*JINI D'AYA*
®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**Wattpad@Ayshatmadu*
*3*
Tana idar da sallah gami da laziminta, tana nan zaune har aka kira isha'i, saida ta gabatar kana ta fito tsakar gida ta samu wuri kan tabarma ta zauna.Isuhu ne ya shigo ta dubeshi fuskarta a sake tace.
"D'an isuhulle lukuti! Wallahi isuhu duk kafi kowa cin abinci gidan nan, shiyasa gaka nan kamar dutse saboda girma, wai ko baka jin nauyin jikinka? Zo isuhulle ka fad'a min ba wanda zai ji."
Hajja dake ciki ta hau mata gyaran murya, isuhu dariya ma ta bashi."
"To Hajja sarkin karambani, kina sallan ma kunnanki na waje, kaji isuhu k'yaleta zo ka fad'a min yau kwanonka cike, amma sai in ka fad'a min."
Hajja data fito ta d'aka mata duka, had'i da cewa.
"Ke dai Humaira Allah ya shiryeki."
"Hajja gaskiya kina yawan dukana a gidan nan fa, zan fara ramawa fa."
Ta idasa maganar tana girgiza kai had'i da d'aga fuskar nan sama.
K'ara d'aka mata duka tayi tace.
"Gidanku! Nace gidanku! Uban wa zaki duka ni?"
Zum'buro baki tayi tace.
"Aryan zan buga, ni na isa in dukeki? Amma gaskiya Hajja ki daina dukan kyakykyawar jikin nan nawa in dai ba bak'in ciki kike dashi ba."
"Dallah ni rufe min baki da wannan bak'ar fatar nan taki, niko baki ga tawa ba fara tas."
Dariya Humaira tayi kana tace.
"Wayyo duniya ina sonki zan barki, ai Hajja wannan farin naki idan ni keda shi ko, sai nayi yanda zanyi ya dusashe, kin san farin ma kala kala ne, akwai mai kyau akwai mara kyau, taki sai kace na tsohuwar zabaya."
Su Adama da suka fito ita da furaira, dariya suka hau yi. Furaira tace.
"Humaira kika ma Hajja data ci kashinki waye a duniyar nan ba zaki mawa ba."
Itama dariyar ta hau tayasu, isuhu dake tsaye har yanzu, shi kanshi dariyar yake.
"Kai isuhulle mai kake har yanzu baka fita ba? Ko dai har ka cinye ka dawo ka k'ara ne?"
Dariyar yaci gaba dayi. Aryan ya shigo ya samu guri kusa da Hajja ya zauna, Humaira ta mik'e saida ta dafa kan Aryan ta girgiza kana tace.
"Yusufa d'an gidan Hajja."
"Dallah ni k'yaleni bana so."
Rank'washi ta kai mashi a kai ta wuce. Yana sosa wurin yace.
"Hajja kin ganta ko?"
"K'yaleta ka ganta nan tun d'azun ta addabemu, ka san halin 'yar uwar nan taka."
Kafin ta sallami isuhu sai da ta gama tononshi, sannan tazo tasa nata abincin, ta jawo kwanon man shanu ta tsiyaya son ranta, kana ta jawo robar yajin da yaji daudawa ta fara barbad'awa Hajja ta d'auke robar tana fad'in.
"Yaji duka yaushe aka kawoshi har kin kusa shanyeshi, dan haka ya isheki haka."
Kallon Hajja tayi ta saki murmushi ba tare da tace komai ba ta fara cin tuwonta.
Haka ta zauna duk wanda ya shigo sai ta toneshi haka ta dawo kan furaira.
"Ke kuma furaira dan kar kiyi aiki shine kika shige kika kwanta wai kanki na ciwo, amma yanzu tashinki ya kai nawa wurin k'aro miya kunji miya mai dad'i ba irin naku ba. Ke ni fa duk wani pretending na mutum ba wanda ban sani ba."

YOU ARE READING
JINI D'AYA
Fanfictioncikin d'aga murya mai rikitarwa yayi magana wanda yasa tayi saurin d'ago da rinannun idanunta da suka rine daga kalar fari suka koma ja. "ina so ki fita a harkata, mace wadda ta san mutuncin kanta nake so na aura ba ba wadda ta watsar da nata a titi...