12 Zamani

312 19 5
                                    

*JINI D'AYA*

®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

©
*EASHA MD*

*Wattpad@Ayshatmadu*

           *12*
Tunani ya'ki barin 'kwa'kwalwarta, mai yasa Yaya Jawad ya min haka? Idan har zan barshi abinda zai ci gaba da min kenan tabbas. Dogon ajiyar zuciya ta sauke, gaba d'aya ji tayi bata son fita palour, domin gani take kamar idan ta fita za a gane abinda ta aikata, har yanzu tambayar kanta take, wai dama Yaya Jawad d'an iska ne ko kuwa duk cikin son da yake mata ne kamar yanda ya fad'a? Ya zama dole in nisanta kaina dashi idan ba haka ba tabbas nan gaba ba zan iya hanashi abinda yake son yi dani ba. Ji tayi wani hawaye ya sauko mata.

Hannu tasa ta share hawayen tare da jan majina. Komawa tayi ta a hankali ta kwanta kan gadon wanda har yanzu hawaye bai daina zubo mata ba. Ji tayi an turo 'kofar d'akin, ba tare da ta d'ago taga ko waye ba, ta share hawayen dake idonta. Bata ankara ba taji an d'ago da kanta, kwantar da ita yayi kan kafad'arshi yace. "Mai ya sameki Humaira?"

Nunashi tayi da hannunta tana kuka tace. "Kai ne bana son irin abin nan a rayuwata, saboda Allah zai tambayeni na sani ba kyau kuma kaima ka sani ba kyau."

D'ago da fuskarta yayi yana kallonta yace. "Humaira mai na miki? Ni ban maki komai ba, kike cewa ba kyau ai ba zina muka yi ba, kuma ni zan aureki fa miye a ciki, d'an 'karamin laifi ne wanda da munyi sai mu nemi gafarar Allah."

"Amma Yaya ka san..." Ya katseta "Shiii! Yi shiru Humaira, kin gane sonki ne ya jamin haka, aure fs zamu yi kinga yanzu zaki ga Dad ya sama min aiki, da na fara lokacin kin fara karatunki ba sai muyi aure ba. Yanzu idan nayi mashi maganar ina son na aureki ba zai yarda ba, zai ce in bari ki fara karatu, ni kuma ba zan jure ba idan har ina tare dake sai hannuna ya kai jikinki."

Zum'buro baki tayi tace. "To tunda haka ne ai sai muyi nesa da juna da shaid'an yazo ya rin'ka shiga tsakaninmu."

"Humaira ba zaki gane bane, ni kuma ba zan iya nesa dake ba, burina a kullum in jini kusa dake."

Bubbuga 'kafarta tayi a k'asa tace. "Ni gaskiya Yaya Jawad bana so idan kuma kace zaka takura min sai in koma Maiduguri."

K'ura mata ido yayi wanda har ya fara lumshesu, kallonta yake ba 'ka'k'kautawa, wanda ita kuma gaba d'aya hankalinta ya tashi ji tayi tsoro ya fara kamata, da sauri ta mik'e zata bar wurin ya jawota, hannunta ya ri'ke tam. K'o'k'arin 'kwacewa take yi. Cikin kasalalliyar murya yace. "Please Humaira sau d'aya kawai."

Kuka ta fara mashi tana 'ko'karin 'kwace kanta amma ta kasa. "Humaira ba zan maki abinda kike tunani ba, abu d'aya ne kawai, ni kaina ai ba zanso in maki haka ba." Shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya, har yanzu a tsorace take tace. "Idan wani ko Mommy ta shigo fa?"

"Ba wanda zai shigo daga ni sai ke."
Tana k'o'k'arin tureshi tace "Amma ai Allah yana ganinmu ko? Kuma zai tambayemu a kan abinda muka aikata."

"Humaira zamu tuba fa ba wani abu bane, kece kike tsoron haka."

"Amma Yaya idan Allah ya d'auki rayuwarmu a haka fa?"

Toshe mata baki yayi da hannunshi, dan maganarta ya fara isarshi.

Kuka take tana kai mashi bugu, magana ya fara mata a hankali. "Humaira kin san ba zan cuceki ba, kada ki manta kefa jinita ce, dan haka ki fad'a min ta yanda za ayi na cutar dake? Iyakata dake romancing daga nan ba zan wuce wani wuri, ni kaina ai ba zanso haka ya kasance tsakanina dake ba har sai munyi aure."

A hankali tayi magana, "Yaya Jawad shaid'an fa ba ta yanda ba zai iya canza maka da zuciya ba, ni wallahi ina tsoron wani abu ya faru dani, kuma Allah ba zai barni ba." Cikin zuciyarshi yake magana Kai wannan yarinya ta riga ta san Allah, ilimin addini ya riga ya shigeta da yawa. A fili kuma ce mata yayi.

"Humaira wai ko ba kya sona ne? Baki da 'kawaye da suke baki labarin soyayayarsu da samarinsu? Duk ciki wanda zai baki labari zaki ji kwatankwacin haka zai baki, kuma kinga ba zina zamu yi ba." Binta yayi da kallo dan ya gane ko maganarshi ta fara shigarta, kanta dai na sunkuye ba tare da tace mashi komai ba. Ci gaba da aika mata sa'konni yake, ita dai burinta taga ya k'yaleta. Amma ina yayi nisa baya jin kira.

Tun tana da k'arfin 'kwace kanta har tayi la'kwas ta tsaya taga iya gudun ruwanshi. Har sai da ya gaji dan kanshi ya k'yaleta. Kuka ta sakar mashi. Gaba d'aya ya rud'e yace. "Humaira mai kuma na maki ina ce yanzu da yardarki na maki?" Kukan taci gaba ba tare da ta kalleshi ba.

