*JINI D'AYA*
®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**Wattpad@Ayshatmadu*
*15*
Washegari tunda ta tashi da safe tayi aikin da ta san zata yi ta fara shirin fita. Saida tayi wanka ta shirya tsaf, jallabiya tasa tayi rolling kanta da gyale. K'ara kallon kanta tayi jikin mirror tana jin dad'in yanda idan tayi kwalliya take ganin tayi kyau. D'an murmushi tayi ta fito.
D'akin Hajja ta shiga tace. "Hajja na shirya zan tafi sai Allah ya min dawowa."
Hajja ta dubeta tace. "Ya banga jaka ba? Nayi tunanin zaki d'an kwana masu biyu."
Kallonta tayi tace. "Hajja naga alama dai baki son zama dani kiyi ta korata, bari dana dawo zan had'a kayana na tafi tunda kin gaji da ganina."
Waro idanu waje tayi tace. "A'a rufa min asiri ni ban gaji dake, na dai yi tunanin zaki d'an masu kwana biyu yanda zasu ji dad'i."
"To ni dai na tafi sai na dawo." Ta kama hanya ta fita. Aryan ta had'e dashi ya dubeta yace. "Sister wannan wanka haka sai ina kuma?" D'an kad'a idanunta tayi tace. "Yau mun tashi da shirin ziyara dan ni da gida yau sai dare ba inda ba zani ba yau."
Dariya yayi yace. "Ai naga alama kam, ba zan d'an samu wani abu ba wurinki dan bani da kud'i." Hannu tasa a jaka ta ciro dubu uku ta mik'a mashi tace. "Gashi kayi maneji da wannan nima tun wanda Daddy ya bani ne ban ma kashe ba." Cikin jin dad'i ya amsa yana godiya. Har titi suka fita tare ya tarar mata napep ta tafi. Gidan Aunty Fanna ta fara zuwa, tararta tayi cikin farin ciki tana fad'in.
"Ga bak'in kaduna oyoyo shine sai yau nake ganinki wato saboda ba 'yan uwanki shine sai yau nake ganinki love? Ai da suna nan da tuni kinzo." Tana dariya tace. "Kai Aunty ba haka bane, ban gama jin d'umin jikin Hajja ba shiyasa na'ki fitowa sai yau. Gashi yau ma sauri-sauri zanyi in koma gida."
Aunty Fanna tace. "Aiko baki isa ba daga zuwa ba zaki kwana ba zaki ce zaki tafi."
Tace. "Dan Allah Aunty kiyi ha'kuri har yanzu ba gidan da naje tunda nazo duk yau nake so inje."
Gyaran zamanta tayi tace. "Nace nan zaki kwana idan kuma ban isa ba sai ki nuna min iyakata." Taci gaba da kallon TV da take yi, murmushi kawai Humaira tayi dan dama ta san halin Aunty Fanna ba zata barta tazo yau ta tafi ba a ranar, musamman da ta san yanzu ba garin take ba. "Gashi kuma banzo da kayan canzawa ba Aunty."
Tace. "Ai ba wani abu bane idan zaki kwanta sai ki cire ki linke, ko da yake ai Ali na unguwar bari in kirashi ya amso maki kaya na mata d'iyar tawa 'yar gayu ce ba zata maimaita kayan da tasa ba." Ta idasa maganar tana kallonta tana dariya, itama dariyar tayi.
Haka ko akayi sai dai ta kira Ali yazo mata da kaya, washegari ma da k'yar ta barta ta tafi saida rana yayi. Gidan Uncle Ali ta fara zuwa, haka su Zainaba suka rugo suka rungumeta cikin murna. "Sai yau muke ganinki ko?"
Tace. "Ku bari kawai duk son yawona sai naji bana son fita." Nan ta gaida mamansu suka shige ciki suka fara fira. Dubansu tayi tace. "Wai ku ya naji shiru ne yaushe zamu zo musha biki ya kamata fa ace ansa rana." Sa'adatu tace.
"Kada ki damu an kusa sa masu rana."
Tace. "Kefa ai had'aku ya kamata ayi mu wuce wurin."
"A'a sai na cashe sannan za ayi nawa duk sai na kaisu d'akinsu, dan harsu Yaya Lubabatu da Yaya Maimunatu duk tare za a had'asu kinga duk an wuce wurin." Cikin jin dad'i tace. "Kice mun kusa shan hidima? Allah sarki sai mu kad'ai za a bari mu uku, gara ma nice k'aramar cikinku. Kuma dai ana gama nasu sai ayi naku sai kuma ni 'yar auta." Dariya suka yi gaba d'ayansu.
Sai yamma ta wuce gidan Aunty Yana, nan ma sun tareta da murna, bayan ta gaida mamansu suka zauna zaman fira, ranar dai sai dare ta koma gida. Tana shiga d'akin ta fad'a jikin Hajja tana fad'in. "Wash Hajja na gaji yau."
"Ke ni kada ki karya min 'kafafuwa." Ta d'ago ta kalleta tace. "Idan na karya ba sai in gyara maki ba."
Tace. "Ko kuma ki idasani gaba d'aya ba. Daga zuwa ki dawo kuma sai kika 'bige da kwana?"
Tace. "Ki bari kawai Hajja Aunty Fanna ce ta ri'keni kin san halinta ai bama taso na dawo ba taso na zauna."
Hajja tace. "Ai jiya duk sai naji ba dad'i wallahi."
