6 Sa rana.

354 19 0
                                    

*JINI D'AYA*

®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

©
*EASHA MD*

*Wattpad@Ayshatmadu*

           *6*

Yau ne kwanakin ya cika da Mallam Babba yaba ma samarin su Asiya su turo ya cika, sun cika al'kawari bayan sun zo har gida sun gaida Mallam, sai gashi na siya ya fara turowa aka tsaida magana, washegari na Fatima ya turo, wata d'aya kawai aka sa ranar bikin.

An kawo goron auransu, tazo wucewa Mallam Babba ya k'wala mata kira ta shiga d'akinshi, ta duk'a yace.

"D'auki kayan sa ranar 'yanuwanki ki shiga ma Hajja dashi." D'auka tayi tana mai jin dad'in sun kusa shan biki tayi ciki dashi. Mik'a ma Hajja tayi ta zauna zaman surutu.

"Wayyo dad'i! Hajja har na k'osa ranar nan tazo akwai cashewa dan wurin rawar ba galan zan zubar ba yafin k'arfin galan sai dai in zubar da jarka."

Hajja dake kallonta tace "Innalillahi! Kai ni da wannan 'ya, wato kede halinki ban san wane iri bane?"

Dariya tayi kana tace. "Kai Hajja ni wallahi wani zubin dariya kike bani, abu kad'an sai ki zauna kiyi ta faman yima mutane sallallami, ni yau naga ikon Allah. Kinga Hajja bari in tashi in had'a kayana, zan tafi gidan Aunty Fanna can zan tare har sai an gama biki zan dawo, zanje mu fara shirye-shiryen biki."

Hajja tace "Ai ga hanya nan sai ince aje lafiya a dawo lafiya, Allah yasa taro ya tashi lafiya."

Zama tayi ta samu k'atuwar jakarta ta ja jera kayanta, saida ta fara lek'awa d'akin Mallam Babba ta tadda baya nan, sannan ta dawo tace. "Hajja naje inma Mallam sallama na tadda baya nan, idan ya dawo ki fad'a mashi na tafi gidan Aunty Fanna. Sai kuma abu na gaba ki bani kud'in machine tunda Mallam baya nan."

"To naji d'ari biyar ai ya isheki har ki d'anyi wani abin ko? Wai Wai shin takwara in tambayeki mana naji kince fa ba zaki k'ara zuwa gidan Innar taki ba, gashi kuma kin shirya zaki tafi? Nifa bana so kije ki dawo da 'bacin rai gidan nan kice maki wani abu, gashi tafiyar mai tsawo kina fad'in har sai anyi biki zaki dawo, kuma maganar karatun islamiyya fa dan in kika je can baki k'o'k'arin kizo islamiyya."

"Kai Hajja wannan irin magana haka? Kin manta na riga na had'a haddata, kawai ni jiran walima nake da d'an abinda ba a rasa ba."

Sauke ajiyar zuciya Hajja tayi kana tace. "Ni ba wani abu nace ba, da san san samu ne da kin bari sai bikin ya rage sati biyu sannan ki tafi."

Kallonta tayi tace. Gaskiya Hajja tun yau zan tafi, ki d'auko min kud'in in tafi."

D'aga pillow tayi ta d'auko kud'in ta mik'a mata, ta amsa tayi mata godiya. Fitowa tayi da jakarta ta lek'a d'akin su Adama tace. "To nifa na tafi gidan Aunty Fanna zanje mu fara shirye-shiryen biki."

Da sauri furaira tace. "Gidan Aunty Fanna?"

"Eh gidan Aunty Fanna wani abu ne?"

"A'a bakomai amma tun yanzu zaki tafi ki barmu da kewarki."

D'an murmushi tayi tace. "Kai ni kuna tsaidani kunga tafiyata." Fita tayi nan ta samu d'aya daga cikin almajiran wurin ya d'aukar mata jaka ta wuce.

Tunda ta shiga gidan suke murnar ganinta, Aunty Fanna ta dubeta tace. "Kin gama fushin dani kenan?"

"Kai Aunty Fanna to duka yaushe ma aka yi abin sati d'aya kenan fa da barin gidan, ai duk yanda 'ya tayi fushi da uwarta dole ta sauko."

