11 Jawad.

323 20 0
                                    

*JINI D'AYA*

®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

©
*EASHA MD*

*Wattpad@Ayshatmadu*

           *11*

Washegari tunda wuri su Daddy suka taho, zaman shirya masu abinci suka yi, wanda Humaira ce take ta ti'kin aiki, dan har yanzu Talatu kwance take. Saida ta gama ta jera komai sannan ta shiga ciki tayi wanka, doguwar riga kawai na atamfa tasa, ta haye gado taci gaba da latse-latsen wayanta data saba, 'karar mota taji ya tsaya, ta tabbatar da su Daddy ne suka dawo.

Saida ta tabbatar sun huta taji maganarsu a palour sannan ta fito, gakdasu tayi tare da masu sannu da dawowa. Duka suka amsa mata cikin kulawa. Mommy tace. "Humaira baki ci abinci ba fa?"

Tana d'an murmushi tace. "Bana jin yunwa kin san ban dad'e da yin breakfast ba na shiga kitchen."

"To yayi kyau kinga ga fruits nan yanzu ki shiga ciki ki had'a mana fruit salad kada ki gaji."

Tana d'aukar ledan tace. "Kinji Mommy to idan bani zanyi aikin ba wa zai yi? Ai dole ni zanyi shi."

Kitchen ta wuce ta fara aikin, saida ta gama had'awa ta zuba masu ta kai masu. Mommy tace. "Sannu 'yar albarka, kisa ma yayanki nashi ki kai mashi d'akinshi."

Sa mashi tayi ta wuce d'akin da sallama ta shiga ta sameshi kwance, kallonshi tayi tace. "Kai Yaya Jawad duk gajiyar ne haka?"

Yana shirin mi'kewa yace. "Kawai ki bari, ai zuwa Maiduguri ba k'aramin tafiya bace." Ya fara shan fruit salad yace. "Humaira ina son muyi magana sai dai ban san ya zaki d'auketa ba. Humaira.!" Ya fad'i sunanta can cikin mak'oshi wanda ya fito da iska, ji tayi tsigar jikinta ya tashi. D'an ajiyar zuciya ta sauke. Yaci gaba. "Humaira zuciyata ta fad'a sonki na rasa yanda zanyi da ita." Ji tayi gabanta ya fad'i, sunkuyar da kanta k'asa tayi. Da sauri ta mik'e zata bar d'akin ya ri'ko hannunta. Binta yayi da kallo wanda suka 'kura ma junansu ido na tsawon lokaci, ita fara sunkuyar da kanta k'asa.

Ji take zuciyarta na bugawa da 'karfi. Dan Jawad yana da wani kwarjini da sai yau ta k'ara tabbatar da hakan, bayan ya furta mata kalmar so wanda bata ta'ba tunanin haka daga gareshi ba, gashi a gabanta yana mata maganar so. Tsinkayo maganarshi tayi dai-dai kunnanta.

"Humaira ko baki sona ne? Dan na fad'a maki ina sonki shine kika mik'e zaki tafi ba tare da kin bani amsar komai ba?"

K'ara sunkuyar da kanta k'asa tayi tana jin zuciyarta na k'ara bugawa. Ta d'ago kanta tana kallonshi tace masa. "So fa kace Yaya Jawad?" Yace "Yes ko ban kai matsayin bane?"

Ta had'iye yawun daya tsaya mata a ma'kogwaro tace. "Amma Yaya Jawad meyasa zaka ce kana sona bayan ka san ni 'kanwarka ce?" Dariya ya fara mata, saida yayi mai isarshi sannan yace. "To dan kina 'kanwata sai aka ce maki maganar so ba zai shiga tsakaninmu ba? Aure ma zamu yi."

Rufe fuskarta tayi da tafin hannunta tana murmushi. Shima murmushin yayi had'i da hura mata iska a kan fuskarta. "Baki bani amsata ba, I love you Humaira.!" Cikin jin kunya da nauyi maida mashi da martani, tana furta kalmar amma ga tsararrakinta da suke tare a school. Tace "I love you too Yaya Jawad." Da sauri ta fisge hannunta ta fita d'akin da gudu. Hannunshi duka biyu yasa cikin aljihun wandonshi yana dariya yabi hanyar da ta fita da gudu. Fad'awa yayi kan gado yana sakin murmushi had'i da lumshe idonshi.

Itako tana shiga d'aki tsayawa tayi tana maida numfashi, can ta saki murmushi wanda bata san dalilin yinshi ba.

Ranar tana kwance da daddare duk juyawar da za tayi fuskokin mutane biyu take gani, Ashir da Yaya Jawad.

Haka washegari da abin ta tashi a ranta, sai juya kalmar son take a bakinta, gashi itama ta furta mashi tana sonshi da wuri, kenan tana sonshi da gaske kenan? Tunanin yanda soyayyarta zata kasance tsakaninshi dashi take.

