*JINI D'AYA*
®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**Wattpad@Ayshatmadu*
*10*
Washegari ta shirya da wuri, ta fito ta samu Mommy a d'aki, gaidata tayi ta amsa cikin kulawa. Kana tace "Ya akayi Humaira?"Tana wasa da yatsunta tace "Dama gidan Yaya Maryam nake so in je na kwana biyu banje ba."
Dariya Mommy tayi tace. "Shine abin jin nauyin fad'a min, Humaira ya kamata ki saba damu zama ne fa zamuyi dake na har mu aurar dake, idan kina haka taya zamu san matsalolinki da abinda kike so har mu maki? Ina so duk abinda kike so ki rin'ka fad'a ba tare da kinji komai ba."
D'aga mata kai tayi. "Yauwa 'yar albarka, da yaushe zaki tafi?"
"Zuwa nan da anjima."
Har zata fita Mommy ta tsaidata da fad'in. "Humaira mai zaki ci ne dan nima ban yi break ba? Saboda daddy'nku tun asuba yayi Maiduguri."
Waro idanu waje tayi kana tace. "Maiduguri kuma Mommy? Shine bamu san da tafiyar ba?"
"Nima jiya d'aya daya dawo da daddare yake fad'a min Maiduguri zashi."
"To Allah ya dawo mana dashi lafiya. Da plantain zan soya da k'wai, Yaya Jawad baya nan bare yaji dad'in sani aiki da yawa, ke me kike so in maki?"
D'an jim tayi sannan tace. "To nima yi min hakan ya isheni, Talatu ce wai bata da lafiya shiyasa har yanzu ba ayi komai sai ki had'a da ita da Mallam Habu mai gadi."
Bayan ta amsa mata ta fita, ta fara had'a komi, sanin duk abinda zata yi zasu so yasa da sauri ta d'an ji'ka shinkafarta da gyad'arta da ruwan zafi dan yayi saurin yin taushi bayan ta fara soyawa tayi saurin markad'a gyad'ar ta d'aura kan gas, saida ta kusa gama suyar sannan ta markad'a shinkafar shima ta tace.
Bata wani d'auki lokaci ba ta gama had'a komai, zuba ma Talatu nata tayi ta kai mata har d'aki, tayi mata sannu, ta aje mata, godiya ta mata ta fita, ta had'a na Mallam Habu ta kai mashi nashi, dawowa tayi ta had'a masu nasu ta fito dashi, Mommy ta fito itama bayan tayi wanka ta shirya. Zama suka yi suna break d'insu su tare suna d'an fira.
"Wai Mommy yau Yaya Jawad da wuri ya fita ne?"
Amsa ta bata da cewar. "Ai tare suka tafi, yace wai ya dad'e bai je Maiduguri ba."
"Wai lallai yau ana shan hanya, da sun sani sun fad'a min munje tare, saboda ina son inga Hajja da Mallam Babba da friends d'ina."
Momma tace. "Kada ki damu zaki je, bari ya dawo sai in fad'a mashi ya za'ba maki lokacin da yaga ya dace kije sai ki gansu."
Tun ba a ce an barta ba ta fara jin dad'i. "Momma na gama bari in tafi."
"To in kije ina gaidata sosai." D'aki ta koma ta k'ara gyara jikinta, lifaya ta nad'a ta fito, mommy ta bata na machine tayi godiya ta tafi.
Tana isa gidan Maryam da take zaune tana kallo ta mik'e da sauri ta rungumeta tana jin dad'i. "Kai Yaya Maryam wannan irin murna haka ai sai ki karyani irin mamutsa haka."
Kujera suka k'arasa tana cewa. "Ke ko ba dole ba, yaushe rabonki da gidan nan kamar an maki wani abu. Me kike so in had'o maki?" Mi'kewa tayi ta fara kawo mata kayan ciye-ciye, tana tambayarta su Mommy. "Yau ina bindin naki na ganki ke kad'ai?"
Zaro idanu Humaira tayi had'i da ri'ke baki tace. "Kai Yaya jawad d'in ne bindi? Aiko zai ji labari sai na fad'a mashi."
Tana dariya tace. "To ai na san bindinki ne, ni ban san wane irin shak'uwa yake tsakaninki dashi ba, zanga ranar da zaki aure ya zaiyi."

YOU ARE READING
JINI D'AYA
Fiksi Penggemarcikin d'aga murya mai rikitarwa yayi magana wanda yasa tayi saurin d'ago da rinannun idanunta da suka rine daga kalar fari suka koma ja. "ina so ki fita a harkata, mace wadda ta san mutuncin kanta nake so na aura ba ba wadda ta watsar da nata a titi...