®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**JINI D'AYA*
*Wattpad@Ayshatmadu*
2
Bayan wasu shekaru k'alilan.
Zaune suke cikin palour. Suna fira cikin so da k'aunar junansu.Dariya yayi tare da kai mashi duka a kafad'a. Kallonshi yayi shima cikin dariya yace.
"Kai Daddy nafa girma da duka ko ba haka ba Mommy?"
Mommy tayi dariya tare da cewa.
"Kaga yau ni nawa ido ne ba ruwana a ciki."
Daddy ya k'ara dariya tare da mik'ewa yace.
"Yau tunda har Mommy tace ba ruwanta a ciki zan nuna maka baka wuce duka ba."
Da sauri Jawad ya mik'e ya fara zagaye d'akin Daddy na binshi da gudu.
Fad'i yake "Daddy sorry!"
Duka d'akin dariya suke, Yaya Najib har da hawaye saboda dariya. Da gudu ya k'arasa jikin Mommy.
"Mom kada ki bari ya bigeni."
Dariya suke Mommy tace.
"Daddy gashi ka buga son ranka ba taimakon da zan maka, jiya kai da Daddy haka kuka tasomu cikin gidan nan, dan haka ba abinda ya dameni ku k'arata."
Marairaicewa yayi tare da kama kunnanshi da duka hannyenshi yace.
"I'm sorry mommy! Ba zan k'ara ba, nima ba ruwana da Daddy daga yanzu kece ta hannun damana."
"Najib kajishi mu yarda ko kada mu yarda?"
Cikin dariyar mugunta Yaya Najib yace.
"Mommy kada mu yarda dashi kin sanshi baki biyu gareshi a gidan nan. Ko ba haka ba sister."
Maryam na dariya tace.
"K'warai kuwa Yaya."
K'ara marairaicewa yayi da fuska yana kallon Daddy yace.
"Dad kaga duk sun juya min baya ko, miye abinyi? Kawai mu had'a kanmu mu k'yalesu."
Dariya Daddy yayi tare da mak'e kafad'a had'i da cewa.
"No nak'i wayan naka."
Dariya suka hau yi mashi gaba d'aya, komawa yayi ya zauna tare da tamke fuska, alamun sun 'bata mashi rai ba ruwanshi dasu.
K'arasowa wurinshi suka yi gaba d'aya, suna dariya had'i da duk'awa suka dafashi suna mai mashi magana cikin kyakyakyawan lafazi.
"Haba miye haka, ni dai ban san Jawad d'an uwana da fushi ba, common mik'e mu isa field mu d'an wasa jikinmu."
Janshi yayi suka yi d'aki suka yi shirin fita. Dama k'a'ida ce da yamma sai sun fita sun d'an buga k'wallo, basket ball ko bollyball.
Suna isa compound d'in wurin Najib ya fara d'aukan k'wallon, Mommy ta samu kujera ta zauna tana kallonsu gwanin sha'awa da murmushi d'auke a fuskarta, tana jin dad'in yanda gidansu ke tafiya.
Maryam ce ta zagayo ta bayan Mommy ta rungumeta ta baya itama d'auke da murmushi a fuskarta, ri'ke hannun nata gaba d'aya Mommy tayi.
Yaya Jawad ya kalleta yace.
"Sister ya akayi yau ba zaki yi wasan bane ba? Kinfa fi son basketball."
D'an girgiza kanta tayi tace.
"Yaya yau bana jin yin wasan ne gaba d'aya."
Jin abinda ta fad'a yasa gaba d'ayansu suka yo kanta da tambaya, cikin kulawa Daddy yace.

YOU ARE READING
JINI D'AYA
Fanfictioncikin d'aga murya mai rikitarwa yayi magana wanda yasa tayi saurin d'ago da rinannun idanunta da suka rine daga kalar fari suka koma ja. "ina so ki fita a harkata, mace wadda ta san mutuncin kanta nake so na aura ba ba wadda ta watsar da nata a titi...