Wayarta ce dake kusa da ita ta fara ringing, dubawa tayi taga number Ashir, lumshe idanunta tayi tare da sauke ajiyar zuciya, d'agawa tayi ba tare da ta iya furta komai ba. "Humaira!" Taji ya furta sunanta. Sai a lokacin tayi mashi sallama ya amsa. "Akwai abinda ke damunki ne?" Ta bashi amsa da "A'a ban dai dad'e da tashi barci bane."

"Alright my princess bari na barki ki huta ko? Zuwa anjima zan kiraki." Ba tare da ta jira ya katse ba ta katse wayar tabita da kallo. Kallon number d'inshi da har yanzu ba tayi saving ba tayi, zuciyarta ce ta aiyana mata da ya kamata tayi saving number nashi, sunanshi tasa tayi saving ta aje wayar, toilet ta shiga tayi wanka. Bayan ta gama shiryawa tayi palour ta tadda Mommy zaune k'asa tana break. Kusa da ita ta zauna ta gaidata.

"Humaira sarkin barci sai yanzu kika tashi?" Murmushi tayi tana jawo flask, nan ta had'a abinda zata ci. "Har Daddy ya fita ne?"

"Aiko bai dad'e da fita ba." Humaira tace "Naso mu had'u saboda in mashi maganar zuwata Maiduguri." Mommy tace "Aiko ya riga ya fita sai idan ya dawo. Jawad ma yace idan kin tashi ki soya mashi chips." Humaira tace "Kai Yaya Jawad shi dai ya cika sa aiki maimakon yasa Talatu ta soya mashi, in banda abinshi ga doya an soya."

Mommy ta kai wani doyar bakinta tace. "To kin sanshi bai son doya sai yace tsaya mashi take, gama kije ki soya mashi." Saida Humaira ta gama sannan ta shiga kitchen ta fara fere dankalin, bayan ta gama ta zauna zaman yankasu 'kanana, Talatu data shigo tace. "Kai ni dai ban san mai yasa Jawad yafi son a soya mashi dankali haka ba? Shi nan dad'inshi yake ji?"

Humaira tayi murmushi tace. "Tunda kika yana son haka yana jin dad'inshi ne." Talatu tana wanke-wanke suna d'an ta'ba fira da Humaira har ta gama had'a mashi ta d'auka tayi hanyar d'akinshi. Tana shiga ta taddashi har yayi wanka ya gama shiryawa yana fesa turare a jikinshi ta shiga da sallama, ya amsa yana mai juyowa yana kallonta d'auke da murmushi a fuskarshi. Dire tray d'in tayi tace. Yaya an tashi lafiya?"

Yana kallonta yace. "Ba lau ba saboda da tunaninki na kwana jiya." Waro idanunta tayi tana murmushi.

Nan ya sata ta zauna ya'ki barinta ta fita har ya gama break, kallonta yayi d'auke da murmushi a fuskarshi, ya d'auko wani cover dake d'auke da zobe a ciki ya bud'e ya ciro. Hannunshi na murmushi ya jawo hannunta, ba tare data hanashi ba, tabi hannun da kallo yayin da ya fara zira mata zoban a yatsanta. Ba tare da d'aya daga ciki yayi magana ba.

Ji tayi ya fara murza mata hannu, ta fara k'o'k'arin fisge hannunta had'i da mik'ewa tsaye, ri'kota yayi yana kallonta, itama binshi tayi da kallo, ji tayi gabanta ya fad'i, gani tayi gaba d'aya yanayin fuskarshi ya canza, idanunshi sun canza daga girma sun rage, gani tayi yana 'kara lumshe idanunshi.  Ji tayi tsoro ya kamata ta fara k'o'k'arin kwace kanta amma ta kasa. Ya Ilahi! Mai yake shirin faruwa dani wayyo Hajja.

Hannayenta tasa tana 'ko'karin tureshi, amma ina ta kasa dan ya riga da ya 'kara mata nauyi, ji tayi ya had'ata da bango ya matse. Kuka ta sakan mashi, ya sunkuyo da bakinshi dai-dai kunnanta yace. "Why are you crying? Humaira sonki ne ya jamin haka, na kasa controlling kaina, i really love you Humaira."

K'ara fashewa tayi da kuka tace. "Please Yaya kada ka cutar dani ni jininka ce?" Dogon ajiyar zuciya ya sauke yace "Is ok dear. Ba zan cutar dake ba." Yaci gaba da shafa bayanta kamar k'aramar yarinya. Da sauri ta tattara duka k'arfinta gaba d'aya ta tureshi, ta samu ta fita d'akin da gudu.

Tana shiga d'aki ta fad'a toilet, kuka ta saki wanda bata san dalilinshi ba, d'auraye fuskarta tayi ta fito, samun bakin gado tayi ta zauna ta rafka uban tagumi.

JINI D'AYAWhere stories live. Discover now