CHAPTER NINE

1.8K 150 0
                                    

  💘SHIN SO DAYA NE?💝
     
    TARE DA ALKALAMIN
           📝
      HAFSAT AL-MUSTAPHA

_Watpadd:Hafnancy_

            
        🌼BABI NA TARA🌼
   Page 40-45
Zai soma magana kenan mukaji k'arar tsawa wanda k'arar ba k'aramin tsoratani yayi bah, kuma adaidai lokacin text message ya shigo wayata daga Ash queen,kamar haka,

"Malama hope kina dai ganin had'ari koh?  and dix is 15mins to 1pm... Don Allah duk inda kike ki taso mu kama hanya kada ruwan nan ya sauko bamu bar garin nan ba... "

Ina gama karantawa na d'ago kai ak'idime ina kallon Mubeen nace"Mubeen don Allah mu tafi kawai kada ruwan nan ya sauko ya tsayar damu anan...Gashi Ash ta min text wai nama taso mu kama hanya kawai... So juz leave the discussion zuwa wani lokaci idan kai ka kawo min taka ziyarar.... " Na mike da niyyar fita ah 'joint' din.

Da sauri naji yace"Don Allah Zahra ki tsaya ki saurareni don yau nake son muyi ta ta k'are... "

"No Mubeen bazan iya saurarenka yanzu bah don gaba d'aya hankalina ya k'arkata zuwa gun 'yan'uwana da kuma can Zaria..... " Na fadi hakan cikin k'osawar mu bar wajen.

"Koda kuwa zan fadi miki cewar akwai dangantaka mai k'arfi tsakanina da HANAN... Shi din mah bah zaki tsaya ki saurareni bah....? "

Da sauri na kalleshi,na koma na zauna da mataccen jiki. Cikin rashin kuzari nace"Ban fahimta bah... Pls ka fitar dani acikin duhu.... "

Ahankali ya cigaba da magana kamar bai son yayi, yace"HANAN is my wife not a blood sis...and JASMINE is our 4years old daughter........... "

Ak'idime na mike ina fadin"What????? Mubeen mai kunnuwa suke jiye min?? Mubeen dama ashe kana da aure yaudarata kawai kake son kayi.... ? pls answer me now.... " Na fadi hakan already in tears Allah mah yasa inda muka zauna babu mai jin abinda muke fada sai dai yaga actions namu.

"Don Allah Zahra take it easy I can  explain...."

Cike da tsiwa nace"U can explain what??? everything here is clear and straight forward..... Hanan matarkace and Jasmine 'yarka... Toh What else do u want to explain here again??....  Mubeen nidai juz accept the fact dat ka riga ka gama da rayuwata totally... " Na karashe maganata cikin tausayawa kaina, sannu ahankali na soma rera kuka mai tsuma zuciya.

Sai daya kyaleni nadan taba kukan maybe don na dan sami rest of mind ne don kun san ance wani kukan yakan yi reducing pains, zuciya takan sami dan sassauci.

Don kaina nayi shiru, na koma yin kukan zuci. Ganin nayi shiru ne ya bashi damar cigabawa"Hanan 'ya ce ga wata k'anwar Mummy. Mummy itace tayi rik'onta tun tana yarinya har zuwa sanda ta mallaki hankalin kanta.Tun tana k'aramarta yarinyar ta shaku dani, nima hakan na shaku da ita.

As time goes on, shakuwarmu ta wuce over wanda na lura ita yarinyar mah harta kamu da matsanancin sona, ni kuma har ga Allah Soyayyar wa da k'anwa kawai nake mata.

Ganin ta kamu da matsananciyar soyayyata ne ya sanya na soma k'aurace mata don bana son soyayyar ta mata yawa acikin zuciya har tazo mata illah.Ashe abinda ban sani bah kuwa shine, ashe dama can Mummy ta kudira aranta son ta had'amu aure ni da Hanan d'in.

Sanda tajewa Mahaifinmu da kudirin nan,  nata atake yayi na'am da zancen tare da nuna mata lallai yama fita son wannan had'i.Mahaifiyata kuwa tama riga ta rasu kafin wannan zancen ya taso, koda yake even if she was alive,nasan bah zata hana hakan faruwa bah don yadda suke zaman lafiya da Mummy da kuma yadda taga Mommin ke masifar kaunata dole ta mata k'ara ta hanyar yin na'am da batun.

SHIN SO DAYA NE? (Complete) Место, где живут истории. Откройте их для себя