Ta tafi

465 20 3
                                    

*JINI D'AYA*

®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

©
*EASHA MD*

*Wattpad@Ayshatmadu*

           *4*

Fitowa tayi d'auke da jakarta a hannu ta dubesu gaba d'ayansu tace.

"Jirgi zaya d'aga, sai ince sai na dawo, amma fa zanyi missing d'inku da yawa, kamar in fasa tafiya."

"Ke kyaji dashi dama kin tafi Allah ya kiyaye hanya."

Cewar Hajja dake zaune tana kankare k'umbanta.

Su Adama ne suka mik'e dan rakata, furaira ta amshi jakarta ta ri'ke mata, zasu wuce ta k'ara shiga d'akin Mallam Babba dan yi mashi sallama.

"Har zaki tafi kenan?"

"Eh Mallam sai na dawo."

"To ki kula da kanki, bana so kije saboda karatunki,"

"Mallam ai ka san Mallam Ali ke k'ara mana karatu, zai rin'ka k'ara min a gidansu."

"To shikenan, hakane kuma."

Ta mik'e zata tafi, har ta kai bakin k'ofa ya dakatar da ita da fad'in.

"Aishatu dawo kisha rubutu gashi nan yanzu na gama rubuta maki, kinga gashi har na manta."

Tsayawa tayi cak, had'i da d'an 'bata fuska, sannan ta juyo ta dawo ta zauna ya mik'a mata, ba yanda zata yi dole ta amsa ta shanye ta mik'a mashi cup d'in.

"Yauwa 'yar albarka Allah ya dawo min dake lafiya."

Mi'kewa tayi ta fita suka rakata har bakin titi ta hau keke napep ta tafi tana d'aga masu hannu.

Tana isa gidan ta rataya jakarta ta sallameshi ta shige ciki.

Tana shiga palour da sallamanta, Aunty Fanna ta tareta da.

"Ga d'iyata ga d'iyata. Ya gida?"

Nan ta gaidata ta amsa cikin sakin fuska.

"Ina su Yaya Asiya fa?"

Sun fita amso d'inki nan mak'wafta yanzu zaki gansu sun shigo." Mi'kewa tayi ta shiga ciki ta aje kayanta sannan ta dawo wurin aunty Fanna suna d'an ta'ba fira su Asiya suka shigo.

Ganinta yasa suka fad'ad'a fara'arsu.

"Allah sarki 'yaruwa! Jiya muka gama labarinki kwana biyu bamu ganki ba saboda bamu shiga makaranta ba."

"Aikuwa ai gani nazo, Mallam Babba ma na son ganinku na isar da sak'onshi.

Had'a ido suka yi gaba d'ayansu tare da warosu waje, Fatima tace.

"Tofa neman mai Mallam yake mana? Allah dai yasa lafiya ba laifi muka yi ba, ko dai rashin zuwanmu islamiyya ne?"

Ta idasa maganar tana kallon 'yaruwarta.

"Kai a'a bana jin rashin zuwanmu ne, sai dai idan wani abin ne daban. Ko Humaira kin san dalilin da yasa yake nemanmu? Dan na san ba zaki rasa sani ba tunda kullum kina tare dashi?"

Cewar Asiya da tayi maganar tana kallon Humaira. Dariya tayi kana tace.

"A'a ban san dalili ba, sai dai idan kunje kwaji dalilin da yasa yake nemanku."

Ta koma ta kishingid'a jikin kujera.

"Sister ai bamu ga ta zama ba yau ya kamata muje mu gana da mallam."

Asiya tace. "Shikenan bari yamma tayi sai muje."

Aunty Fanna dake zaune tayi dariya tace. "Wai duk wannan rud'ewar ta miye haka sai kace wad'anda suka yi laifi?"

JINI D'AYAWhere stories live. Discover now