"Humaira ki fad'a min mai na miki? Ki fad'a min idan akwai abinda ba kya so zan daina."

Cikin kuka tace "Ka daina ta'ba ni."

Yana kallonta k'asa-k'asa yace. "Shine kawai damuwarki?"

Ta d'aga mashi kai. Yace " wannan ne dai ba kya so ko? Insha Allahu i will never touch you again, zan yi k'o'k'arin inga na daina jin abinda nake ji a kanki, amma Humaira ina so ki sani duk soyayyarki ce ta jawo min haka. Ina so abin nan da ya shiga tsakanina dake ya zamto daga ni sai ke, kada ki fad'a ma kowa."

Tana jinshi duk maganar da yake amma bata ce mashi komai ba, can ta nisa tace. "Ashe ka san abinda muke yi ba dai-dai bane shiyasa baka so kowa ya sani, yanzu ai Allah yana kallonmu, shi bamu jin kunya da tsoronshi ne shiyasa muke yi yana kallonmu? Amma muna jin kunyar mutane su san muna aikatawa?" shiru yayi yana kallonta kanta a kasa in banda wasa da zoben hannunta ba abinda take yi, mi'kewa yayi ya fita ta bishi da kallo tana harararshi, gaba d'aya ta rasa meke mata dad'i, to in dai wannan ce soyayya aiko ana tafka babban kuskure a zamanin nan da muke ciki. Mi'kewa tayi ta fad'a toilet tayi wanka, dan tana ji a ranta ba zata iya sallah ba tare da tayi wankan ba, dan kokwanto zai shiga zuciyarta, gara tayi sallan duk da ita ta san tsoro bai barta taji komai ba, sai dai ruwan da ta gani bata tantance na miye ba, so gara tayi wankan.

Haka tana wanka tana kuka dan ta san wannan shine first time da haka ya faru da ita. Wanda bata so hakan yaci gaba da faruwa da ita, a iya shekarunta bai kamata ace zata rin'ka biye ma namiji ba, da wannan rayuwar ai gara aure, to ta Yaya zata fad'a masu tana son aure. Abin da kunya. Haka ta gama wankan ta fito tana ta sa'ke-sa'ke a zuciyarta, dan ta fara jin gidan ya fita a ranta. Sallar la'asar ta tada, tunda ta kai goshinta k'asa sujjadar k'arshe take kuka tana rok'on Allah gafarar abinda ta aikata tana kuka, saida tayi rok'on da take ji a ranta Allah ya gafarta mata sannan ta d'ago. Bayan ta idar toilet ta koma ta d'auraye fuskarta ta fito ta gyara fuskar da kwalliya, ta zizara kwalli a idon dan bata son a gane tayi kuka. Zama tayi taci gaba da danne-dannen waya.

Mommy ce ta shigo ta taddata zaune ta dubeta tace.

"Humaira kizo dan Allah ki taya Talatu girki, tuwon shinkafa zaku yi miyar kuka, kin san Daddy'nku sai ki had'a miyar, dan ni nafi son tuwon shinkafarki yana min dad'i sosai."

Dariya Humaira tayi tace "Kai Mommy to bari inje mu d'aura yanzun nan." Mi'kewa tayi ta fita ta shiga kitchen ta tadda Talatu a ciki ta dubeta tana murmushi tace. "A'a su Hajiya Talatu an shigo kenan?"

Talatu na dariya tace. "Zaki fara tonon naki kenan da kika saba?"

Tace "Ai kin san idan banyi ba bana jin dad'i." Aiki suka fara, Talatu ta fita d'auko wayarta da ta bari a d'aki. Jawad ya shigo, tana ta aikinta ba tare da ta san ya shigo ba sai da k'amshin  turaranshi ya bugi hancinta, hakan bai sa ta d'ago dan ta tabbatar ko shi d'in ne ba. Kallonta yake yaga har yanzu bata waigo ba yace. "Humaira dan Allah ko zaki d'an soya min plantain ki kawo min?" Dai-dai lokacin Talatu ta dawo, Humaira taci gaba da aikinta ba tare da ta tanka mashi ba. Talatu tace.

"Humaira baki ji Yaya Jawad na magana ba?"

"Ina jinshi cewa yayi in soya mashi plantain in kai mashi, yanzu zan soya mashi idan na gama wanke shinkafa." Kallonta yayi d'auke da murmushi a fuskarshi ya juya ya fita. Talatu ce ta dubeta tace. "Humaira mai yasa kika ma Yaya Jawad haka? Naga mutuminki ne, yanda yake janki a jiki, ai bai kamata a ganku a rana ba." Eh mutumina tunda yana son ya b'ata min rayuwa.

"Humaira shine kika yi banza dani ko, baki san fushi ma bai maki kyau ba." Tana fere plantain d'in tace. "Kede kika sani ni banda lokacinki."

Bayan ta gama soya mashi tace. "Talatu dan Allah mik'a mashi." Amsa Talatu tayi ta fita, ba a jima ba sai gata ta dawo tace "Kin san ina kai mashi sai da yace kina ina ke ba zaki iya kawo mashi ba."

D'an murmushi Humaira tayi tace. "To idan ba zai ci ba ai sai ya aje kada yaci." Ita dai Talatu yau Humaira ta zaman mata abin kallo dan bata saba ganinta haka ba, kullum Humaira cikin walwala take, amma yau duk ta canza, ko da yake d'an Adam ajizi ne, ba dole bane kullum ka kasance cikin walwala.

JINI D'AYAWhere stories live. Discover now