Murmushi Aunty Fanna tayi, dan dama ba tun yanzu suka fara haka da ita ba, shiyasa duk yanda Humaira tayi fushi da ita ta san zata sauko.

Tunda suka shiga d'aki Humaira ke tsara masu yanda bikin zai kasance.

Sun barshi da zumar gobe zasu je su fidda anko.

Washegari tunda wuri ta tashi ta gama shiryawa, hatta komi na breakfast ta gama had'awa su kawai take jira su tashi suyi duk abinda zasu yi su fita. D'an ji take kamar bikin ne yazo.

Tunda ko suka tashi take addabarsu suyi sauri su shirya su tafi. D'an dole suka gama shirinsu da wuri sun fito dan tafiya suka ma Aunty Fanna sallama suka tafi.

Komi na anko Humaira ita ta fidda, ba k'aramin dad'i taji ba na yanda suka bata muhimmanci a cikin hidimarsu duk da girme mata da suka yi nesa ba kusa ba, amma duk da haka d'aukansu take tamkar tsararrakinta dan kusan tsawonsu d'aya da ita, sai dai ta fuska a gane sun girme mata, amma idan ta jera dasu ba sai ka zaci k'awayenta ne, bare kuma an dage an fito da 'yan matancin tun lokacin bai yi ba.

Suna gama siyayyan kayan ankon wanda suka siya harda ita, bayan sun fito ta dubesu tace.

"Ya kamata mu wuce gidan Uncle Ali da Aunty Yana mu nuna masu ankon ko?"

Fatima tace "Hakane." Gidan Uncle Ali suka fara zuwa, saida suka gaisa da Mama sannan suka zauna zaman fira.

Mariya ce ta fara d'aga kayan tace. "Wow! Amma kayan ba k'arya sunyi kyau sosai, hala za'ban k'anwa ne?" Ta idasa maganar tana kallon Humaira.

Asiya tace "Kamar ko kin sani, dan Humaira komi nata na gayu ne sai kinga ya fita da ban."

Zainaba tace "Ai k'anwarmu ba daga baya ba." Sa'adatu tace. "Yau naga ikon Allah kun zauna sai faman kod'ata kuke, karfa kusa kanta yayi girma da yawa."

Murmushi Humaira tayi ta juya idanunta tace. "Ya son ranki 'yan mata, dan sun san hakan ne shiyasa suke ta kod'ani."

Ta idasa maganar tana mai d'aura k'afa d'aya kan d'aya. Mama dake zaune tana dariya ta nuna ta had'i da cewa. "Kinga 'yar gidan Hajja baki da dama."

Dariya suka yi, nan ta nuna masu atamfa mai d'an duhu tace. "Wannan shi zamu yi amfani dashi wurin kamu, sai kuma wannan ranar d'aurin aure za a sashi."

Nan suka zauna suna ta tsara yanda bikin zai kasance. Saida suka yi sallah suka ci abinci kana suka yi shirin tafiya, gidan Aunty Yana suka wuce. Nan ma suka nuna masu ankon da shagon da zasu su siyo sannan suka yi gida.

Nan suka yi ta tura ma k'awayensu ankon ta WhatsApp.

Humaira ba zama yanda ka san itace amaryar, da kanta ta kira Maryam d'in Baba Mustapha ta fad'a mata ankon bayan ta amshi wayan Fatima ta tura mata, dan duk a family d'insu jininta yafi had'uwa da Maryam, kasancewarta ita kad'ai ce mace ba yanda bata yi da Humaira ba ta koma kaduna da zama tak'i tace tafi so a barta wurin Hajja.

Tana ganin ankon ta turo da nata kud'in dan a siyo mata a d'inka mata a nan da wuri.

Humaira da kanta ta koma kasuwa ta siyo mata, kana ta had'a da nata taje ta kai masu d'inkin.

Gand'oki wurin Humaira, saida ta dawo ta fad'a mata kud'in d'inkin, harda na Humaira ta amsa wurin Daddy ta turo ta account d'in Fatima. Humaira najin dad'in yanda iyayenta da 'yanuwanta ke nuna mata kulawa, shiyasa a rayuwarta bata kukan maraici sai idan taso, dan dan maraya duk yanda zaka kyautata mashi baya gani. Gani yake a kullum baka sonshi.

JINI D'AYAWhere stories live. Discover now