Uhm! Kaji Hajja keda kike ta korata kin 'kosa kiga na tafi amma kike cewa duk kinji ba dad'i."
Hajja na dariya tace. "Tunda baki yarda ba shikenan." Nan suka zauna suna ta fira duk da firan sai an had'a da rikici, wayanta da aka kira yasa ta mik'e tayi d'aki. Saida tayi wayarta mai isarta kana ta shiga toilet tayi alwala ta dawo tayi shirin barcinta tayi addu'a ta kwanta.
*** ***
Washegari ma bata zauna ba, ranar gidan k'awayenta taje. Sosai Humaira take jin dad'in ziyarar da take tayi. Tana jin inama kada ta koma tayi zamanta cikin 'yanuwanta. Yanzu ya zaman mata kullum sai ta fita saboda sunyi waya da Daddy yana so ta dawo idan ya shigo garin saboda yana son zuwa cikin satin nan. Shiyasa ta dage take ta ziyartar 'yanuwa da abokan arzi'ki.Humaira tun ana gobe Daddy zai zo take jin bata jin dad'i, dan yanzu take jin sha'kuwarsu ta 'karu da Hajja bata son rabuwa da ita. Ji take kamar idan Daddy yazo tace mashi ta fasa zama kaduna tafi son Maiduguri. Zaune take tayi shiru duk surutun nan da sa magana yau bakin ya mutu. Hajja ce ta shigo ta sameta tace.
"Takwarata lafiya yau naji ki shiru ne ko baki da lafiya ne?"
Kwantawa tayi jikin Hajja hawaye ya zubo mata tace. "Hajja bana son komawa kaduna nafi son zama daku ni dama zai k'yaleni a nan kawai." Shafa kanta Hajja tayi tace. "Humaira kada ki damu zamanki a can yafi akan nan, kinga a can ma ba ruwanki da yawo da tara 'kawayen da kike yi."
Uhm Hajja da baki san rayuwar da nake fuskanta a can ba da sai kinfi son zamana a nan, baki san rayuwata gab take da canzawa ba a can, bayan nan kunfi sa min idanu akan lamurana, can ko sai akan karatu kawai da zaman gida suka sani. Hajja ce ta d'agota tace.
"Ya naji kinyi shiru Humaira tunanin mai kike yi?"
Tace. "Hajja ni da gaske nafi son zama a can, can fa ba wani dad'i kowa yana d'akinshi yana hidimarshi. Ni Hajja ki kirashi kice ya k'ara min kwanaki."
Hajja tace. "Kada ki damu ba kin kusa fara karatu ba, da kin fara zaki ji kina jin dad'in can d'in, kuma bana son ya gane baki son zama dasu ba zaiji dad'i ba, shima mahaifinki ne koda mahaifinki nada rai yana da iko dake." 'kara kwantawa tayi jikin Hajja duk tana jin ba dad'i. Da kanta Hajja ta kwashe sauran kayanta da ba wankakku ba tasa aka wanke mata aka goge mata.
Hajja da kanta duk ta had'a mata kayanta, duk walwalar Humaira babu shi, ko fira suke sai dai ta bisu da idanu.
Ranar ko da yazo ji tayi har gabanta na fad'uwa, da zata iya data fad'a mashi ita ba zata koma ba, tunda ta gaidashi ta had'a mashi abinda zai ci ta kai mashi d'akin Mallam Babba ta fito tayi d'akinta. Kuka ta zauna tana tayi, dan har ga Allah bata son komawa garin, ga inda tafi jin dad'in zama cikin 'yanuwanta da abokanta.
Ita kanta Hajja bata son tafiyar Humaira da duk wanda ke gidan, dan zuwan da tayi ji suke kamar kada ta koma. Dan tana d'ebe masu kewa sosai a gidan, bata fushi kullum cikin sa mutum farin ciki take.
Tunda ta shige d'aki bata k'ara fitowa ba, sai da daddare shima abinci ta fito taci. Hajja ta dubeta tace. "Humaira idan kin san akwai matsala a gidan babanki ko akwai abinda ake maki da baki so ki fad'a min gaskiya?"
Tace. "A'a Hajja ba abinda ake min, asalima duk abinda zasu ma na cikinsu nima haka suke min, ni dai kawai nafi son zama daku ne kawai."
Tace. "To in dai hakane ki saki jikinki, saboda ba zaiji dad'i ba yaga baki son zama dasu kada ki damu, duk inda kike addu'armu na nan biye dake." Ita kanta Hajja tun d'azun take share nata hawayen ta dai k'i nuna ma Humaira ne dan kada ta karyar mata da zuciya. Amma ita kanta tana son zama da ita. Nan ta zauna taci gaba da yi mata nasiha da bata shawarwari kan rayuwa.
Zama tayi tana ta bata labaru na ban dariya har saida taga ta ware tana ta fira, sannan itama taji zuciyarta tayi sanyi. Nan suka raba dare suna fira harda su Adama. Ranar kam ansha firar ban kwana da Humaira.
____________
Ba karantawa ana wucewa ba a rinka yi ana voting 😅
![](https://img.wattpad.com/cover/200252883-288-k277299.jpg)
YOU ARE READING
JINI D'AYA
Fiksi Penggemarcikin d'aga murya mai rikitarwa yayi magana wanda yasa tayi saurin d'ago da rinannun idanunta da suka rine daga kalar fari suka koma ja. "ina so ki fita a harkata, mace wadda ta san mutuncin kanta nake so na aura ba ba wadda ta watsar da nata a titi...