*JINI D'AYA*
®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**Wattpad@Ayshatmadu*
*13*
Kusan 3 weeks kenan Humaira tana wasan 'buya da Yaya Jawad, tak'i tsayawa su ke'be su biyu wanda hakan ba k'aramin damunshi yake ba, ta riga da ta fad'a mashi sai dai su rin'ka waya, daga nan ba abinda zai sa ta tsaya dashi daga ita sai shi idan har ba sa masu rana aka yi ba. Duk da itama abin yana damunta na rashin zama tare dashi, sai dai tana ji a ranta hakan shi ya dace idan ba haka ba kam zasu ci gaba da tafka babban kuskure a rayuwa wanda ba kowa zai shiga damuwa da dana sani ba sama da ita. Dan ba wanda zai yi kuka idan ba ita ba.
*** ***
Zaune suke gaba d'ayansu a palour Daddy ya dubeta cikin kulawa yace. "Humaira naji har yanzu baki k'ara maganar zuwanki Maiduguri ba ko kin fasa ne?"Da sauri tace. "A'a Daddy ban fasa dama kai nake jira kayi magana inji ranar da kasa na tafiyata."
Dariya yayi kana yace. "Ai nayi zatan kin fasa kin manta da Hajja?" Dariyar itama tayi tace. "Haba ina Daddy ai Hajja bata mantuwa a raina, yanda nake sonta da kewarta ai ji nake na fiku sonta ma." Gaba d'aya dariya suka yi Mommy tace.
"Haba yarinya wane ke ki fisu sonta."
"Taf Mommy aiko na fisu sonta. Daddy yaushe zan tafi?"
"Ki shirya gobe da safe Jawad ya kaiki tasha ai zaki gane gidan da kanki ko?"
"Zan gane mana ai ba inda zan 'bace a cikin garinmu."
Maida kanshi wurin Jawad yayi yace. "Jawad sai ka shirya da an fito masallacin asuba ka kaita tasha saboda ta isa da wuri." D'agowa tayi ta kalli Jawad dake kallonta idonshi gaba d'aya ya kad'a yayi jawur. Kauda kanta tayi da sauri.
Mi'kewa tayi tace. "Daddy bari inje ciki in fara kimtsa kayana." Kallonta suke suna dariya ganin yanda take ta zumud'in tafiya.
Tana shiga d'aki cikin murna ta fara fito da kayanta tana shiryasu a jaka. Mommy ce ta shigo ta taddata tana ta had'a kaya, sakin baki tayi tana kallonta tace.
"Humaira wannan uban kayan fa da kike had'awa sai kace ba zaki dawo garin ba?" Murmushi tayi tace. "To ai kada in tafi da kad'an in zo kuma in dad'e."
Zuwa tayi tana tayata had'awa tace. "A'a Humaira sunyi yawa kayan ki ragesu, kinga ke kanki zasu dameki."
Da kanta taci gaba da had'a mata kayan ta rage ta maida wasu cikin wardrobe, har a cikin ran Humaira bata so haka ba, dan ita taso ta kwashe kayanta duka idan ta tafi ba zata dawo ba, sai gashi Mommy tazo ta tarwatsa mata komai.
Saida ta tabbatar da ta gama had'a mata komai da ya dace ta tafi dashi sannan ta fita.
Ranar Humaira sai dai barci 'barawo ya saceta, dan ta 'kosa taga asuba yayi. Tun uku na dare ta tashi tayi wanka ta d'auro alwala ta fara doka nafila da addu'a.
Tana nan zaune har aka fara kiraye kirayen sallah. Sai da tayi sallah sannan ta d'auko kaya tasa. Jakarta ta fara fito dashi palour ta aje ta koma ta d'auko takalminta da gyale ta fito, ganin Daddy da Yaya Jawad tayi sun dawo daga masallaci. Dubanta suka yi gaba d'aya, Daddy yace.
"Ni da gand'oki nufinki har kin gama shiryawa? Aiko da rabon in hana tafiyar nan." Da sauri tace. "Wai Daddy ai idan ka hana wannan tafiyar sai nayi ciwo." Dariya yayi kana yace.
"To ina Mommy take?"
Mi'kewa tayi tace. "Bari in yo mata magana." D'akin ta shiga ta taddata kan sallaya. "Har kin shirya anya kuwa yau kinyi barci?" Dariya Humaira tayi, Mommy ta mik'e suka dawo palour a tare. Daddy yace.
YOU ARE READING
JINI D'AYA
Fanfictioncikin d'aga murya mai rikitarwa yayi magana wanda yasa tayi saurin d'ago da rinannun idanunta da suka rine daga kalar fari suka koma ja. "ina so ki fita a harkata, mace wadda ta san mutuncin kanta nake so na aura ba ba wadda ta watsar da nata a titi...