*JINI D'AYA*
®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**Wattpad@Ayshatmadu*
*7*
Shirye-shiryen biki ya kankama, amare sai gyara ake sha ta ko ina, Humaira kanta ba a barta a baya ba wurin dilka da shiga turare, ita kanta duk inda ta gitta k'amshin amare take.Humaira ba zama, taje ta amso masu kayansu, da kanta ta zauna ta goge masu, idan kaga yanda Humaira ta zage a hidimar sai kayi tunanin itace amaryar, hidima take da jikinta, dan komi ita suka sakar mawa, ana jibi biki su Maryam suka duro garin. Murna sosai take da ganinta dan yaushe rabon data gansu, harda Jawad da Najib duk suka taho gaba d'aya, dan ita Humaira tafi sabawa dasu.
Tunda taji sun iso tayi sauri ta shirya ta wuce gidan Hajja da suka sauka, tunda ta shige cikinsu take ta zuba masu surutu. Wayoyin dake hannun Maryam ta kalla tace. "Kai yaya Maryam wayoyi biyu a hannunki duk masu zafi kinji dad'i."
Dariya Maryam tayi tace "Kema ba kina da naki ba?" Fiddo 'yar k'aramar wayarta tayi tace.
"Wannan lakhshmi d'in, gashi k'iris ya rage ta Gunjan." Dariya suka hau mata. Najib yace. "Wato dai Humaira har yanzu kina nan yanda kike? To ai tana da daraja wayar tunda har take da sunan indiyawa."
D'an murmushi tayi tace. "Ni dai da za a taimaka a d'an bani 'yar babbar nan nima in d'an shigo gari, Yaya Maryam ki bani guda d'aya mana."
Dafata Maryam tayi tace "ki bari da walimarki zanzo maki da sabuwar waya mai kyau, sai ma ki fad'a min irin wadda kike so."
"Shikenan tunda ba zaki bani ba, na san Daddy ya siya maku nima da Babana na nan da yanzu ya siyo min."
Daddy daya shigo yaji abinda tace ya dubeta yace. "Mai kike so Humaira daya gagareki har kike fad'in haka?"
Sunkuyar da kanta k'asa tayi tana mai murza hannunta, dariya suka yi mata, sannan Jawad yace. "Daddy waya take so kaji abinda ya kawo haka."
K'arasowa yayi ya rik'eta yace. "Haba hunting akwai abinda zaki nema ki rasa a duniyar nan, mune iyayenki mu zamu maki duk abinda kike so, dan haka waya dai kamar an siyl maki ita, kina da iyaye ace baki da waya. Najib tashi yanzu kuje ku siyo mata waya yanzun nan itama taci biki da sabuwar waya."
Tsalle ta hau yi da murna tana mashi godiya. R'iketa yayj yace. "Murnar ta isa haka wace iri kike so?" Juya idanunta ta hau yi, Jawad ya k'ura mata ido yana murmushi. Tace Daddy wata infinix S4 nake so da naga friends d'ina sun siya kwanan nan."
"To an gama 'yar Daddy da tun ina kaduna kika fad'a kina so ai da mun taho maki dashi." ATM d'inshi ya mik'a masu yace. "Gashi nan sai ku ciro kud'in wayar idan kunje." Amsa suka yi suka fita. Dad'i ya mata yawa bakin nan ya'ki rufuwa. Hajja ce ta dubeta tace.
"Kai wannan baki yau ya'ki rufuwa, buri fa ya cika."
Dubanta tayi tace. "Sosai kuwa buri ya cika tunda kin kasa cika min, Daddy na kan yawan ce mata ta maku magana ku sai min sai tak'i Wai ba za a bani babbar waya ba yanzu sai na gama makaranta, haka nake gani friends d'ina da babbar waya wad'anda ma basu kaini gata ba."
Dariya Daddy ya hau yi yace. "Duk abinda kike so ki kirani ki fad'a min ba sai kin fad'a ma Hajja ba."
Tana dariya tace. "Shikenan Daddy an gama."
Tunda suka kawo mata wayar tace. "Gashi kowa ya gama gani zan sata a charji dan saita cika zan kunna."
Kallonta suke kawai suna dariya, tunda suka gama gani ta amsa ta kaima Mallam Babba ya gani, amsa yayi ya gani yasa mata albarka kana yace. "Kin tafi kin barmu ko d'uriyarki bamu k'ara ji ba a gidan nan, karatun islamiyyar ma kin aje."
YOU ARE READING
JINI D'AYA
Fiksi Penggemarcikin d'aga murya mai rikitarwa yayi magana wanda yasa tayi saurin d'ago da rinannun idanunta da suka rine daga kalar fari suka koma ja. "ina so ki fita a harkata, mace wadda ta san mutuncin kanta nake so na aura ba ba wadda ta watsar da nata a titi...