai kuma kaga yayi saurin bude idanuwan.
Kana ganinsa kasan yana tattare da damuwa, don hankalinsa mah ah tashe yake.Dauko wayarsa dake saman gadon yayi, ya sanya k'iran Fadima akaro na barkatai, don tun yammacin jiya yake ta trying line dinta amman yaki shiga, sai faman ce masa 'switched off' ake.
Wannan karon mah 'switched off' d'in aka sake ce masa wanda haushin hakan ya sanyashi yin cilli da wayar saman gado har takai karshen gadon, kiris! ya rage ta fado k'asa amman koh ajikinsa.
Rasa inda zai sanya kansa yayi.
"Anya pretty tana lafiya kuwa?" Hakan ya fadi afilli cikin tsananin tashin hankali don shi dai sanin da yayi wa Fadima bata taba barin wayarta babu chargy,koda babu wuta toh za tayi charging d'insa da wutar Generator.
Ya tabbatar da cewar amsar tambayarsa yana ah gidansu Fadimar. Don haka ya yanke shawarar zuwa gidansu d'in idan gari ya gama wayewa.
Daga hakan bacci barawo yayi awon gaba dashi mai nauyi kuwa don bai sami wani wadataccen bacci bah adaren jiya,all thinking abouh Fadima Sa'ad.(Hahaha ke dai 'yar fillo kin shiga uku)
BARI MU WAIWAYI MUBEEN
Tunda motarsu Fadima ta tashi, ya bi motar da idanuwa,bai daina kallonsa bah har sai daya ga motar ta bar layin.Tambayar kansa yake, "anya na kyautawa Zahrata kuwa? "Meyasa zan boye mata cewar ina da mata har da 'ya? Why will I keep our relationship secret to my family? Wanda na lura abinda mah yafi b'ata mata rai kenan?"Tambayoyin daya shiga jerowa kansa kenan wanda bashi da amsar ko daya. Gunjin kukar Hanan ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya lula.
Sannu ahankali ya juya ya soma takawa har yakai inda take tsaye take kukarta mai taba heart.
Ganin ya iso dab da ita ne ya sanyata saurin d'aga masa hannu,tace"Mey kuma zaka ce min? Koh ba'a fad'a bah kowa ya shaida ka fi sonta akaina.... Na maka abinda kakeso don farin cikinka mijina ya fiye min komai... Zan iya jure koh wani irin kuncin rayuwar da zan shiga indai akanka ne....Inaso ka bani izini ni da kaina zanje na nuna wa Mummy cewar nice na baka goyon bayan ka k'aro wani auran..... Abu Jasmine bana kaunar wani abin ya sameka sabida bah karamin so kake yiwa wannan baiwar Allahn bah.... So juz permit me to talk to Mum abouh it...... "
"And do u think diz is a minor problem da har kike tunanin tunkarar mum da wannan maganar? "
Murmushin takaici yayi, sannan yace"Hanan ke kanki kin kwana da sanin cewar yadda mummy ke masifar kaunarki ba zata taba yadda na karo wani auren bah.... Ke dai kawai ki bari zanyi handling wannan issue din da kaina.... Will meet her tomorrow."
Kokarin magana take ya katseta ta hanyar rungumota"Shhhhh! Its okay Hanan dita don't say anything again.... Kuma bana son kina fadin cewar nafi sonta akanki... No, kowacce da matsayinta azuciyata, zan mah iya cewar matsayinki yafi nata aguna because ke din 'MATATACE' kuma 'UWAR YA'YANA'........ Don gashi muna expecting wani babyn very soon.... " Ya fadi hakan tare da shafo 3months old pregnancy dinta wanda babu wanda zaiyi tunanin tana da ciki sai su d'in da suka san da abinsu.
YOU ARE READING
SHIN SO DAYA NE? (Complete)
PoetryIt's all about heart touching love story,betrayal & hot love💗............ Karku sake abaku labari